Gangar jikinsa na aura7

Advertisements

_____

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter7

bawai su daban suke da ku ba a’a kuma kowacce a cikinku ta dage zata iya zuwa na daya, biyu da ta uku. Don haka duk wacce take so itama next term taji sunanta a cikin wadannan ukun to ta dage da karatu, don haka ku sake tafawa Rauda da Nusaiba da kuma Pamella. Tafi raf-raf ya dinga tashi saida Haisam ya ce ya isa tukunna suka daina. Ya dauko wata katuwar anbulam wacce aka like ta da salatif an yi rubutu da maka dara-dara kamar haka:
FIRST POSITION IN J.S.S 1A
RAUDA SHITU MUKTAR.
Ya mikawa Rauda, daliban suka tafa mata raf raf ya ce taje ta zauna. Ya sake dauko wata wacce girmanta bai kai girman na Rauda ba, itama an like jikinta da salatif an rubuta.
SECOND POSITION IN J.S.S 1A
NUSAIBA IDRIS.
Ya mikawa Nusaiba aka tafa mata ta tafi ta zauna itama. Ya dauko ta karshe itama girmanta bai kai ta Nusaiba ba, a jikinta an rubuta.
THIRD POSITION IN J.S.S 1A
PAMELLA MARTINS BENIN
Aka tafa ta karba da murna ta tafi ta zauna, Haisam ya ce “To yanzu zan kira na hudu zuwa na goma suma su fito nan su tsaya a tafa musu don suma sunyi kokari matuka. Fargaba ta sake dira a zuciyar Hannah. Ta ce a ranta “Idan kuma bana cikin mutane goman nan ni kaina nasan banyi kokari ba, shikenan karshen makarantata yazo don nasan tunda Malam Haisam ya rantse nasan da gaske yake sai ya zaneni sannan ya korani gida saboda tsananin da ake mata da azabtarwa. Baya ga bautawa ga horon yunwa, babu wanka ko tayi wankan ma kusan daya ne da bata yi ba don wankan babu sabulu, sai wani lokaci ne idan tayi wanke-wanke idan omo yayi saura take boyewa tayi wankan dashi shima a sati baifi sau daya ba. Anan kuwa sunkinan sabululai Haisam ya siya mata. Ga mayukan shafawa iri-iri masu kamshi, ga man gashi, dake ita daman gashinta ba irin kalar kitso bane ko tayi kitson kwana biyu zai fara zamewa. Amma yanzu da ta sami mayuka masu sa gashi yayi laushi sai take wankewa da man wanke gashi ta mulke shi da man gashi tasa ribon ta daure tamkar na indiya. Baki sidik a kwance fatar jikinta tayi fayau luf-luf sumul-sumul kamar ba ita ba, ita bata ki har shekara shida ba’a yi hutu ba.
Malam Haisam yaci gaba da kiran daliba ta hudu, ya kira ta biyar, ta shida Hannah ba ta ji sunanta ba, ya kira ta bakwai da ta takwas. Sai kukan da take ya kara tsananta har na kusa da ita suka fara jiyo shesshekar kukan da take yi suna juyowa suna kallonta, Haisam ya kira ta tara sannan ta goma ya ce “Hannah Abubakar Imam. Shima sai da yayi ajiyar zuciyar jin dadi. Hannah ta mike ta taho idonta tamkar anyi wasan ruwa kaca-kaca da hawaye. Haisam ya dafa kanta ya ce “Hannah kukan meye haka kike shesshekawa lafiya? Yi shiru goge hawayenki kinzo ta goma kinyi kokari. Dadi da kwanciyar hankali suka lullube Hannah, yasa aka dinga tafawa daliban da zuka zo na hudu zuwa ta goma. Daga karshe ya ce su koma su zauna ya ci gaba da kiran dalibar data zo ta goma sha daya zuwa ta saba’in da shida ta karshe kenan wata gandamemiyar ajin ce tafi kowacce girma a ajin mai suna Eneka Eddiward ita ce ta zo musu ta karshe. Da yawan dalibai suka rushe da kuka jin Malam Haisam ya furta repeating suna tunanin shikenan za’ayi musu repeating, Haisam ya shiga lallashinsu yana cewa kowacce tayi kokari babu wacce za’ayiwa repeating kasancewar da sauran damar da zasu iya dagewa nan gaba ba’ayi second term ba balle third term sannan suka ji dan sanyi a ransu suka fara goge hawayen daya jika musu ido. Hannah ta koma gefe tana kallon jifgin mutanen data kayar yayin da zuciyarta take jinjina mata ai kinyi matukar kokari tunda kin wuce mutane sittin da shida. Farin ciki ya lullube zuciyar Hannah. Ta sake sa ran dawowa makaranta idan hutunsu ya kare. Kasancewar taji Haisam ya yaba da sakamakonta don haka zai sake yi mata siyayyar makaranta da biyan kudin makaranta da aka ce duk term ake biya, kuma dubbunnan nerori.
Bayan kowacce tayi shiru da kukan da dayawa suke yi, sai Haisam ya ce “Duk kunyi kokari kasancewar *yan ajin babu marar kokari ya ce kowacce tazo ta karshe a nan ajin idan a wani ajin ne, B, C ko D ita zata zo musu ta wajen goma sha wani abu, kunga kowacce tayi kokari karku damu.
Ya dauko wata katuwar leda a gefensa ya ce dai-dai da dai-dai su ringa tasowa suna karba. Biscuit ne mai dadi ya rarraba musu kowacce daliba ta samu tun daga kan Rauda har Eneka Eddiward kowacce ta fara fara’a da murna tayi kokari. Da Haisam yaga duk sun ware yana musu wasa suna dariya sai ya ce “Ina so na shaida muku daga yau ko kuma in ce daga gobe ranar da za’ayi hutu idan na tafi hutun nan na tafi kenan. Gaban  kowacce ya yanke ya fadi. Bamu gane ka tafi kenan ba Uncle Haisam. Su duka suka tambaya. Haisam yayi murmushi ya ce “Kun san ni copper ne, nazo ne yin bautar kasa wannan makarantar (N.Y.S.C) kuma yanzu lokaci yayi da muka kare don haka idan na tafi hutun nan bazan dawo makarantar nan ba. Ina muku fatan alheri kuma shawara nake baku akan kowacce ta dage tayi karatu banda wasa.
Ko wacce jikinta yayi sanyi fuskarsu alamar basu ji dadin wannan batu na class master dinsu ba. Suna son Haisam saboda kula da soyayya da yake nuna musu wasa da dariya a koda yaushe. Sai wasu da yawa daga cikinsu suka rushe da kuka. Babu kamar Rauda, Nusaiba da Hannah. Ai kuwa gara Rauda da Nusaiba akan Hannah wani sabon tashin hankali ya rufta mata fiye dana dazu. Haisam zai bar makarantar nan ita kuma ina zata dosa?.
Haisam ma wani tsananin bakin ciki ne ya mamaye a zuciyarsa. Yana tsananin son yan ajinsa, baya so ya tafi ya barsu yana tausayinsu kasancewarsu yan yara, babu kuma wani Malami ko manyan daliban da zasu zauna suna basu shawarwari kamar yadda yake yi musu kowanne lokaci. Ga kuma kanwarsa Hannah, wa zai kula da Hannah? A bar zancen kudin makaranta da siyayyar (Provission) ita kanta tana bukatar a kula da ita da kara karfafa mata gwiwa wajen idan ta tafi gida hutu ta dawo makaranta. Koda a gida an ce baza ta dawo ba tasa kuka har sai an dawo da ita. Ga wasu abubuwan da suka yi mata nauyi a aji, ma’ana bata ganewa sai shi Haisam da kansa yake nunnuna mata har sai ta gane.
Allah Sarki Hannah ya fada a zuciyarsa ji yake kamar ya rushe da kuka dan tsananin bakin cikin rabuwa da dalibansa. Amma ya daure ya dinga lallashinsu, idan wadannan suka yi shiru sai wadansu su rushe da kuka. Haisam dai har ya gaji da lallashinsu ya ce su tashi su tafi dakunansu sai gobe zasu hadu a wajen asembly hutu. Suka nufi dakunansu kowacce na sharbe hawaye. Haisam kuma ya nufi gidansa a nan staff quaters yana mai matukar jin ba dadi a ransa. Kowa yayi shiru ya daina kuka amma banda Hannah. Nusaiba da Rauda suka dinga lallashinta amma ta ki dainawa ta ki cin abinci sai kamar tayi shiru ta daina sai ta tuna karshen makarantarta yazo sai ta sake rushewa da kuka.
Haka ta yini cur tana kuka. Rauda ta ce “Waini Hannah kukan nan da kike yi kinfi kowa son Yaya Haisam ne? Ni fa munfi kusa da shi Babana abokin Babansa ne. Kuma Yayana Auwal abokinsa ne. Haka kuma Yayata Uwa daya uba daya Ramla budurwarsa ce koma na ce matarsa ce don har ansa musu rana. Sanda muke America yan gidansu a gidanmu suke sauka in sunje kuma da muka dawo nan kasar saboda Yaya Haisam ne aka kawoni makarantar nan tunda yana Malami ya ce da Abbana makarantar akwai karatau. To harni na hakura na daina kuka ke ba za ki hakura ba kamar kinfi kowa sonsa. Ya ce dai ke kanwarsa ce kuma ni a sanina yan uwansa duk a Kano suke na sansu kuma amma ni ban sanki ba. Kuma duk a yan uwansa babu masu kama da ke. Ke kamar wata Balarabiya kike ko buzuwa ce ni dai ban sani ba.
Nusaiba ta ce “Haba Rauda meye haka in ita ba yar uwarsa bace zai fada ne? Hannah ta sake rushewa da kuka. Daman abunda Rauda take yi mata ya isheta. Tunda aka kawo ta Malam Haisam ya ce kanwarsa ce taga Rauda tana kishi da ita, wai ya za ayi ace Hannah kanwar Yaya Haisam ce bayan ita kadai ce kanwarsa a makarantar.
Washe gari da sassafe dalibai
suka shirya kayansu
tsaf na tafiya gida suka saka
kayan makarantar
(Uniform) suka dunguma
babban dakin taro (Hall) don yin
assembly hutu. Hannah da
Nusaiba suka
kinkimo jukunkunan kayansu na
sakawa suka kuma rarrataya
jakar littattafansu a baya.
Akwatinansu kuwa da katifu da
bokitai a wani daki
ake lufgawa a rufe. Ba’a tafiya
dasu gida. A bakin
Hall din suka ajiye jakunkunan
sannan suka shiga
cikin Hall din dan yin assembly,
kasancewar Principle, vice
principle da duk Malaman sun
karaso wajen assembly.
Kallo daya Haisam yayi wa
Hannah yasan tasha
kuka kuma tana cikin tashin
hankali. Principal ta
sanarwa dalibai cewa an basu
hutun kwana arba’in
da biyu. Don haka ranar da
kwana araba’in da biyu
ta cika kowacce daliba kada ta
kara ko kwana daya, idan ta
kara to za’a korata gida. Ba za’a
karbeta ba. Sannan tayi musu
nasihohi akan idan
suka je gida su dinga taya
iyayensu aiki banda
yawo a gari, gidan kawaye balle
kuma masu zuwa
gidan samari. Mataimakin
principal ma ya tofa
albarkacin bakinsa. Ya jawa
daliban kunne akan su zama
masu da’a da ladabi da biyayya
a duk inda
suke. Sauran Malamai ma suka yi
musu nasihohi akan suyi amfani
da abinda Principal ta fada
musu
da mataimakinta. Sai kuma daga
karshe Malamai
uku da suka zo bautar kasa
suka yiwa daliban
makaranta sallama akan in sun
tafi sun tafi kenan, ba zasu
dawo ba. Malaman yan bautar
kasar sune
Uncle Haisam, Rose Iliya da
Hassan Bawa. Dalibai
manya da yara sunji ba dadi
saboda sun saba da
Malaman musamman Haisam
saboda kirkinsa da wasa da
dariyarsa yasa kowacce daliba
taji tana sonsa.
Musamman daliban da yake
koyarwa suna matukar bakin
ciki da rabuwa da Malaminsu
wanda
ya kware wajen koyar musu da
Geography. Nanfa
dalibai suka rude da sururtu
wasu na kuka wasu na fadin. “We wll
miss you! We wll miss you so
much!! Uncle Haisam,
Please ,stay don’t go
please. A haka dai principal da
sauran Malamai suka fice suka
umarci daliban suma su tafi duk
wacce aka zo dauka.
Hannah da Nusaiba a bakin
barandar Hall din wajen
jakunkunasu suka zauna.
Nusaiba tace
“Allah Yasa Daddy na tun jiya
yazo Kano daga
Abuja. Ya kwana a Kano yau da
safen nan ya kamo hanyar
Kazaure.da ace yau zai taho
daga Abuja
gaskiya inajin ai sai yamma zai karaso,
wallahi murna nake
yi yau kamar za’a sani a
aljannah, dama ace ina rufe
ido na na ganni a gida. Hannah
tayi murmushin
karfin hali don babu walwala a
zuciyarta, dama ace
duk wanda baya son zuwa gida
ya daga hannu sai tafi kowa
daga hannu don ta zauna a
makarantar.
Nusaiba ta kalli Hannah wacce
tun safe bata murna.
Musamman ma yanzu da taji
ance hutun kwana
arba’in da biyu za’ayi sai ranta
ya sake baci. Ga kuma babban
tashin hankali Haisam zai tafi.
Nusaiba ta kula da Hannah ko
irin dokin tafiya gida bata yi. Sai
surutu take ita kadai Hannah
bata
sauraron ta sai wani tunani take
na daban, Nusaiba
ta dan zungureta da gefen
hannu ta ce “Waike Hannah
meke damunki ne ko murna bakya
yi gida fa
zamu. Hannah ta nisa sannan ta
sake yin murmushin karfin hali
ta ce “Me kika gani? Wallahi
nima ina murna dama na bude
ido in ganni a gida yanzu.
Nusaiba taji dadi da wannan
gudunmawar
hira da Hannah ta fara bata. Ta
ce “Ni kuma ina zuwa gida fruit
salad zansa ayi min inci wallahi
shi
nake marmari. Kefa kina zuwa
gida me zaki fara sawa ayi miki?
Hanna ta ce “Wa zansa? Nusaiba
ta ce “A’a masu aikinku man ko
mamarki tunda ana
dokinki ai komai kika ce kina so
za ayi miki. Hannah tayi ajiyar
zuciya, alamar wadanne yan
aiki ko kuma wacce mamar
zansa, Iya Abu? Lallai ashe sai
dai in mutu. Nusaiba ta
zungureta tace “Ke
ma kice a hada miki fruit salad,
fruit salad? Hannah ta tambaya
domin ita bata taba jin sunan ba
ma balle ta sanshi ko yaya yake.
Ta ce “A’a ni makanni
zan suyo inci. Nusaiba ta zabura
ta ce “Meye makani,
kwatantamin yadda yake nima
idan naje
gida ince a soyamin. Hannah ta
ce “Aishi makani
dafa shi ake yi. Ba kisan gwaza
ba? Nusaibah ta ce “Gwaza!
Gwaza!! Menene ma gwaza? Oh
cocoyam
za ki ce min, Kai! Allah ya
sawake inci gwaza sai kace
wata yar kauye? Hannah tayi
shiru don ita
tasan yar kauye ce kuma su
acan gwaza ce abun marmari.
Nusaiba ta ce “A ina kuke samun
gwaza
ni bana ganin ta ma ko a
kasuwar Abuja. Hannah ta ce
“Mu muna samu.
Uncle Haisam ne ya tunkaro
wajen da suke zaune,
su duka suka mimmike tsaye
don girmamawa gami
da cewa “Good morning sir. Ya
ce Morning Hannah,
Good morning Nusaiba. Yau
yan mata sai gida
naga Nusaiba sai murna kike yi
ko? Nusaiba ta ce “Yaya Haisam
murna yau nake yi kamar za’a
sakani
a aljannah. Haisam yayi dariya ya
ce “Hannah ke fa,
kema kina murna kamar za a
saka ki a aljannah?
Hannah tayi murmushin karfin
hali ta ce “Eh ina
murna nima. Shigowar wata
mota kirar end of discussion ce
ta katse hirar da suke tazo ta
tsaya, kafin mutumin da yake
ciki ya fito daga motar Nusaiba
Idris ta daka tsalle ta mike da
gudu ta nufi
wajen motar nan tana cewa
Babana oyoyo. Ya taho
shima da saurinsa ya rungume
ta su duka murma suke yi.
Nusaiba ta ruko hannun
Mahaifinta ta nufo
wajen da Malam Haisam da
Hannah suke a zaune su duka
suka mike don girmamawa.
Nusaiba ta ce “Baba ga class
master din mu da nake baku
labarinsa a wasika nace shi yake
kula damu Uncle Haisam
sunansa. Alh. Idris yayi dariya ya
ce “Oh Uncle Haisam ne duk
wasikun Nusaiba sai ta rubuto
mana labarinka da kai da
kawayenta Hannah da Rauda.
Haisam yayi murmushi ya ce
“Allah Sarki ai ga kawarta
Hannah. Hannah ta duka ta
gaishe
shi ya mikawa Haisam hannu
suka gaisa. Nusaiba ta ce “Baba
daga wannan hutun Uncle
Haisam ba
zai dawo ba. Alhaji Idris ya ce da
Haisam “Ai daman teaching
practice kake yi anan
makarantar ko? Haisam ya ce
“Eh bautar kasa (NYSC) nayi
kuma mun gama. Alhaji Idris ya
ce “Ba dadi yara sun saba
da kai gashi zaka tafi, mun gode
Allah Ya saka da alheri.
Haisam ya ce “Ba komai ai
kannena ne. Nusaiba ta ciro
takarda daga jakarta da biro ta
mikawa Haisam tace ya rubuta
mata lambar wayarsa. Ya karba
ya
rubuta mata, ta karba ta mikawa
Hannah tace “Hannah rubuta
min lambar wayar ki a kasan ta
Uncle Haisam. Hannah tayi turus,
ita bata taba ganin waya  a gidansu bama balle ta san yadda
ake amfani da ita har tasan
wata lamba, Haisam yayi sauri ya
ce “A’a ke rubuta mata taki zata
kiraki. Nusaiba ta rubuta
lambar wayarta ta mikawa
Hannah, Hannah ta karba. Daga
karshe Hannah ta kamawa
Nusaiba
jakarta suka nufi wajen mota.
Alhaji Idris ya bude but Haisam
ya kama ya saka. Nusaiba ta
rungume
Hannah su duka suna hawaye.
Nusaiba ta ce “Kina zuwa gida ki
kira ni a waya kuma kullum
zamu
dinga waya muna gaisawa.
Alhaji Idris ya dafa kansu ya ce
“Ku daina kuka hutu za kuje
yana
karewa zaku dawo ai baku rabu
ba gaba daya.
Nusaiba da Mahaifinta suka
shiga mota ya ja suka
tafi Hannah da Haisam suna
daga musu hannu har suka kure
sannan suka koma inda suke
zaune da
suka zauna. Sai ga cincirindon
dalibai suka zo game
da barin makarantar da zaiyi.
Suna bashi lambobin wayar su
shima ya basu tasa, Haisam ya
baiyana
musu cewar in Allah Ya yarda
duk term zai dinga
zuwa yana ganin su. A haka dai
suka dinga wasa da dariya
kamar yadda suka saba.
Rauda ma ta karaso wajen ta
zauna ai hirar da ita
basu lura da sanda motar gidan
su ta shigo ba, sai kawai suka
hango Auwal Yayan Rauda ya
tinkaro
su. Rauda ta mike da gudu taje
ta rungume Yayanta, yana
karasowa ya mikawa Haisam
hannu suka kashe ya ce “Malam,
Dama haka kake sa daliban
naka a gaba kuna rera hira?
Haisam yayi
murmushi ya ce “Bankwana
muke yi kasan daga yau shike
nan bazan dawo ba, Auwal ya ce
“Wai
har kun gama bautar kasar?
Haisam ya ce “Kwarai
kuwa ba fama nake da kai ba
kazo ka dinga yi mana dan
kwana biyu ma kaki to gashi
nima Allah
Yayi min komawa gida gaba
daya mun zama daya.
Ya ce “Lallai shekara kwana ce
kamar yaune muka
kawoka kamar kayi kuka
bakasan kauye. Haisam
ya tuntsire da dariya ya ce
“Gashi kuwa na saba
yanzu har bana jin dadi zamu
rabu da dalibaina. Nan dai
Auwal ya sami yar kujera ya
zauna shima
dake gwanin wasa da dariya ne
da mutane ya dinga hira da
daliban nan yana zolayarsu
dakyar
Haisam ya banbaro shi daga
wajen daliban nan.
Auwal da zolaya ya sami yara
yana ta zolayarsu
musamman Hannah, duk da ma
baisan yadda take da Haisam ba
yana tayi mata wasa wai ita
balarabiya ce ta koya masa
yarensu yana
tambayarta me ake cewa yaro
da larabci? Ta yi
dariya ta ce “Ban sani ba, shi a
tunaninsa taki fada
masa ne kawai, baisan ita ba
balarabiya ba ce.
Auwal ya Mike ya ce da daliban,
“To ragowar kwaki da kanzo na
tafi tunda kun zama yan
kwantai ba’a
zo daukar ku ba. Ya kalli Hannah
ya ce “Ke yar Yemen jirgin
kasarku baizo ba kema mun tafi
mun
barki sai kinfi kowa yin kwantai
saboda ke ba yar kasa ba ce.
Hannah ta kyalkyale da dariya.
Sauran dalibai suka ce “Mu
bama cin kwaki bamu san ma
yadda kanzo yake ba Allah Ya
sawake
kuma muma yanzun nan za’azo
daukar mu. Haka wasa da dariya
aka dinga yi da Auwal da su
Hannah Haisam na gefe yana
kallonsu yana dariya ya ce da
Hannah “Kema dauko jakarki
kizo mu tafi na riga nayi muku
signing ke da Rauda mu tafi
kawai. Auwal ya ce da Hannah
“Ah ke da nace sai
kinfi kowa yin kwantai ashe tare
zamu tafi dake ko a filin jirgi
zamu ajeki ne a Kano? Hannah
tayi dariya
ta ce “Oho, ni dai banyi kwantai
ba. Haisam ya dauki jakar Rauda
Da qar saboda nauyi ba zata iya
dauka ba ya kai ya saka a mota.
Auwal ya ce “Hannah kawo
kema in taya ki tunda baki da
karfi
don nasan a garinku bakwacin
tuwo sai yar gurasa da zuma
ko? Hannah dai murna take
kawai
da ba gida za’a kaita ba Kano
zasu wuce da Yaya Haisam.
Rauda da Hannah suka je suka
shiga mota
a gidan baya suka zauna, Yaya
Haisam da Auwal suma suka
shiga motar, Yaya Haisam ne
yake
tukawa Auwal yana zaune a
gefe, suka nufi get din fita.
Dalibai na daga musu hannu har
suka tafi.
Rabon Rauda da ta yiwa Hannah
magana tun jiya yau ko magana
bata yi mata ba saboda tsabar
tana
kishi da ita wai saboda Yaya
Haisam yana ji da ita, itama ya ce
kanwarsa ce, yanzu kuma taga
yan uwantakar ta tabbata gata
a motarsu Yaya Haisam zai wuce
da ita gidansu ma. Ta kalli
Hannah ta
yamutse fuska ta ce “Kema Kano
zamu da ke kenan, daman a
Kano kike baki taba gaya mana
garinku ba? Hannah tayi shiru ta
rasa amsar da zata bata. Haisam
ya ce “Eh Rauda da ita zamu je
Kano a gidanku ma zata zauna
kinga sai ku dinga karatu a gida
tare ko? Rauda ta ce “Sai ka ce
basu da gida ai a gidansu za’a
nemeta. Cikin rada Hannah ta ce
“Babu wanda zai nemeni, ni
bazani gida ba. Ta mudubi
Haisam yake kallon bakinta yayi
murmushi kawai.
Haisam ya nufi hanyar cikin
Kazaure Auwal ya dubi
Haisam ya ce “A’a Haisam ina
zamuje mu da zamu
kama hanyar Kano. Haisam ya ce
“Cikin gari zani akwai wacce
zamu dauko. Basu tsaya a ko ina
ba
sai a kofar gidan uwar biyu,
daman a shirye take suna aika
yaro yayi sallama ya ce inji
Malam Haisam
sai ta fito da gyalanta daman a
shirye take tsaf ta fito.
Bayan sun gaisa Haisam ya ce da
su Rauda su matsa mata ta
zauna, suka matsa ta shiga ta
zauna
a kujeran baya sannan suka
gaisheta dukkanninsu. Haisam
yaja mota suka tafi bai tsaya a
ko’ina ba sai a babbar tashar
Kazaure ya sami waje a bakin
tasha ya tsaya ya juya ya kalli
uwar biyu da Hannah ya ce “To
anan zaku hau mota ko?
Uwar biyu tace “Eh akwai mota
har Babban -mutum a nan,
Uwar biyu ta yunkura zata fita ta
juya ta kalli Hannah wacce bata
da niyyar fita bata masan da ita
za’a fita ba a tunaninta uwar
biyu ce kawai zata
sauka ita kuma su kara gaba su
tafi Kano. Sai taji uwar biyu ta ce
“To Hannatu fito mu tafi ko?
Cikin
rudani Hannah ta juya ta kalli
Haisam don jin abunda zai ce sai
ya rasa me zai ce mata kwai ya
sunkuyar da kansa kasa ya kasa
magana, ya fito daga motar ya
bude but ya dauko jakar
Hannah.
Nan da nan kwandastocin mota
suka zo suna cewa “Babura
zaku hau ne, ko Daura? Uwar
biyu ta ce
“Motar Babura zamu hau sai mu
sauka a Babban- mutum. Haisam
ya mikawa kondastan da zasu
Babban-mutum jakar Hannah,
uwar biyu ta ce “Af har yanzu
Hannah bata fito daga motar
bane?
Haisam ya leka cikin motar ya
tsaya yana kallon Hannah baice
mata komai ba, ta sunkuyar da
kai
cikin sanyin jiki ta janyo jakar
littattafanta (school bag) ta
rataya ta juya ta kalli Rauda ta
kalli Yaya Auwal ta ce “Na tafi
sai anjimanku.
Rauda tayi murmushi ta ce “Au
har da ke zaku shiga motar haya
kin fasa zuwa Kanon ne?
Hannah
ta kada kai kawai sannan ta
fito. Yaya Auwal yana yi mata
wasa yana cewa “Af ashe ke
yar kauye ce ma, motar Babura
zaku hau ko? Hannah ta fita ba
tare da ta bashi amsa ba.
Haisam da Hannah suma
suka nufi cikin tasha daman
uwar biyu da kwandastan daya
dauki jakar sun shige cikin
tasha. Motar bus ce wacce baifi
mutane hudu ba a ciki bata cika
ba. Uwar biyu ta zauna a kujerar
baya
aka saka jakar kayan Hanna a
but Hannah ma taje kusa da
uwar biyu ta zauna, jikinta sanyi
kalau
kamar marar laka hankalinta a
tashe yake kamar wacce za’a
kaita lahira ba gidansu ba.
Haisam ya zaga ta wundon
uwar biyu dake zaune ya
danko kudi ya mika mata ya ce
“Ga wannan kuyi kudin mota
dan karku matsu ki biya kudin
kujerun bayan a barku ku kadai
sannan ki fito ki shiga Aishalle
super maket kafin mota ta cika
ki suyowa
Hannah sabulun wanka, wanki,
man shafawa dana gashi. Biskit
da alewowi ta yiwa yan
gidansu
tsaraba. Ya sake debo wasu
kudi masu yawa ya ce “Wannan
kuma ki ajiye da zarar hutu ya
kare ya rage kwana biyu kije ki
taho da ita ki kawota gidanki
zanzo in kara yi mata siyayya na
mayar da
ita makaranta. A cikin kudin ki
bawa Mahaifinta dan na
kashewa ki gaya masa lallai-lallai
hutun kwana arba’in da biyu
aka basu da zarar hutu ya kare
za ki zo ki dauke ta inji ni za ki
ce. Ki san dai kalaman da zaki
gaya masa na kwantar da
hankali kada ya
hanata dawowa kinsan tsofaffin
nan namu, kice ke uwar dakinta
ce a wajenki take a makaranta
na
Nina hadaku, ki ce ina gaishe shi da
kyau. Uwar biyu tayi godiya ta
shi albarka kamar ita aka bawa
kudin ko jikarta. Ya dauko wasu
kudin ya mikawa uwar biyu ya
ce “Ki sayawa Hannah sarka da
dankunne na jiyal mai kyau ki
bata. Uwar biyu ta ce “Kai kudin
yayi yawa Malam Haisam duk a
cikin wannan ya isa
nayi mata siyayyar, ya ce “Ba
komai na gode uwar biyu Allah
ya kiyaye hanya ta ce “Amin
Malam
mune da godiya. Ya zagayo jikin
wundon da Hannah ke zaune
tayi tagumi ta langwabar da kai
a
jikin wundon mota hawaye ne
yake sulalowa daga idanuwanta
daya bayan daya.
Nima kawai sai naji hawayen tausayi ya fara biyo kunci na

Mu tara donjin yaddah komar Hannah kauye zai kasance  shin zata samu tarbar kirki ko kuwa????

Advertisements

_____

Ina zan Sani mu hade  gobe insha Allah

Advertisements

_____

About AIS

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Advertisements _____ Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *