[Advertisements⬇️]

MARAICIN RAHMA3 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hausa novels
MARAICIN RAHMA

             Chapter 3

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

www.littafanhausane.com.ng
Dan danan Ahmad ya kara daure
fuska,fitowa mimi tayi dauke da brush da katon carpet din da suka zo dasu daga
birni,ta shinfida musu a gindin bishiya,suka
zauna ahmad in banda hararar mimi ba
abinda yake,ramata na fitowa mimi ma ta
shiga tayi brush ta fito,fitowa rahma tayi su
ammar na satar kallonta ta Dora ruwa a wata yar tukunya babba,sannan tace musu
ina kwana,ammar ne yauma ya amsa
kawai,Ahmad latsa waya yake a ranta cewa
tayi wannan dan rainin hankali ne ,na
tsaneshi ma,bayan ruwa ya tafasa ta juyewa
mimi ta shiga wanka,sannan ta kara tafasa wani sannan ta koma wajen su Ahmad tace a
cikinku akwai me yin wanka,mamaki su
ammar sukai yau ga mace me acting din
maza,ita kuwa rahma ko a jikinta dan ta
sawa ranta ba so take kowa ya aureta ba
dan haka ba wani noke noke uban kowa ma ya tsaneta bata da damuwa,Ahmad cikin
tsananin fushi ya Daka mata tsawa akwai
sa’anki anan eh,tsorata rahma tayi ta sulale
ta koma daki,a ranta tana me cewa daga
abin arziki ya zama tsiya,dan ma na
karramasu,lallai yan birni basu San mutunci da kara ba,tana haka har mimi ta fito,a
tsorace rahma ta sake fitowa taje wajen
shanunta da wani sabon kokonta me kyau,ta
fara tatsan nonon cikin kwarewa,sai
kallonta suke har ta gama ta sauke ruwan
gefe ta kara gyara wutarta ta dauko wata tunkunyar ta kara wanketa,ta Dora madarar
ta tafasa ta,yanda suka ga tana aikin sun
yaba kwarai sabo da tsaftarta,tuni mimi ta
Debo cups din da suka zo dasu guda 4 duk
kowa an zuba masa madarar,ta debo kayan
tea dinsu,namansu,da snacks ta Jere a gaban brothers dinta,ramata ko Inda suke bata
kalla ba,mimi tacE rahma kawo ki hada tea
mana kar ya huce,tana son sha amma kunya
takeji dan haka ita fresh milk kawai take sha
da safe sai indomie watarana,
Dama tana da indomie ta guda 3 suma a kasuwa ta siyo ranar juma’a dan haka ta
dauko daya,ta dauko attarihu da albasa,taje
wajen da kajinta me kwana ta dauko kwai
guda biyu tazo tayi hadaddiyar indomin ta
cikin kwarewa da tsafta,dan malam hassan
da ke zuwa daga birni koya musu karatune ya koya mata dafa indomie kala kala,sabo da
yana dafawa yaci in yazo,shi yasa ta
iya,suna kallonta tayi lafiyayyar indominta
da dafaffan kwai a ciki,
Tuni yawun Ahmad ya tsinke,Barin ma
ammar mayen indomie,tsam mimi ta mike ta koma wajen rahma tace tab ai wlh baki isa
ba sai naci,daria rahma tayi tace kinga ungo
wannan kije wajensu Ku ci,ni wata zan dafa
dama taku ce wannnan,
Mimi ce ta dauka ta kai musu nanfa suka
rufarwa indomie sai da suka ga bayanta,rahma kuma bason ci take ba dama
amma haka ta kara dafa wata tacinye abarta
a gindin murhun sai murna take yau cikakkun
yan birni sunci girkinta sun yaba,tattara
komai tayi ta wanke,ta gyara gidanta
fes,harda kunna turaren wuta na tsinke,gida sai kamshi,ta cika gidan da ruwa ko
ina,sannan taje ta salla wanka,tasa yar
powder ja da kwalli ta shafa Vaseline a lips
Dinta,sai gata ras,ta dauko wata yar
tsohuwar doguwar rigarta yer kanti
wankarkiya,amma da gani ta tsufa sosai, wata hula tasa,sannan ta kunce shanunta
tazo India su mimi suke suna hirà,tace mimi
zanje kiwo sai yamma,in zaki amfani da
koma meye gasu nan kiyi kawai,na
tafi,juyawa tayi tare da kada kan shanunta
da sanda sai kiwo.
Fitar rahma kiwo ke da wuya Ahmad ya
sauke wani gauron numfashi,yaya a dafa muku ruwa kuyi wanka anan gidan muje
wurin dady kasan yau za a fara aikin fa cewar
mimi,da Sauri Ahmad ya amince dan har ga
Allah yafi jin dadin zaman gidan
ramata,kunna risho mimi tayi duk tare suka
zo da abinsu ta daura musu ruwan wankan,kowa yayi wanka cikin dakin
ramata suka shirya sukayi komai sai
kamshin turaren Ahmad yake gidan haka
suka dunguma sai wajen dadi,suna zuwa
suka tarar dady ya sha manyan
kaya,gaishesa sukayi sannan mimi ta mika masa soyayyen namansu kadan yaci da lemo
suka wuce gonar gaba dayansu,yayin da
suka tarar da ma’aikatan dadi tuni sun fara
aikin,Ahmad sun zage suna ta tsare tsare a
wajen ba yanda suka iya dole suyi ko dady
yaci ubansu, Bangaren ramata kuwa ta rasa dalili tunda
taje kiwo ta kasa hasala komai sai tunanin
Ahmad,ta rasa me yasa yake birgeta,kuma
in ta ganshi gabanta yana faduwa,ga
tsoronsa da takeyi,tunda ta fito kawai so
take ta koma ta sake kalonsa hmmm, Da kyar ta iya kaiwa karfe biyu ta jawo
shanunta suka dauko hanyar gida,Ahmad
kuwa ya kai kololuwar gajiya a wajen ga
rana kawai bacci yake so yayi,ruwa faro ya
dauka yana sha,ya sha malt,sannan yace
mimi tazo suje a dafa musu abinci yayi hakan ne dan ya gudu,dadi ya ganeshi kawai ya
kyaleshi,suna zuwa Ahmad ya shige dakin
ramata kamar nasa ya haye mata bed ya
kwanta sai bacci,mimi ce ta kunna risho ta
fara musu girki,har zuwa tayi ta siyo naman
rago ta musu. Jullof rice tasha nama,ta musu farfesun kifi Wanda shima a garin ta siyoshi
ana kamowa a rafi,lemo da ruwa ta debo ta
shirya komai a dakin ramata,sannan tayi
wanka tasa wata atamfa super Riga da skert
tayi kyau sai kamshi takeyi,sallah tayi
sannan ta tashi Ahmad dan 5pm ta kusa,yana tashi yayi wanka ya sa wani 3quater da Riga
armless farare kal yasa p cap yayi matukar
kyau kamar bature,sallah yayi yaci abincinsa
ya koshi ya koma bed ya kwanta,ammar ne
ya shigo yaci shima sannan yayi wanka da
sallah ya kwashi na dad ya tafi kai masa, Mimi ma gyara gidan tayi ta koma gonar da
ake aiki ahmad kawai aka bari yana
baccinsa hankali kwance,ana haka ramata ta
dawo gidan da shanunta,tun daga kofar gida
take jin wani asirtaccen kamsh,dakinta ta
shiga ba karamin firgita tayi ba da taga mutum na bacci sai da ta kalla sosai ta gane
waye,hakura tayi da shiga dakin ta koma
cikin rumfa ta zauna tana jira ya tashi ya fito,
Har wurin magrib ta gaji da jira ta Shiga
dakin da sallama amma shuru gajiya tayi ta
turo baki tana kunkuni cike da shagwaba ta sa hannu ta buga kafarsa kadan,a hankali ya
bude idonsa,yana ganin itace ya kara tamke
fuska gashi ta turo masa baki yace lallai ma
wannan village girl din,ai tana jin yayi
turanci bata San sanda tace to city boy in ka
tashi na dawo dakina kuma wanka zanyi,tsananin mamaki ya kama ahmad
gashi wai har tana gane turanci,kuma wai
wanka zatayi ya fita me take nufi kenan kar
yaganta,lallai ma yarinyar nan to me zai gani
a jikinta yan Matan kirki ma na birni basa
gabansa bare wannan kwailan,harara ya watsa mata tare da ficewa daga gidan baki
daya,
Kaf garin su ramata ya dauka cewar ramata
ta zama karuwa,ta Tara mazan birni a
gidanta,kuma me gari ya yarje mata sabo da
tana bashi cin hanci,sai gulma ake zance ya cika kauyen Cewar ramata ta zama karuwa
da yan birni take harka,ko ina kallonsu ake
ana ga yan iskan ramata nan,ko INA suka
wuce yaran gari na tsokanarsu suna cewa
karuwai ne,wasu suce yan iskane,yau
kwanan su mimi uku a garin amma su ko ajikinsu dan sun San kauyenci ke damun yan
garin,ramata kuwa ta saba da mimi sosai
sun zama kawaye,ammar ma da yake me
fara’a ne da tsokana sun saba da
ramata,Suna hira,da wasa sosai,Ahmad
kuwa Hutu ke kawoshi da cin abinci gidan,ko hira suke baya kulasu,ya matsu ma su tafi
gida,kamar a qaya yake haka yake jinsa,
Ramata ta kaiwa baffajo shanunta yaci gaba
da yimata kiwonsu,dan yanzu bata iya fita
kiwo sabo da tsokanar da ake mata a
gari,yanzu an kara tsanarta a gari a dalilin yan birni,gashi nan da 2days su baffajo da
inno zasu tafi kiwo wani dajin me nisa,sabo
da yankinsu yanzu ba abincin dabbobi da
yawa,dole su zama fulanin tashi,kayan abinci
da kudi ya bawa rahma ya mata nasiha kan
tsoron Allah da aure yace da asuba zasu bar gari ba lallai su hadu ba,tasha kuka
sosai,tasan yanzu bata da wani sauran gata a
duniya, gashi kowa ya tsaneta gashi yan
birnin ma nan da 11days zasu tafi,ba Wanda
zata gani taji dadi,Kiwon ma ta bawa su
baffajo su tafi dasu kiwo dan garin yanzu ba ciyawa dabbobi wahala suke, tunani take
idan yan birni sun tafi ya zatayi,
Dady kuwa ramata ta birgeshi,kuma ya yaba
mata yanda take kula da yaransa, gata me
hankali, shima ya samu kiran gaggawa a
wani companynsa dake lagos har ya koma lagos ya Dora su Ahmad su kula da aikin dan
bazai dawo garin ba,yace tunda sunga kan
aikin sai Dora har zuwa nan da 11days
sannan su tafi gida,abin baiwa Ahmad dadi ba
Sam, yaso shi aka tura lagos.
Kamar kullum sun gaida me gari sun tafi
aikinsu,Ahmad yana inuwa yana waya da
frnd dinsa doctor najib suna ta daria,mimice
tare da ramata suka karaso dauke da
abinci,tun daga nesa rahma ke karewa
Ahmad kallo yanda yake daria tare da rangada turanci me dadi,a ranta cewa take
jiba komi NASA me kyau ne,ji yanda yake daria
dama yana daria haka lallai,sai kuma ta tabe
baki tace to ina ruwana dashi ma,
Mimi ce ta dan daketa a baya tana daria tace
me kike tunani kawas,daria tayi tare da aika mata da harara tace dama ai akwai sa ido
mimi,ammar ne ya taho yana daria yace
rahma yan mata ko kin San daria na miki
kyau,harararsa rahma tayi tace Allah ya
ammar ko tam,cike da shagwaba ta fadi
maganar kwashe mata sukayi da daria,kunkuni ta kama tana dira diran
kafafu,duk abinda suke AHMAD na
kallonsu,shi dama baya shiga harkar wani
kuma yana da kunya,dan shi Su sukeyi shi
yakejin kunya ma,mimice tace ya Ahmad
abincinka yace sai anjima ki ajiye min,da kyar yake magana,sukam fara ci sukayi
ramata ta debi nata ta juya musu baya dan
kar aga lomarta,ammar ne ke lallabawa
yana zagawa yana kallonta sai yace wooo
tab wannan katuwar lomar fa na gani,daria
rahma take sosai ga kunya,ta rufe idonta da tafin hannunta,can ammar ya kuma
lallabawa ya dauke ruwanta tana kallonsa
yana sa hannu ta rike hannun kokawa suka
fara da hannun rahma Dana ammar,har haki
rahma take,gajiya tayi ta sakar masa
ruwan,mikewa tayi ta dauko abincinsa ta debi miya a cokali ta shafa masa a fuska,daria
suke sosai,tsawa suka ji daga sama an daka
musu,ba kowa bane face ya Ahmad,yace
ammar da girmanka wannan wanne hauka ne sai wasa kukewa mutane da abinci,aikin
banza,in haukarku zakuyi kar kuyi mana da abinci,kazamai kawai,wlh wlh na kara ganin
kana haka sai ka San me zan muku,
Zaku tsiri iskancin banza dan bakusan
darajar abinci ba,ko da kudinku a ciki,masifa
yaci gaba da yi ba ji ba gani,mimi duka
mamaki sukai dan basu taba jin yayi wannan bala’in ba,shuru sukayi ammar yace am so
sorry ya,mimi ma tace pls we r sorry,tsaki
yayi ya juya tare da cewa sorry for ur
self,rahma kuwa bata saba da fada ba har
idonta ya ciko da hawaye,ammar ne ya fara
sorry beauty yasa handkerchief yana share mata hawaye,Ahmad ne daga nesa yace
ammar u r very stupid kaji ko wai bakayi
islamiyya bane,ko kulashi ammar beba sai
da yama goge mata ya tashi tsaye yace
beauty zo muje gidanki ki huta,sosai Ahmad
ya kulu,rahma kuwa bata so ya rakota ba ko dan yan gari zasu kara tabbatarwa
karuwace,kuma ga Ahmad najin haushinta
dama ya tsaneta,kuma bata so ya kara
tsanarta,ammar ne ya dinga kwantar mata
da hankali har sukazo gida sannan ya juya
ya koma wajen aikin,yan gari kuwa ko ina zancensu akeyi.
Yan kauyen sunga ramata ta kara kyau da
fari,ta kuma dan gogewa,ta yi yer kiba
tsabar cin me kyau,ai kuwa yanzu duk sun
zuba ido cewar ramata ciki ne da ita shi yasa
tayi kiba ta kuma haskakawa,yanzu ranar da kowa zaiga ciki ya girma ake jira,a taru a
koreta daga garin tare da mata Allah wadai
da tofin Allah tsine,yanzu mutan gari da
dattawan gari tun suna zuga me gari baya
dauka shima yanzu ya yarda,dan yaga
ammar da Ahmad kwana kadai ke kawosu gidan,gashi dan alherin da suke masa na kudi
sun rage bashi,yanzu haushinsu yakeji tare
da tsinewa ramata da taja masa asara,dan
yana jin tsoron su Ahmad ne sabo da suna da
kudi yana sa rai kullum da kyautar da suke
masa baya da haka da tuni ya koresu daga gidansa,suje su sa amusu na kara da yayi
suma,amma kudi masu gidan rana masu fada
aji baza su bari ko kallon banza ya musu
ba.haka yake kyautata musu ala dole,suna
tafiya zai huce kan ramata to fa.
4:30pm ahmad yayi sallama a fusace dakin rahma dan yana jin haushin abinda suka
masa ita da ammar, ita dan ta rainashi taki
CE masa ko sorry ma,bude ido tayi yace ke
tashi ki fita zanyi bacci,haushinsa taji ta turo
baki ta fice fuuuuu,tana ta kunkuni,kai ya
girgiza tare da yin da kwafa,kwanciya yayi sai bacci.
Tunda ya koreta ta hakura a ranta tace ai
baki ne sun kusa ma tafiya,tabarma ta shinfida a gindin bishiya ta kwanta tana ta
tunanin iyayenta,baffajo,da idan yan birni
sun tafi ya zata kasance a garin,rahma sun
shaku sosai da su mimi da ammar,yayinda
Ahmad ko shiga harkarsu baya yi,yau ta
kama gobe su mimi zasu tafi ABJ,mimi kayan sawanta kaf ta kwashe ta bawa ramata da
kayan abincinsu da duk wani kayan
amfaninsu,wankin boxers da singlet ammar
yayi ya wankewa Ahmad ma nasa ya
shanya a gidan rahma,lallabawa rahma tayi
ta saci singlet daya da boxers na Ahmad,sabo da in sun tafi ta dinga shakar kamshinsa,tana
jin dadi,yau da safe duk Suna cikin motarsu
driver zaija su wuce,ramata na kuka mimi
ma na hawaye,ammar na tsokanarsu,sannan
ammar ya debo kudi ya bawa rahma yace
tayi amfani dasu kin karba rahma tayi sai da Ahmad ya daka mata tsawa yace dallah
malama karbi mu wuce kina waisting mana
time,hannu na rawa ta karba suka ja mota
suka wuce,komawa gida tayi ta kwanta tana
tunani,
Kwanan su Ahmad uku da tafiya me gari ya kira ramata,yace ya yanke mata nan da
3mnths ta kawo miji ko ya bayar da ita
sadaka,idan taki kuma to tabbas zai koreta
daga kasarsa,kuka take tana bashi hakuri
amma inaa,rufemin baki munafukar banza
fasika,tashi ki ban waje,tana kuka ta tashi,ta tafi,haka rahma ta dage da addua ba dare ba
rana akan Allah ya kawo mata agaji,kullum
da singlet din Ahmad take bacci da boxers
dinsa tana jin dadi tare da tunawa dash.
Ramata yanzu ba Sana’a ga kudin da take
dasu tuni sun kare,kayan abinci ya kare,bata da komai,sai ta kwana bataci ba,har bara sai
da ta fara,ganin irin wulakancin da ake mata
a kauyen ne yasa ta daina zuwa barar,ta
koma sana’ar daka da surfe tana samun
goma da ashirin na shan koko da
sauransu,yanzu goge baki ma da gawayi da aswaki take amfani,fatarta kuwa ko
Vaseline ta Dade rabon da ta shafa,tayi
duhu,ta dan rame,dan ma tana da hakuri da
tawakali,gajiya tayi ta tafi wajen dangin
baffanta akan su riketa ta sauna wajensu
kafin baffajo da inno su dawo ammaa fir suka ki saima zagin tsamar nama da suka
mata,yunwa da wahala suka kara kwasarta
ta tafi dangin mamanta nan ma suka mata
kaca kaca,suka ce bada su ba zama da
karuwa,haka ta dawo taci gaba da karbar
wahalarta. Tun ramata tana jurewa har ta kai ga ta kasa
sai kuka,yau ta kama ranar kasuwa ko
wanka babu haka ta tafi kasuwa dan ta roki
wasu masu siyen furarta ko rance su
bata,sai addua take,ta isa wajen baba tsoho
ta fada masa,ya tausaya mata da kyar ta samu 200 wajensa,ta koma gun me saida
wake shi kam hakuri ya bata haka ta karaci
zagayenta da kyar wani matashi me sonta
wato isa ya bata dari ta hada Dari uku,taci
abincin hamsin ta dawo gida,haka kudin suka
kare, Rayuwa taja yau kwanakin da me gari ya
yanke wa ramata sun cika,kofar gidansa ya
cika dam da mutane yayin da ramata ke
tsakiya tana sharbar kuka,
A bangaren su mimi kuwa tunda suka koma
mimi kullum zancen rahma takewa mum,dan mum ta tausaya mata,kuma taji dadin yanda
ta kula da yaranta,yau Ahmad tun 8am ya
bar gida ya dau hanyar garin su rahma,dan
yace kwana daya zaiyi ya dawo,so yake
yaje da wuri ya gama komai gobe da safe ya
juyo,run 12pm yana garin yana shiryawa ma’aikata aikinsu sai daya gama komai ya
taho domin gaida me gari,daga nan zai bawa
rahma sakon mimi data rokeshi ya tafi dashi.
Tun daga nesa ya hango jama’a damkam a
kofar gidan me gari wasu na jifa wasu na
zage zage da sauri ya karasa yaga meke faruwa hakane.
Karasawa Ahmad yayi cikin mutanen wajen
nan ya tambayi mutane uku me ya faru ai kuwa gulma na cinsu da sauri suka kwashe
lbr suka bashi tun farkon rayuwar ramata
har zuwan yan birni,da kuma abinda me gari
yace suka ce ai munji dadi barin irin wannan
yarinyar guba ne a rayuwarmu data
yaranmu,take ran Ahmad ya baci,wato duk a Kansu ne ake mata haka a grain Allah sarki,ji
yayi wani tausayinta ya shigeshi
Me gari ne ya daka mata tsawa yace to tunda
haka ne in dai baki yarda da zabi na ba sai
dai ki bar kasata,tana kuka tace dan Allah
kayi hakuri,me gari ne ya daga hannu ya shara mata mari tsinaniya INA magana kina
yi tambadaddiya asararriya,take fuskarta
tayi ja dauke da yatsun me gari,su kuwa yan
garin dadi kawai sukeji suna ihu jira kawai
suke suji na annabin da za a daura dashi,sai
cewa suke jira kawai Muke a daura da Muhammad,domin su duk namiji sunansa
muhammadu,suka CE wa zai auri wannan ai
sai marar gata hhhh,can wani yace aradu da
na sa kudina abani wannan tsohuwar
karuwar gwara nayi sana’ar gwanjo ko
naira ishiri in siyar, Mai gari ne cikin karaji yace munafukar
banza na aura miki zabina ko zaki bar
kasar,shuru rahma tayi,haushi ne ya kwashi
me gari ya sake daga hannu da niyyar
marinta karo na biyu,cikin zafin nama
Ahmad ya rike hannun tare da cin kwalar me gari,yana huci,idonsa ya kada yayi ja sabo da
Bacin rai,da kyar ya saki me gari yace
tsohon banza,Jan hannun rahma yayi ta mike
hannu yasa ya share mata hawaye,ya riketa
har mota ya sata ciki,tsananin mamaki ne ya
kama yan kauyen Wanda ya haddasa musu mutuwar tsaye,yau ga wani ya shake me
gari guda,lallai yan birni ba kunya,me gari
ne ya nisa yace kowa ta tafi gida a mata
addua a ja mata tsinuwa cikin carbi dai
dai,tsinanniya kanjamauce ajalinta,me gari
yaji haushi ya kulu akan be huce haushinsa kanta ba lallai Ashe bariki ma Nada rana,an
rabasu da kaya,wannan shedaniyace cewar
mutanen yankin.
Tunda Ahmad ke sharara gudu ba Wanda
yayi magana cikinsu bai tsaya ko ina ba sai
wani makeken hotel dake cikin garin kebbi city,tun a hanya rahma ke kalle kalle yau
taga birni,ba ta kara shan mamaki ba sai da
suka shiga cikin hotel en,daki Ahmad ya
kama guda biyu rahma daya shi daya,duk
abin nan ba Wanda ke wa wani
magana,room dinta ya rakata ya nuna mata yanda zatayi amfani da toilet fuskarsa
kamar an aiko masa da mala’ikan daukan rai
tsabar tamkewa,fita yayi yace saura ki fita
kallo wlh ranki sai yafi na saniyar da ake
noma da ita baci,dariya ya bata kan abinda
yace kallonsa tayi tana murmushi,yana fita tace jarababbe na gode dai tunda ka taimaka
min,wanka tayi da sallah,jikinta har rawa
yake sabo da yunwa,bai Dade ba ya dawo
Leda masu kyau guda biyu ya Watso mata
yace ki sa key kofarki,dan in aka saceki ba
ruwana, Yana fita ta kulle ta dawo ta bude
ledojin,lashe baki tayi ganin hadadiyar
founded yam with egusi soup yasha naman
rago,ga wani farfesun kaza,ko ta kan daya
ledar bata bi ba ta hau cin abinci sai da ta
cinye tas,tasha ruwa da juice tayi hamdala,hannu da baki ta wanko ta sa a
dustbin,nutsuwa ce ta saukar mata,daya
ledar ta bude taga kayan sawa kala
biyu,dogayen riguna masu kyau da tsada
daya light blue and white,dayar kuma baka
da ratsin golden da siririn mayafansu,sai ta ga panties da bra kala 5,taga wando tight
legins, dogo kala 2,harda brush da
toothpaste,masu tsananin kyau,tayi murna
kwarai,sai dai taji kunyar ganin pant,ga bra
wasu yan kanana,ita da bata taba sawa
ba,kunya ta kara rufeta ta fada gado ta gudundune tana dariar kunya,haka bacci ya
kwasheta,ba ita ta farka ba sai da asuba
sallah tayi ta koma bacci,ban kara shan
mamaki ba sai Dana ga rahma ta tashi sanye
da boxers din Ahmad black me ratsin fari da
singlet dinsa fara,ba karamin kyau suka mata ba,cikin magagi ta mike ta dauke
kodaddun kayan da suke jikinta ta watsa a
dustbin,su ramata an samu wuri lol,
Tambayar kaina nayi taya ta iya dakko
singlet da boxers da ta data na Ahmad
Wanda take bacci dasu a gida,Ashe a jikinta ta sa ta Dora kaya a kai,ta fita wajen me gari
idan ma ya koreta to suna jikinta kar ta bar
su a garin,sai ga Ahmad ya taimaketa,har
11bata ga Ahmad ba har ta gaji da bacci,so
take ta koma bacci ta kasa gashi ta fara jin
yunwa ko wanka ta kasa yi tana tunani karfa Ahmad ya gudu ya barta,har ta fara
kuka wiwi taji ana nocking kofarta,da sauri
ta bude,har tana murna ta zata Ahmad ne sai
taga ma’aikacin hotel dinne,kallo daya ya
mata yace ga abinci oga yace a kawo,da
turanci yayi maganar,amma kadan ta tsinta a ciki,ta dan kwantar da hankalinta
Kadan,tea lafiyayye,bread,soyayyen kwai
da chips sai plantain,nadar abinci tayi tayi
dam,ta hade bed,bacci ne ya kara kwasheta,
Bangaren Ahmad kuwa kauyen ya koma da
safe ya karasa abinda ya kaishi ya dawo hotel din daya ajiye ramata,kai tsaye wanka
ya fesa,ya hade cikin tsadaddiyar farar
shadda kal ba hula Kansa,sai gashin daya dan
Tara da saje baki luf luf sai sheki yake,ga
dinkin irin dai dai jikinsa,abinci yaci yaje
masallaci sallah ya dauki komai nasa yasa a booth,ya dawo dakin rahma nocking ya mata
da kyar ta mike ko wanka batayi ba tana ta
bacci da singlet da short dinta,cikin tangal
tangal ta bude kofar.
www.littafanhausane.com.ng

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]