[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
Chapter 35
Haisam ne ya shigo ya tarar da
Hannah a tsugune yaje ya tabata
yaga taki dagowa yasa hannu ya
tasheta tsaye yaga kuka take yi,
jikinta gaba daya karkarwa yake
idonta ya ki budewa gaba daya.
Ya
girgizata yana kiran sunanta ta
rushe da kuka ta rungume shi ta
ce “Yaya daman ana mutuwa a
dawo? Ya ce “Ban gane ba? Ta
ce “Iya Salmai na kuka a daki
wai jiya taga Babana har sunyi
magana da shi. Haisam yaja
hannunta zuwa cikin dakin
wajen Iya Salmai. Haisam yasha
wuya kafin ya lallashi Iya Salmai
ta daina kuka ta fara amsa
tambayoyinsa. Iya Salmai ta
bude baki ta fara
basu labari tiryan-tiryan. Ta ce
“Duk ranar kasuwa ina kai tallar
zogale ina zama tare da fulani
masu sayar da nono. Muna
labari dasu har suke bani
labarin wani bawan Allah
wanda yanzu ya zama
Malaminsu shi yake koya musu
karatun Sallah da basu iya ba sai
zuwansa garinsu. Suke cemin
mutumin basu san taka maimai
ko dan asalin wanne gari bane
don yaki ya fada. Yayi doguwar
suma har an binne shi masu
binne shi na juyawa sai su kuma
fulanin rigarsu suka kawo gawa
kusa
da wannan kabari sai suka ga
kabarin yana motsi, sai aka ce a
tona aga ko meye saboda daga
dukkan alamu yanzu aka rufe
kabarin watakila bai mutu ba
doguwar suma yayi yanzu ya
farka. Suna tonowa saiga
mutum mai rai bai rasu ba yana
salati, aka garzaya dashi asibitin
Babura wajen watansa guda
baya magana Malam Sule har
saniyarsa ya sayar yana sayawa
mutumin magani.
Bayan an sallamesu daga asibiti
ya warke ragas ya ce sunansa
Malam Garba amma bazai koma
garinsu ba saboda yasan an
gama zaman makokinsa ansan
ya mutu zasu tsorata suce yayi
fatalwa. Iya salmai ta sharbe
hawaye ta ce “Da raina na kawo
ko Malam Habu ne sai na ji ance
Malam Garba sunansa. Na
tambayesu ina ne garin su
mutumin sai suka ce bai fadi shi
ko dan wanne gari bane yaki
fada sai ya ce yana rokarsu dasu
rikeshi su taimake shi shi kuma
zai dinga taya su da kiwo zai
dinga koya musu karatu. Aka
gina masa bukkarsa a bayan
gidan Malam Sule. Malam sule ya
rike Malam Garba tamkar dan
Uwansa suje kiwo tare suci
abinci tare ya koya mana karatu
da daddare bayan kowa ya
dawo daga kasuwa
mutumin yana da kirki. Cikin
zumudi Hannah ta ce “Da ganan
sai akayi yaya? Iya Salmai ta ce
“Sai nabar maganar anan na
manta da ita saboda zaiyi wuya
ace Malam Habu ne kuma bance
su suffantamin yadda mutumin
yake ba na dai tambayesu yana
zuwa kasuwa wataran su
nunamun shi, suka ce baya
zuwa ko ina kullum
yana cikin riga. Wataran wani
mijin kawata ya zo ya same ni ya
ce yau yaje wata riga wajen
kanwarsa da take aure a rigar
yaga wani mutum kamar an
tsaga kara kamarsa daya da
Malam
Habu, har na tambaye shi yana
da wa ko kani a Babban-mutum
ya ce min bashi da kowa. Sau
uku
mijin kawar tawa idan yaje rigar
yake zuwa yake fadamun irin
kamar mutumin da yake gani da
Malam Habu harta baci,
tafiyarsu, maganar komai iri
daya da Malam Habu. Sai jiya na
ce muje rigar
nan inga mutumin nan. Wallahi
ina zuwa saiga Malam Habu, na
yanke jiki na fadi sai yazo ya
tasheni ya ce “Salmai lafiya? Na
sake tabbatarwa shine sai ya ce
“Ina yar Baba? Hannah ta rirrike
Iya Salmai tana kuka tana cewa
tashi ki kaini gurin Babana in
ganshi. Haisam ya rike baki
kawai yana
kallon ikon Allah sai Kabbara
yake yana cewa “Allahu Akbar.
Ya jawo Hannah jikinsa yana
lallashi ta kwantar da hankalinta
yau komai dare zasu je su
ganshi insha Allah. Wada ya ce
“Iya da kin lallabashi ya dawo
garin nan kun taho tare. Iya
Salmai ta ce “Nayi-nayi yazo mu
tafi yaki ya ce kuma kada in
fadawa kowa na ganshi yace
baya
son ya sake irin rayuwar da yayi
a baya tare da Iya Abu da
*ya*yanta shi zamansa a
rigarma yafi masa alheri da
kwanciyar hankali, daman
Hanne yake ji ya aiko a duba
halin da take ciki ance *yan
Uwanta sun tafi da ita Niger.
Shikenan hankalinsa a kwance
sai dai wani lokaci idan ya
tunata zaiyi
kuka harya godewa Allah.
Hannah ta girgiza kai ta ce
“Babana kuwa ki ka gani Iya
Salmai? Kai bashi bane Babana
ya mutu, mutuwa daya ce Yaya
Haisam ka tuna kaifa kace min
ba’a mutuwa a tashi. Haisam ya
ce “Hannah kar kiyi mamaki ikon
Allah ya wuce haka. Ana samun
irin haka mutum yayi doguwar
suma a binneshi ashe bai mutu
ba, aga kabarin yana motsi a
tono kuma mutum ya tashi ya ci
gaba da rayuwa sai dai wasu
sukan rasa ido ko kansu ya
karkace
ko bakinsu ya juye. Yana faruwa
amma a mutane goma baifi a
sami irin haka sau daya ba,
zamu je
mu gani Allah Yasa shine
Hannah ki huta da koke-koken
nan da kullum ki keyi na rashin
Mahaifanki. Iya Salmai ta ce
“Shine mana na ganshi har
munyi magana da shi, Malam
Habu ras yake babu inda
ya lahanta a jikinsa. Haisam ya
ce “Ikon Allah ne, ba tare dake
muka ji shirin INDA RANKA ba na
FREEDOM RADIO akwai mutumin
da aka binne shi sau uku ana
tonoshi ashe bai mutu ba suka
yi hira da shi shima ras yake ba
inda ya nakasa.
Hannah ta mike da sauri tana
cewa “Ku taso muje. Jikinta
rawa yake kamar ta zama
tsuntsuwa ta
dira a gaban Mahaifinta. Haisam
ya cewa Shehu direba ya zauna
shi da Wada zasu je su dawo.
Haisam na tukawa Hannah a
gefensa Iya Salmai a baya tana
nuna hanya suna tafiya. Sun isa
rigar suka iske bukkarsa babu
kowa wani bafillatani
yana biye da shanunsa suka
tambayeshi ko ina Malam Garba
yake sun leka bukkarsa baya
nan sai ya ce “Yanzun nan ya
rabu da su shi da Malam Sule
suna can kogi shanunsu suna
shan ruwa. Ya kwatanta musu
inda kogin yake suka nufa. Har
suka isa surkukin da mota ba
zata iya wucewa ba
suka ajiye motar suka fara
dabawa da kafa tun daga nesa
suka hango shanu suna shan
ruwa da
wasu mutane guda biyu suna
zazzaune. Suna karasawa
mutanan na juyowa sai ga
fuskar Malam Habu tar muraran,
ya gigice ya zabura ya mike
tsaye Hannah sai ta kwalla kara
ta rike kai ta
sulale ta fadi a sume Haisam ya
riketa dan razana.
Suka taru akan Hannah ana
zuba mata ruwa sai ta farfado,
fuskar Mahaifinta ta sake gani,
ta fada a
tsorace “Baba kai ne kuwa? Ya
matsa hawaye ya ce “*yar Baba
nine, suka rike juna sai kuka
suke
tamkar ransu zai fita yayin da
farin ciki tamkar ya hallakasu.
Wohoho hasko min zukatan
wadannan bayin Allah Uba da
*yarsa masu tsantsar son juna
da shakuwa.
Hannah ta ce “Baba kai ne
Uwata kai ne Ubana, kana raye a
duniyar nan baka mutu ba kaki
ka nemeni ai sai kazo in ganka
kayi min bayani in yaso sai kace
kar in fadawa kowa.
Malam Habu ya ce “Yi hakuri
*yar Baba da ace haka kawai
nazo miki tsorata zakiyi, ko
kuma ma
ki rasa hankalinki ban san ta ina
zan baiyana kaina gare ku ba,
da dai aka ce min kin bar
hannun Abu hakika na san kin
fita daga kangi. Suka karasa
cikin bukkarsa inda suka
zazzauna har Malam Sule.
Malam Habu ya zaiyane musu
labari kamar dai yadda fulanin
nan suka gayawa Iya Salmai.
Hannah ta bawa Babanta labarin
rayuwar ta har zuwa rana ta irin
ta yau ya dinga hawaye daga
karshe yayi hamdala ya mikawa
Haisam hannu suka gaisa yana
ta shi masa albarka. Daga karshe
Hannah da Haisam sunyi-sunyi,
juyin duniyar nan akan yazo su
tafi da shi Kano yaki.
Kasancewar Hannah tasan yana
matukar son yaje kasa mai
tsarki wato Makka sai ta ce
“Baba Makka fa zamu wuce da
kai. Tana ambaton Makka sai ya
ce “Indai Makka ce zanje kunga
sai inyi zamana acan in dinga
ibada har Allah Ya dauki raina,
kuje ku
gama shirye-shiryen ku kuzo ku
dauke ni ku kaini,
Allah Ya shi muku albarka.
Hannah ta nunawa Haisam ya
tafi kawai ya barta ita zata
zauna anan da Babanta tunda
bazai yarda ya bisu su tafi dashi
ba. Dakyar Haisam, Malam Habu,
Malam Sule da
Iya Salmai suka lallasheta ta
tashi suka tafi tana rusa kuka ita
a wajen Babanta zata zauna. Ta
bisu
bisa sharadin za suje Babban-
Mutum su kwana washegari in
zasu tafi su sake biyowa ta
ganshi sannan su wuce Kazaure
sai su wuce Kano kuma duk
bayan sati zata dinga zuwa tana
ganin
Mahaifinta.
Suna tahowa a mota Hannah ta
ware take ta murna kamar zata
zuba ruwa a kasa tasha. Ta ji
zuciyarta wasai tamkar bata
taba jin bacin rai a rayuwarta
ba, Haisam yaji wani sabon farin
ciki
saboda Hannarsa no more cry
(babu yawan kuka). Suna shiga
Babban-mutum suka bullo ta
kofar gidan Iya Abu har sun
wuce Hannah ta cewa Haisam ya
dawo
baya zata shiga ta gaishe da su
Iya Abu. Da farko Haisam yaki sai
da Iya Salmai ta sa baki sannan
ya bar Hannah, ta ce ya taho su
shiga tare suka dunguma su
duka da Iya Salmai cikin gidan.
Suna shiga tsakar gidan suka ji
yiiim a fuskarsu an watso masu
tsommokarai. Wasu mata ne
guda
biyu sun damko wata tsohuwa
zasu yi waje da ita.
Hannah ta jawo tsohuwar daga
hannun matan ta ce “Ku lafiya
ina zaku kai ta, me tayi muku?
Haisam ya tashi tsohuwar zaune
ya ce “Iya mai ya faru, ta ce “Ku
taimakeni bayin Allah wadannan
mugayen matan zasu kashe ni
wuya su ke bani.
Hannah ta matso kusa ta ce “Ke
wacece, kuma meye hadinki da
su? Tsohuwar ta ce “Sunana
Abuwa da gidana ne muka
sayar yanzu kuma haya nake a
ciki ban biya kudin haya ba
shine za su
kore ni. Sai Hannah ta ce “Iya
Abu kece? Ta ce “Ni ce, wace ce
nake gani kamar Hanne?
Hannah ta ce
“Ni ce, ikon Allah Iya Abu kece
kika zama haka, meya same ki a
ido daya ya tsiyaye? Ga kafarki
daya ma ta kumbura kamar
jarka ciwon kafa kike yi? Iya Abu
ta rushe da kuka, Haisam yayi
murmushi ya ce “Wai yanzu
Abun ce ta zama
haka? Iya Salmai ta ce “Abu ai
tayi kyan gani tun wata sadaka
mai tsoka da wani mai kudi ya
basu
dubu uku-uku ita da abokin
bararta Alh. Bilya, kunsan
kuturtar tasa ta baiyana, matan
da *ya*yan
duk sun watse kudi babu. Itama
Abu duk *ya*yan nata sun zama
*yan iska matan da mazan, sun
sayar da gidan Uban yanzu haka
haya take dan ba su da gidan
zama.
Matan gidan suka ce “Sun sayar
mana da gidan muka ji
tausayinta muka sakata a daki
daya haya
gashi yau wata biyu bata biya
mu ba *ya*yan nata *yan daba
basu je sunyo dabar ba sun biya
mata.ba
Wallahi yau bazata kwana a
dakin nan ba sai dai in ta shiga
cikin rumbun nan mai gidan
tururuwa.
Hannah ta bude baki zata roki
matan Iya Salmai ta katse ta ta
ce “*yar Baba barta ta kwana a
runbun tururuwar ko kwana
daya ne taji idan da dadi, kin
manta ranar da ita da abokin
bararta Alh.
Bilya suka yi watsi da kayanki
suka ce ki koma runbu. Haisam
ya ce “Haka akayi, ai kin bani
labarin yadda kuka yi, ta kwana
ko sau daya ne ta ji “Iya Abu ta
rushe da kuka tana cewa “Yanzu
yaya za’ayi mutum dan Adam
ace ya shiga wannan runbun
mai tururuwa ya kwana.Iya
Salmai na kwasar kayan Iya Abu
tana watsawa cikin runbun tana
cewa. “Kwana daya kawai zaki yi
kafin Hanne tayi tunanin inda
zata samar miki ki dinga kwana.
Hannah taji wani hawayen
tausayi
ya zubo mata ta fita kofar gida
tana hawaye.
Haisam da Iya Salmai kuma suna
can suna lallashin Iya Abu tayi
hakuri ta kwana a gidan
tururuwar zuwa gobe, Iya Abu
ta rarrafa ta shiga rumbun tana
rusar kuka tana cewa “Duniya ta
juya min baya yau na shiga uku
na lalace. Haisam da
Iya Abu suka fito kofar gida
suka sami Hannah da Musbah
dan gidan Iya Abu, kaca-kaca da
shi kamar mahaukaci talauci
tsantsa. Hannah ta girgiza kai ta
ce “Musbah ya haka? Ya fashe
da kuka ya fara zaiyanawa
Hannah irin halin da suke ciki na
talauci da bala’in da yake ta
bibiyarsu ya bata labarin cewar
sunyi aure sun kai matansu
gidan suna zaune da Iya Abu.
Iya Abu ta fara yi musu masifa
tana so ta gallaza musu su kuwa
suka bijire mata, har wata rana
suka rufe gidan babu kowa
suka yi mata duka har sai da
suka tsiyayar mata da ido daya
daga karshe ma suka fice suka
fasa auran. Mu kuma a
tsakaninmu muka dinga fada
akan gidan, matan su Mahajana
sun
zama karuwai suma suka ce nan
gidan zasu dinga kawo maza
mu kuma muka ki yadda a kayi
ta
rigima daga karshe gidan aka
sayar muka raba kudin ba tare
da Iya Abu ta sani ba duk muka
watse, yanzu sai tayi bara
sannan ta biya kudin haya. Ga
wani ciwan kafa, kafarta ta
kunbura
kamar bokiti komai ya cakude
mana. Hannah ta share hawaye
ta ce “A gidan Iya Salmai zan
kwana
gobe da safe ka tattaro min
kanku kuzo ku same ni kafin na
tafi. Ya rakasu har mota yana
soshe-soshe ya ce “To Hanne
bani na kashewa da daddare
mana, Iya Salmai ta ce “Zai sha
wiwin dare kenan. Hannah ta
ciro dubu biyu ta bashi ta
ce “Musbah kar kasha wani
abun maye kaci abinci ka
sayawa Mahaifiyarka abinci ka
kaimata. Ya dinga godiya da
farin ciki. Har zasu shiga mota
saiga Alh. Bilya ya taho ta ce da
su Haisam “Ga Alh. Bilya bari na
bashi sadaka ta karasa wajensa
ta zuba masa dubu biyar a
kwanan bararsa ta ce “Alhaji ga
sadaka. Ya ce “Na gode Allah Ya
karba.
Iya Salmai ta matso kusa dashi
ta ce “Bilya ka gane ta kuwa? Ya
ce “Baturiya ce ne? Kai kamar
balarabiya, daga Makka take ne?
Iya Salmai ta ce “Hanne ce *yar
gidan Malam Habu, budurwarka
ta
da mai dakin haya. Ya sunkuyar
da kai kasa dan kunya. Iya
Salmai ta sake cewa “Ina zaka
jene? Ya
ce “Abu na biyowa muje bara
ance za’a bada sadakar abinci a
kofar gidan mai gari, Iya Salmai
ta ce “Abu tana ciki kayi sallama
a runbun nan mai tururuwa
zaka ji ta amsa. Hannah ta shiga
mota
cike da tausayinsa, Iya Salmai
ma tazo ta shiga, daman Haisam
yana ciki yana kallan su ya
girgiza kai yaja motar suka tafi.
A hanya Hannah take cewa
“Yanzu tun a duniya Allah Yake
sakayya ba sai an mutu ba ko?
Haisam ya ce “Kwarai kuwa
shiyasa a ke son mutum ya
dinga shirya alheri a rayuwarsa.
Hannah ta ce “Allah Sarki yanzu
dubi kudi irin na Alh. Bilya babu
kamarsa a garin nan, dubi isa da
mulki da rashin mutunci irin na
Iya Abu yanzu sun zama a bamu
dan dago-dago. Iya Salmai ta ci
gaba da basu irin bala’in da Iya
Abu da *ya*yanta suke ciki.
Hmmmm su Iya Abu anga rayuwa
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]