[Advertisements⬇️]

MARAICIN RAHMA2 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hausa novels
MARAICIN RAHMAH

                  Chapter2

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Haka rahma take kullum yau da dadi gobe ba
dadi,yau taci me kyau jibi ta kwana da yinwa,gata Allah yayota me kara da kunya
da kawaici,akan ta roki wani abu awajen
wani koda baffajo ne gwara ta kwana da
yinwa,gata da hakuri da juriya amma ba
aure a tsarinta,baffajo da inno abun na
damunsu har me gari sun rasa ya za suyi da ita,gashi duk danginta basa kula lamarinta
bare a samu a daura mata aure da wani ko
da dan uwanta ne,abinda basu sani ba rahma
ta sawa ranta in akace za a aura mata wani
to tabbas guduwa zatayi ta bar garin. Birnin tarayya abuja wani gangamemen gida
na hango na alfarma dake cikin unguwar
maitama gidane wanda ya amsa sunansa ko
a Abuja sai an yi da gaske a samu kamar
gidan,wasu zaratan sojojine a kofar gidan
su 5 suna zagawa da bindigogi,gidane na gaske wajen tsaruwa da kyau Wanda yafi gaban
kwatancen masu karatu,cikin gidan aljannar
duniyane,flowers masu kyau,garden tare da
grass carpet,swimming pool har 2 kowanne
designe daban,bangaren garden motoci kuwa ba
karama,dalla Dalla ne na gaske birjik,part uku ne a gidan part din mom and dad komai
golden color ne,sai part din sauran yaran
gidan dark brown and golden,sai na babban
yaya komai white color ne,gidan ya tsaru
komai na alfarma ne,duk yanda zan fada
bazai fadu ba,abin ya wuce a iya fada sai Wanda ya gani,
Wani handsome guy na hango yana sakkowa
daga saman steps da alama wurin dady yaje
dan a part din yake,wata dattijuwace ta
biyosa tana my boy wait tsayawa yayi yana
murmushi,turare ta fesa masa me dadin kamshi,yace tnx mum I luv u,kai ta dungure
masa tace ammar kenan,wai Ina sauran
yara na ne kuma yau banga Ahmad ba,gashi
rana har tayi,ammar yace mom kin San
yaya Ahmad  fa shi halinsa daban ne,bari na
nemo miki su Mimi suna part dinmu. Numfashi mon taja tace kafin ka fita ka kira
min Ahmad da duka yaran kace ina nemansu
kuma karma ka manta yau dady na Neman
kowa a dare tunda yau Sunday babu me fita
bare ace an gaji,yace yes mom daria sukayi
duka ya wuce ta koma wurin dad. Dare wurin 9 duk yaran dady sun hallara su
bakwai maza uku manya mata 4,dady ke
bayani kan gidan gonar da zai Gina a wani
kauye dake kebbi state,tare da yin
gagarumin noma a yankin,yace Ahmad Kaine
babba dole da kai a tafiyar this time around,saboda sadiq ke zuwa irin wannan
wurare dan haka yau ba sadiq a tafiyar
kuma ka sani dani da kai da ammar da kuma
Mimi za a tafi kuma sai munyi 2wks munga
komai na tafiya sannan mu dawo,muna da
masauki a kauyen da yarana masu kula da harkar,amma dole a fara a idonmu,tunda dad
ya fara magana Ahmad ya bata fuska dan
baya son doguwar tafiya,kuma baya son
nesa da gida,gashi kuma wai kauye zasu
zauna har 2 weeks shikam ya tsani Noman nan
da dad ke so,shi bega wani alfanu a harkar gona ba,shi an takura masa,amma dole ya
bisu ya ya iya,dan a 1 day ma ai zasu iya
zuwa a dawo amma ace har 2weeks haba,
Shi kuwa ammar da Mimi murna kawai
suke,dady yana kula da ahmad ya share shi
kawai,suna fitowa daga dakin dady kowa ya baje a palo mum ce ta fito,autarsu amal ce ta
fada jikin mum tana momi nima zanje pls
mum,mum ce ta shafa gashinta tace amal sai
watarana zamuje,da sauri amal ta mike tana
kuka ta fice,ita kam salma tabe baki tayi taci
gaba da game a wayarta,sadiq kam mum yama sai da safe ya wuce,ahmad kuwa da
magana ma wuya take masa channel kawai
ya canja yana kallon news har suka fara
magana da mum sama sama,mimi kuwa ta
cika mum da lbr,haka kuwa akayi kwana
biyu tsakani suka hau daya daga dalleliyar motarsu babba,me tsadar gaske,driver na
jansu sai kebbi.
           Su waye ahmad!!!?
 Alh. Abdullah shehu shine dady Baban su
Ahmad,dan asalin nijar ne iyayensu wanda
sun dade da rasuwa su uku suka
haifa,abdullahi,sani sai autarsu hauwa,sani
shima yana da arzikinsa ba laifi sabo da shi
doctor ne yayi boko,kuma a nijar yake da zama,tare da matarsa fati da yaransa
4,dattijo me dattako kenan,sai hauwa wacce
take auren wani ambasador ita tana
nijar,dady ne babba kuma shine baiyi boko
ba iyakacinsa secondary,kuma shine yafi
kowa arziki a family su,kasancewar yana da zafin nema,kuma da sana,ar noma ya fara har
yayi karfi,noma ne ya kawoshi nigeria kuma
ta karbeshi shi yasa yayi zamansa,inda ya
samu matar kirki me addini wato aisha mum
kenan,abdullah ya mallaki dukiya me tarin
yawa da kadarori,ga kamfanonuwa da dama,ga gidajen mai da sauransu,matarsa
aisha mum fara tas yar fulanin kebbi ce,a
nan suka hadu ya aurota itama ba laifi tayi
boko a bangaren agriculture’s take aiki har
yau,suna da yara kyawawa 7 Wanda kowa
yana da haske sosai ga kyau kamar Arabs,amma Ahmad duk yafi su kyau ga
farinsa shi kamar kusan na bature yake dan
ya sirka da ja ma Kadan, ahmad shine babba
32yrs,sai sadiq 29yrs,ammar 26yrs,mimi
wato zainab 21,salma17yrs,sai auta amal
10yrs duk family suna zaune lfy,kuma suna ziyartar yan uwansu dake kebbi da
nijar,dady na matukar taimakawa marasa
karfi,dattijon kirki ne bashi da wani hali
marar kyau sai abu daya wato bai cikaa
yadda da kaddara ba in tazo ta fannin asara
ne sai da gaske yake iya hakuri,kuma shi Sam baya wasa da yaransa kuma bai cika
sakar musu fuska ba amma sunayin yar hira
har ayi nishadi,shi yasa kowa ke tsoronsa
fiye da mum,
Yaransu sun taso cikin jin dadi,tarbiya ga
ilmin addini Dana zamani,dan Ahmad da saddiq sun sauke,kuma sunyi littatafa da
dama sadiq a Egypt yayi karatu,Ahmad a
England ya karanci harkar business both
degrees da Masters,sadiq degrees ne dashi
yace ya gaji,ammar kuwa yace bazai iya
nisa da mum ba ko umrah baya son zuwa in ba mum,yanzu haka yana final year a wata
private school dake Abuja’,sai Mimi yar level
1,salma ss3,amal js1.
Kowa harkar gabansa yake a gidan kuma
suna mugun son junansu,shi dady yace ba
mace ba namiji a Neman kudi,kowa ya nema,dan haka yakke tasa yaransa gaba
yana koya musu komi,suke kula da komi
NASA na dukiya kawai guiding dinsu
yake,dan yasan illar maraici,mum da dad
suna matukar son Ahmad.
Ahmad fari kyakyawan gaske shi ba dogo ba ba kuma gajere ba normal yake,shi ba kiba
kuma ba rama ba,idonsa masu matukar
kyau,gashin nan ya tarashi luf luf,da wani
dan saje kadan,hanci dogo,ga shi giant,a
mazanma ya amsa sunansa,gashi da tsananin
tsabta da daukan wanka,miskili ne na gaske,mata basa gabansa,nutsatse ne sai
rashin daria da faraa,ga son harkar birni,da
son class etc,yana da abokai amma bai cika
kula kowa ba sai shahid dan gidan wani
minister ne kuma yana da nutsuwa ga
hankali,ba ruwansa ga fara’a da wasa tare sukayi primary,secondary,wannan kenan.
         Cigaban labarin
Tafiya suke sosai a motarsu har Allah ya
kawosu garin kebbi lfy tsayawa sukayi
sukayi sallah suka ci abinci a wani resturant,
sukayi take away suka kara daukan hanyar kauyen,Ahmad sai tsaki yake yana
fushi,Inda ammar ke tsokanarsa,Mimi ta gaji
dan tayi matashi da cinyar ya Ahmad sai
bacci take abinta,yau juma,a yau kasuwar
garin ke ci,sai Dana duba sai naga ai rugar su
ramata suka zo ma tofa,basu suka karasa ba sai yamma lis,wani suka tambaya gidan me
gari,aka kaisu,kowa sai kallonsu yake kamar
a cinyesu,wasu matasan kuwa sha’awa suke
inama sune haka,
An musu saukar girma,madara,zabi
soyayye,da sauransu,haka me gari ya bawa dady daki shi kadai ba laifi komi yana da dan
kyau,ga tsafta, shi yasa ma suka yarda da
zama gidan,Ahmad da ammar ma an basu
dan akurkin daki daya,driver da dan me gari
dakinsu daya,Mimi CE kadai bata da masauki
ko ina an rasa waje,sai maigari yayi umarni da a nemo masa ramata yanzu tazo,
Ramata najin kira gabanta ya fadi,dama
dawowarta kenan daga kasuwa,wanka ta
fito,tana tunanin lfy,ko wani laifi tayi,haka
dai ta shirya cikin Sabin kayan ta na yan
fulani da inno matar baffajo ta siyo mata,da sabon takalmin robarta harda dan turarenta
body spray me dadin kamshi dan Dari da
hamsin ta fesa fito Fes,dole za a fadar sarki
kar a ganta a yamutse tun daga nesa ta hango mota kamar jirgi,zo kuga idon
ramata,kamar zai fado.
A dinga afwa da typing error readers.
Tunda ramata taga mota ta tsaya tana
shafata tana kallonta,ta rasa inda zata sa kanta,tana can kallon mota ,shi kuwa
lawwali dan me gari ya karkace yana ta
bawa ammar labarin ramata yayinda Ahmad
ke jinsu dan shi abin ma haushi ya bashi
yanda suke gulmar wata banza,lawwali ya
gyara zama yace ai in fada ma da me gari yace in aureta naki yarda hauka
nake,yarinya ta tsufa a gida,ta girma har ta
gaji da duniya,shi kam ammar daria yake
kwasa yana ta zungurar lawwali,can
lawwali yace ai su ramata anyi asara ga
kyau sai ya tashi a banza shekara da shekaru ba miji,kawai dan iyayenka sun
mutu, sai da me gari ya harareshi sannan
yayi shuru,
Hakan yayi dai dai da sallamar ramata cikin
nutsuwa da zakin murya,har kasa ta gaida
me gari da alhajin birni baban su ammar cike da ladabi,ta gaida ammar da Ahmad,ba
karamin mamaki ammar yayi ba daya
ganta me kyau haka,ga ta yarinya,dan shi ya
zata takai 35 a yanda lawwali ke basu lbr,shi
kam Ahmad ko kallon Inda take beba,bare
yasan ya take,itakam ta zata ma bakin turawa ne,dan da a hanya ta gansu cewa
zatayi aljanune,wani tsoro ma suke bata
tsabar kyau da murjewar fata.
Me gari ne ya fada mata bukatarsa kan ta
tafi da Mimi gidanta su zauna zuwa 2weeks,ba
tare da jin komi ba ta amince,shi kam dady tunda yaji ita daya take kwana yace bai
yadda ba sai dai ammar ko Ahmad ya bisu
gidan da kyar aka kwantar masa da hankali
cewar ba matsala,haka Mimi ta dauki Jakarta
tabi ramata suka tafi,shuru duka sukayi suna
tafiya,Mimi Ce ta gaji tace ya sunanki?ramata cewa tayi na qaryar ko na gaskia,daria Mimi
tayi tace all,take ramata ta wani kara gyara
murya na gaskia rahma abubakar na karyar
ramata,Mimi ta danyi mamaki da taga
ramata ta gane menene ALL,murnace ta kama
ramata tayi turanci sai dadi takeji,a ranta cewa tayi bari in dinga yara mata turanci ko
ba komai na karu,can ramata tacewa Mimi
and you,zainab ana CE min Mimi,tabbas Mimi
tasha mamaki ko ba komai taga kokarin
rahma a English,suna haka har suka je
gidan,rahma dafawa Mimi ruwa tayi tayo wanka,sannan ta tafasa musu madara da
sugar,sannan itama tayi wanka,kafin ta fito
Mimi ta dakko bournvita ta hada tea lafiyaye
da wannan madarar ta shanu da ramata ta
dafa,bude Jakarta tayi ta dauko musu
soyayyen naman kaza da snacks suka ci,ramata har godiya ga Allah tayi taci abinda
ko a mafarki bata taba gani ba,itakam Mimi
har ga Allah rahma ta kwanta mata har ji
take dama dady ya dauke ta koma birni
gidansu,haka suka kwanta suna hira,yayin
da rahma ta kwashe tarihinta kaf ta fadawa Mimi,ta tausaya mata matuka,itama ta
bata lbrn gidansu da kowa,sannan suka
koma hirar duniya inda Mimi ke bada lbrn
birni ramata na bata na kauye har sukayi
bacci a dan sakarKarin gadon ramata na kara
da katifar yayi,sosai ramata ta kwantawa mimi,ga tsabta,hankali da nutsuwa,ba gida
danci kamar sauran mutanen kauyen,komi
na gidan a wanke a share,a tsaftace wannan
kenan.
Ahmad cikin dare ya kasa bacci Sam shi
kauyen bai masa ba ga yunwa dan baici komai ba,sai juyi yake yana tsaki,gashi Mimi
ta tafi da jakar kayan abincinsu da mum ta
basu,gashi dady ya bada komai na abincinsu
a kaiwa Mimi gidan ramata su zasu dinga
dafa musu abinci kullum,dan haka ahmad ya
kasance cikin tsananin bakin ciki tare da tsinewa noma gaba daya,shi kuwa ammar
kallon american film yake a computer sa
tunda yaga kauyen har wutar nepa ce
dasu,duk da ana daukewa amma ba laifi suna
samu, ammar shi garin ya birgeshi bashi da
Matsala.shi kam uban tafiyar dady dama ya saba yana can suna hira da me gari har sun
saba sosai abinka da manya.
Washe gari tun asuba da su Mimi sukayi
sallah suka koma bacci har 9am basu tashi
ba,ahmad ya kasa bacci dan baisaba da
zama da yunwa ba gashi yana da ulcer,cikin sa har ciwo yake sabo da yunwa,dan haka
da kyar ya iya kaiwa 8am yaje ya dami dad
shi yunwa yakeji,me gari yace shi gidansa
koko da kosai ne sai dumamen tuwo,shi
kuma ahmad baya cinsu,haka dady ya dinga
masa fada akan ya dameshi,suje yaro ya rakasu gidan da Mimi take ta musu girki,da
sauri ya kira dan me gari karami suka tafi
Inda Mimi take har ammar Dama su ko a
gida da wuri suke Brkfast,har gidan ramata
yaro ya rakasu ya koma gida,su kuma suka
Shiga da sallama,ahmad da ammar gidan ya birgesu dan gwadas dashi gashi a
tsaftace,ahmad cewa yayi dama su aka
sauka a gidan tsabar tsaftar gidan kamar
drawing, ammar har pics yayi a gidan ya
dinga selfie, gashi dai na kara ne na kauye
amma yayi kyau,gajiya sukayi da sallama suka leka dakin,ahmad kamar ya hadiyi
zuciya ganin su bacci ma suke, da kyar
ammar ya dinga kwala ma Mimi kira suka
tashi,ramata kunya ta kamata har wani
sunne kai take,cinyayyen brush ta dauko
zata fita,mimice ta tsayar da ita tare da dauko Sabin brush a jaka ta bata,kar kuso
kuga murna wajen ramata,da toothpaste din
mimi ta matsa mata me tsada,har ga Allah
ramata ta manta da su ammar suna waje
tana fitowa da brush a bakinta,ga wani dadi
da sanyi dake ratsata tayi sabon brush ga weather yau ta mata dadi,bata San sanda ta
daga hannaye sama tare da gantsarewa
akayi mika,ta mikar da hannunta tace
uhmmmmm tare da murmushi,ai ammar bai
sanda ya kwashe da daria gashi ya tuno lbrn
da lawwali ya bashi akan ramata,gashi yan brst kamar karamin lemo,amma abinda tayi
sai ya mata kyau,ga dimple dinta,abin
sha’awa,ahmad ne ya harareshi,tare da
masa gargadi da ido,amma ko shi ya firgita
da kyanta.kuma yayi mamakin lbrn su
lawwali, dan sai yanzu ya mata kallon tsab,ita kam ta zata gulmarta suke dan haka
ta balla musu Harara ta murguda musu baki
ta wuce bayi abinta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]