[Advertisements⬇️]

MARAICIN RAHNA1 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hausa novels
: MARAICIN RAHMAH

Chapter 1

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Kebbi state,na wuce garuruwa da
dama,Wani daji na cinna tafiya nake katsam
sai ga asma a wata rigar fulani Wanda babu
komai face yan gidaje Wanda akayi su da
ainihin karan dawa da yayi irin dai gidaje na asalin fulanin daji,babu komai a dajin sai
korayen bishiyu,ruwa da gonakin da mutanen
yankin suke noma,gidajene daya can daya
can,tsalli tsalli,sai wata yar kasuwa,garin
ALLAH ya albarkacesu da niima kala
kala,wannan ne yasa na tsaya kallo, can wata yarinya na hango kyakyawar
gaske,yar doguwa fara fara ja ja,gashinta
har gadon baya amma shi ba baki ba kuma
ba ja ba kalar na fulani dai,hancinta me tsayi
amma ba can ba me kyau,idonta dara
dara,ga eyelashes baki,bakinta hakora kana na lips pink dan cut dashi,kai karshe dai
tayi,sanye take da wasu yagaggun kaya,
wata kodadiyar atamface jikinta duk  ta jeme,takalminta
duk ta daure da Leda,amma daga ka ganta
kaga me tsafta dan komi Fes take,sai dai
kana gani Kasan tana wahala. Yarinyar baza ta wuce yar 15yrs ba sanda ce
a hannunta tana kada yan shanunta Wanda
gaba daya shanun guda uku ne
kacal,saniya,sa,da dan maraki wato dan
saniyar,binta nayi ina dauko muku
rahoto,tiryan tiryan naga dai dai wajen magariba ta nufi wata yar bukka wacce take
zagaye da katangar kara,sai toilet guda
shima na kara da yayi ne,harda rumfar girki
da yan watsatstsun tukwane da sauransu a
wanke fes a gyare.
Jira nake naga wani ko wata ta fito amma shuru,yarinyar naga ta daure shanunta a
wani bangare na gidan ta cire kayanta ta
daura wani jememmen zani ta debi ruwa ta
shige bayi da dan kwandon soson buhu da
wani koren sabulun wanki,ta dan jima ta fito
Ashe wanka ta sillo,dan Vaseline ta shafa da kwalli,ta dauko wata t.shirt ja ta saka ta
daura wani zani Wanda shi na fulani
ne,kayan data cire da zanen wanka ta hada
ta wanke da koren sabulunta,ta
shanyasu,wata sandarariyar shinkafa da
manja ko yagi babu tacinye ta bude randarta tasha ruwa,wata futilar kwai ta kunna a
cikin yar bukkarta ta dakko wata tsohuwar
jaka,wasu littaatafai ta dakko,
Abin mamaki teach your self na hango da
brighter grammar,sai littatafan koyon rubutu
da karatu na Hausa,da bironta sai littafin rubutu guda 2 ciki Wanda a su take
rubutunta,sai da ta gama karatunta kuma ba
laifi ta iya sai ta kuma dauko Qur,ani tayi ta
karatu cikin daddadan muryarta,tabbas da gani ba
jahila bace ko daga yanda tayi sallah ma
komai dai dai,da azkhar du ta dan iya ba laifi,bayan ta gama karatunta ne naga tayi
sallar isha tayi adduoi,amma tana zub da
ruwan hawaye tare da kuka me tsuma
zuciyar me sauraro,bayan ta gama ne ta
kwanta,sai bacci,washe gari da asuba tayi
sallah da azkhar,bayan rana ta fito ne ta kwanta bacci sai wurin Tara ta tashi,tana
tashi naga ta dauko wata Leda ta Ciro
toothpaste da brush duk da brush din tsohone
tukub,da gani yaci duniya,amma tayi
kokari,ta goge bakinta tas,sannan ta shige
rumfar girkinta wuta ta hada ta dauko tukunya ta zuba madarar shanu 1 cup,ta dafa
ta bayan ta huce ta sha abarta ta
koshi,sannan ta wanke kwanikan da
omo,wani botikin karfe ta dauka Wanda
yama gama bulewa ta ko ina ,ta fita,Garin
mutane sun fito jefi jefi,wani dattijo me kamala ya tareta cikin hausarsu da batafita
yace a,a RAMATA da sauri ta durkusa baffajo
ina yini,yace lfy ramata maza ki tafi
kiwo,zan aiko,miki da geron hura yau kanji
yata,murmushin dadi tayi tare da zuba
godiya,gidanta ta cika da ruwa,sannan, ta share ko ina fes,tayi wanka ta tatsi madara
a saniyarta ta rufe a daki,ta kada su sai
kiwo,da alama haka takeyi kullum.yau ma
kamar kullum haka tayi,bayan kwana uku
ranar ta kama ranar juma,a ramata bataje
kiwo ba, ciyawa da ruwa taba shanunta,fura naga tayi me yawa da lafiyayyan nonon
kirdirmo,ta shirya komi a sabuwar
kwaryarta da faifai,du komi sabo me
kyau,har kokunan dama furar ta,ta sa
kayanta me kyau da wani takalmin roba
shima ba laifi,sai kasuwa.tana karasawa kasuwa tun a hanya ake ga ramata fillo nan,
wasu na ga ramata,wasu fillo,ba wanda
ta kula ta nemi waje ta zauna,kafin kace me
har ta kusa saida furarta,mata masu talla sai
gulma da jin haushin ramata suke. ko ya
asalin wannan yarinya yake oho Ku biyoni. !!!
Www.Littafanhausane. Com.ng

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]