[Advertisements⬇️]

Gangar jikinsa na aura4 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hausa novels
 GANGAR JIKINSA NA AURA

CHAPTER 4

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

2pages is gone
ya lullubeta ”
tacehakane malam haisam ni dana
ke cikinsu
yangulma ko sun tambayeni ni nasan
me zan
fadamusu” haisam yace” yauwa ku dauki akwati
da bokiti da katifar kamar yadda
nace akai store
aajiye, sai da safe” suka ce allah ya
kaimu”uwar
biyuta kama akwati ta dora akan hanne ta dauki
bokiti,da katifa a daya hannun suka
doshi store din
kicininda suma suke boye shirginsu .
Malam
haisamkuma ya rataya jakarsa ya nufi gidajen
malamai (staff qurters). Zuciyarsa
cike da
tausayin yaddarayuwar hanne take.
Kuma da burin
canza matanan gaba
               * * * *
HAISAM ABDULHAMID
ZAKAR Sunanmahaifinsa ne
abdulhamid zakar.
Mahaifiyarsakuma sunanta NANA
HAUWA’U
Wacce a yanzu akafi saninta da hajiya nana ko
kuma barista nana kasancewarta
kwararriyar lauya
ce. Mahaifinhaisam haifaffun
unguwar kwalli ne a
kano. Kumasun fito daga tushe daya yar kanwace
aka hadasu aure a lokacin alhaji
abdulhamid ya
gama karatumdigiri dinsa a london
yana da
shekaru ashirin dabakwai ita kuma hajiya nana ta
gama karatun sakandire tana da
shekara goma
sha shida.Dukkaninsu iyayensu suna
da matukar
arziki. Don haka an sakar musu kudi yadda ya
kamata antafka musu kerarren gida,
motoci an
kuma bawa alhaji abdulhamid jari
mai tsoka yana
juyawa itakuma hajiya nana ta fara karatunta na
law a jami’a bayero ta kano. Allah
ya albarkacesu
da ya’yahudu, uku maza mace daya
itace autar.
Wacce ahalin yanxu ko yaye ta ba ayi ba karama
ce.Babban shine yaya habib yanzu
yana da
shekaratalatin , mai binsa shine
abdulhamid ake
kiransa da haisam yanzu yana shekararsa ashirin
da shida mai binsa iziddeen
shekarunsa ashirin da
uku. Sai da iziddeen ya gama
sakandire ya shiga
jama’a sannan aka yi masa kanwa mai shekara
daya anakiranta da amratu.Girma
yazowa alhaji
abdulhamid da matarsa amma
kumakarfi ya
tasamma ya’yansa zasu iya kula da dimbin dukiyarsada kamfanoninsa
yaya habib ya
kammala digirinsa a jamia’ar a.b.u ya
karanta
business admin a yanzu yana aiki a
kamfanin babansa shine kuma mai zurga zurga
zuwakasashe daban daban na shige
da fice da
kayan kamfanonin.Haisam wanda a
shekarar nan
ya kammala karatun jami’a yakaranta
geography yanzu yana bautar
kasa a
f.g.g.kazaure da zararya gama
kujerarsa ta aiki
nanan na jiransa a dayadaga cikin kamfanonin
mahaifinsa. Na uku wato
izziddenyana shekara
ta uku (level 3)a jami’ar bayero ta
kano yana
karatun law don yagaji mahaifiyarsa wato barista
nana wacce itace babbar lauyar
kamfanonin . Tana
kuma farin cikin ganin dayadaga
cikin’ya’yanta ya
taso gadan gadan da karatun law wanda a
cikin’yan shekaru kalilan zai gama ya
zama
cikakken lauya ya canjeta alhaji
abdulhamid ya
dankawa yaya habib ragamar aiki ya koma gida ya
zauna yana hutawa sai
dai yajekamfanonin fisha
yaga yadda aiki yake tafiya yakoma
gida.Dan lelen
abba da umma wato haisam shine yafi kowa shagwaba a gidansu ko
kuma nace shi
akafi shagwabawa tunyana kankani.
Amma ai
izidden ne yakamata yayi shagwaba
kasancewarsa ya dade yana auta kafin ayi
masa kanwa ammashi
yana gefe tun suna yara haisam ne a
kancinyar saboda tsananin biyayya,
ladabi , tausayi
da jinkai irin na haisam shine ya kara masa fada a
wajen mahaifansa sunfisha’awarsu
zauna suyi hira
da haisam sau dubu da suyi
Da yayansa habib tun
suna yara saboda haisam yake magana acikin
nutsuwa yake kalamansa masu
muhimmanci
akoda yaushe fuskarsa cike da
annuri(fara’a),wasa
da dariya damanya dayara. Bashi da raini ga
hakuri , baya ga zunzurutunkokari da
Allah ya
bashi a bangaren karatunsa dukka
akur’ani da
bokon yasan alkur’ani kamar me a kansa duk
gidansu babu mai iliminsa. Hatta
mahaifinsa yakan
yi masa tambayoyi akan duk wata
matsalarsu ta
addini ko ta zamani, yana datsananin hakuri sau
tari ana masa abu da yawa yayi
hakuri.Ammakuma duk gidansu babu
mai zuciya
kamarsa idan aka kureshi, idan yayi
fushi abin babu kyau mai hakuri bai iyabacin rai
ba.Da farko a
enugu state aka turashi bautar kasa
(n.y.s.c)kasancewar shakuwa da
sabon da
mahaifansa suka yi dashi basa so yayi musu nisa
don haka alhaji abdulhamid yasa
adawo dashi
kurkusa saboda yasan manya
manyan kasar
nandaga yan boko har rukakkun yan kasuwa.
Ammaduk da haka haisam yana
korafi shifa
kazaure yayi nisa da kano a
dawodashi cikin kano
inda kullum zaina kwana gida, dakyar dai
akablallasheshi yayi hakuri duka duka
bazai yi
shekaradaya ba zai gama ya dawo
gida gaba
daya. Don haka duk juma’a yaketafiya gida wani
lokaci ma a kanon yake yin
sallar juma’a saivlahadi
da yamma ake dawo wa dashi. Gashi
yanzuma
baifi saura wata uku ba ya kare bautar kasa
kwatakwata ma yakoma inda yake
muradi.Bayan
tafiyar hanne gidan uwar biyu da
kwana uku wato
ranar laraba da sassafe sai ga wata mota an kawo
hanne makaranta haisam ya roki wani
abokinsa
safiyanu yaje cangidan uwarbiyu ya
dauko hanne
da kayanta ya kawotamakaranta. Haisam ya gama
mata siyayyarta kakaf ko
yaran attajiran makarantar
baza su fita kaya ba
(provision)kayanmakarantarta
(uniform)suma har kala kala bibiyu yayi
mata takalma kuwa kala kala akwai
kito, sandal ,
kambos fari dabaki tsadaddu, silifas
dan madina
har biyu, ya siyo mata dawasu yan kanti riga da
siket suma kala biyu. Yasuyo
matajakar zuba kaya
mai kyan gaske yar madaidaiciya
wato(travelling
bag)a ciki aka zubawa hanne kayansawarta, nata
nada kuwa yana gidan uwar biyu,
kayan tande
tande damakulashe kuwa abun baya
lissafuwa
kama daga biskit kalakala, alewa (chocolate)indomie, madara,
milo,sugar
,complakes da dai sauransu ko garin kwaki
babu balle
wani kanzo irin na yan makaranta
makilin da brush hadaddu, mayukan shafawa da
sabulansu
masu kamshi gamayukan gashi cike a
akwatin Hanne
sanye take da kayan makaranta
(uniform)kafar ta kumafarin kambos ne da farar safa
an tufke kitson
kantada waniribom mai kyau mai
fulawa, duk
wanda yaga hanne kwanakibiyu da
suka wuce a yau dai bazai gane taba tayifari
kyal kamar yar
larabawa, ashe mai dangwali yaba
nebda
bakin kwalli suka cabe mata fuska
tayi baki kirin. Safiyanu yazobakin offishin malamai
ya tsaya da
motarsa sannanya fitodaga ciki ya
juya ya kalli
hanne wacce ke zaune abaya
tanakokawa da murfin kofa ta kasa budewa abunka
Da
Yar kauye.Wannan ne karo na farko
da hanne ta taba hawa irin wannan motar
don haka bata san ina
zata ja kofa ta bude ba. Safiyanu yazagayo dasauri
ya bude
mata, ta fito yace” to dauko jakar
litattafan
nakimana” hanne tasa hannu ta
jawo wata bakar jaka(schoolbag)tsadadda mai kyan
gaske, yar
madaidaiciya daidaibayanta cike
take da kitattafan
rubutu da litattafan karatu
(textbook)duk dai kamar yadda aka zano ajikintakardar
babu wanda haisam
bai siya mata ba ga biruka da
fensir da mathematical set din su ya
siya mata .
Safiyanu ya nunawa hanne yadda zaya rinka
ratayawa a bayanta tarataya
suka nufi cikin ofishin.
Suna shiga suka iske wani
malami bayan safiyanu
ya mika masa hannu sun gaisa sai yayi masa
bayanin abinda ke tafe dasu yace
daliba ya kawo,
sai yanuna masa ofishin vice
principal yace nan
zasu shiga.sukayi sallama suka shiga suka iske
vice principal yanaharhada wasu
takardu a
gabansa, bayan sun gaisa safiyanu
yashaida masa
cewa yarinya ya kawo yar aji daya ce sabuwar
zuwa sai ya nemi daya bashi
takardar shaidar
cewar ita dalibarnan makarantar ce
wato(joining
instruction)daman haisam yabashi ya dauko ya
mika masa ya duba yace”sunanta
hanne habu
imamu daga babban mutum ko ?
Safiyanu yace
”eh,”vice principal din nan ya kurawa hanne ido
yana kallonta zuciyarsa cike da mamaki
ga yarinya
kyakkyawa kamar baturiya gashin
kanta har baya
 duk dama antufkemata da ribon amma
kuma sunnan kauyawa gareta gata
kuma daga
kauye. Ya ce a ransa” wata kila dai
asalin
garinsune babban mutum din amma daga birni
take, can yanisa yace”babu komai,”
ya jawo wani
littafin rasitai ya budeyace
da safiyanu” sai ku
bibbiya kudaden in baku rasitai dasauri don yanxu
lokacin assembly ne, don taje ta
shiga
cikin dalibai ayida ita. Vice principal
ya lissafawa
safiyanu yawan kudaden dazai kawo safiyanu ya
dauko ya bashi, shi kuma yana
rubuta rasitai har
ya biya kudin komai  ” sannan
yafadi
sunan dakin da zata je, sannan zata je j.s.s. 1A
ajin malam haisam sunan ajin, yanzu
ka kaita hall
ayi assembly da ita,kayanta kuma a
barsu a nan
bakin staff room ana tashi tazo zamu samaigadi da
prefect din dakin suje ta bata
gado.Safiyanu ya
ce”to” yayi godiya suka fito yana
sake yiwa
hanne bayani akan abinda vice principal ya ce,
yana kuma kara lallashinta
ganinyadda nan da nan
ta canja hankalinta yayimummunan
tashidaga
shigar su ofishin vice principal duk kwalla tacika
mata ido saura kiris ta fashe da
kuka. Yace mata”
kar kiyikuka nanmakaranta ce
karatu kawai za.a
koya miki babumai zaginki balle duka kinji. Gashi
ajin malam haisam za,a kai ki don
haka baki da
matsala zai kula dake”suna tsaye a
bakin baranda
yana yi mata nasiha saiga viceprincipal ya fito
daga ofishinsa zai tafi hall
wajen assemble yyace” ah
har yanzu bata tafi assembly ba ai
gara kuyi
sallama ta tafi,” safiyanu yace ” aima shikenan
mun gama daman hall din zan
tambaya don bamu
ganshi ba,” vice principal yayi musu jagora har cikin
hall din yashige
da hanne a lokacin principal tana bayani hall din
yayi tsit kowa yana sauraro. Amma
daga shigowar hanne da
vice principal
sai kowa
hankalinsa yakoma ga kallon hanne.
Hanne ta zama yarinya ”yar dagwas ‘yar
karama maikyan
gaske akwai dubbunan dalibai a
makarantar daga
jahohi daban daban amma babu mai
kyawun hanne wato kamar wata tauraruwa ce mai
haske a cikin
taurari. Sai sheki take da farar
fatarta hanci har
baka, ga dan karamin baki,gazar
gazar gashin gira dana ido fatar jikinta luwai luwai
irintayan
hutu amma ita dai daga innallahi ne. Ga
ido dara dara
bata da kibakuma bata cika tsaho
sosai ba gata dirarriya duk dadaikarama ce
masassakin budurci
bai fara sassakataba. Wasukitso ne
yiri yiri aka
yarfa mata kamar bada hannu aka
yisuba. Hanne tayi kyau kwarai da gaske a
cikinkayanmakarantar
nan ga ‘yar jakar litattafanta a
baya.Babu
wandazai kalli hanne bai sake
juyowa ya kalli halittar ubangiji ba.Dalibai
manyansu da yaransu
babu wacce bata cedama
nicewannan ba ko kuma
ace ‘yata ce a ransu ba.
Hatta haisam wanda ke tsaye a bakin kofa bai gane hanne
bace. Suka zo
sukawuce ta gabansa ya bita da
kallo sai dai a
zuciyarsa yaketambayar kansa da
kansa ina nasan wannan yarinyar?Tabbasa na santa
a wani waje,
sai daga baya zuciyarsa ta bashiamsar
cewa wannan
itace hanne habu kenan.
Yayi matukar mamakin ganin yadda hanne ta koma haka a
kwanabiyu,hanne ta tsorata ta kuma
rikirkice
ganin dubbunnan idanuwa caa a
kanta, ta tsaya
cak, ta kasa tafiya tana shirinfashewa da kuka.Vice
principal yayi kiran wata prefect
dake tsaye agefe
yace tazo ta kaita layin ‘yan j,s,s
1A. Tazo ta
kama hannun hanne takaita layin ajinsu ana ci
gaba da assembly kamar yadda
sukasaba. Bayan
principal ta gama jawabinta,
vice principal ma ya
fadi albarkacin bakinsa sai aka nemi sauran malamai sucewani abu akan
dokar
makaranta. Bayan sun gama aka
yi national pledge
kowa ya kama gabansa, ya
nufi ajinsu. Hanne ta tsaya cak a inda take tsaye tana
kallon
dalibai kowa yanatafiya ajinsa ta
rasa ina zata
nufa. Haisam ya matsokusa da ita
yace” hanne yaya kika tsaya bakya ganin kowa
yanufi ajinsu ke
kika tsaya idan baki sani ba, ba sai
ki tambaya
ba.To nan makaranta ce kowa ta
kansa yake, gara ki rinkatambayar duk abinda baki
sani ba, muje in
nuna miki ajinnaku, hanne tace” to”
ta bishi suka
doshi bangaren da ajujuwa suke yaci
gaba dayi mata nasihohi akan kada ta sake ta
zama wawuya,
idan bahaka ba sai sauran dalibai su
raina mata
wayo tazama duk abunda bata sani
ba ta tambaya musamman idan malami yana darasi
idan bata
ganeba tayi masa tambaya.Hanne
nasauraro da
alama kuma nasihohin suna
shigarta.Haisam ya kalleta yayi dariya ya ce” hanne ince
kin
zama cikakkiyar daliba babu wannan
damarar?
Hanne ta kyalkyaleda dariya haisam
yace” to tunda kin zama yar birni ‘yar bokomai aji to
yanzu komai
naki zai koma na aji, kin san
abundanake nufi?
Hanne tace ”a’a” yace to sunanki zai
tashi daga HANNE HABU IMAMU ZAI
KOMA HANNAH

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]