[Advertisements⬇️]

Gangar jikinsa na aura30 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter30

Ramlah tayi shiru kanta a sunkuye a kasa jikinta yayi sanyi sai yanzu ta dago ta dubesu tayi ajiyar zuciya ta ce “Naji abinda kuka fadamin nagode. Ta kirkiro wani laujajjan murmushi dakyar ta ce “Hidaya, Aisha da Hauwa kawayena kenan. In tambayeku mana shin Nana Aisha (R.T) matar Manzon Allah (S.A.W) kishiyoyinta nawa ne? Matan Annabi tara ya aura suka zauna tare. Kun manta inda Allah (S.W.A) Ya umarci maza da su auri mataye bibbiyu ko uku-uku ko hurhudu idan sunga baza suyi adalci ba su auri daya. To ashe ba Haisam bane ya kirkiro auren mata biyu don ya cusguna min ko ya bata mun rai shi da amaryarsaba. Hakika na riki wannan hadisin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya ke cewa “Imanin dayanku bazai cika ba har sai ya sowa dan uwansa abun da ya sowa kansa.
Su duka sukace “Allahu Akbar !. Yayin da dukkaninsu suka sake tattaro da hankalinsu ga sauraren Ramlah. Ta ci gaba da cewa “Kuma rai yana son mai kyautata masa. Hannah tana kyautata mun, Hannah tana girmamani haka Haisam yana faranta mun. Kullum addu’a nake Allah Ya zaba mana abunda yafi alheri tsakanina da Haisam. Alherin da Allah Ya zabar mana shine ya kawo Hannah, tsananin kishin da nake dashi da kin Hannah da nake yi da sai Allah Ya yaye min a raina naji ina son zama da ita musamman dana yaba da hankalinta. Ni a yanzu da kuka ganni bani da wani buri a duniyar sai inyi biyayya ga mijina in shiga Aljannah kuma in kiyaye kada in cuci abokiyar zamata mu gama lafiya saboda duniyar nawa take yanzu kana nan an jima babu kai ka mutu ka kuma tafi har abada. Daman yanzu a wannan zamanin da muke duk wani mai hakuri shine abun zagi an dauke shi wawa marar hankali kamar yadda a yanzu kuke daukata to gaskiya ba haka bane nasan abun da nake yi. Ina kuma jin dadin rayuwar aure na a yanzu fiye da rayuwar aurena ada. Kuna murna  kuna jin dadi a zuciyoyinku harma kuna furtawa da bakinku kuna tinkaho da takama kun hana mazajenku aure kuma sun hanu saboda suna tsoronku kuma kun isa, nice marar wayo dana bar mijina ya kara aure har muke zaune lafiya to alhamdulillahi naji dadi. Ku yi hakuri bawai na gwaleku bane, kuma bawai ban gode muku bane naji dadi da kuka hango abunda zai cuceni kuka sanar dani. Sai dai ina ganin  baku fahimci wacece kishiya ba da zaman tare. Sai muke kallon-kallo ni daku, ma’ana kuna mun kallon inama inji abunda kuke cemun, ni kuma ina hango muku wata babbar illa akan mazanku har nake cewa inama zaku yarjewa mazajenku suyi aure kamar yadda Haisam ya kara aure ku zauna lafiya yafi kwanciyar hankali.
Hidaya tasa hannnu ta dakatar da Ramlah ta ce “Karma ki fara hango mana inama mazajen mu su kara aure mu zauna lafiya wanne irin zaman lafiya anyi mana kishiya ai lokacin ma zama zai hargitse. Aisha ta ce “Ke dai Ramlah da Allah Yayi miki zuciya irin ta matan sahabbai kinji dadi kina son kishiyarki amma mu babu sauki idan akayi mana kishiya. Su duka suka kyakyace da dariya suna tafawa. Hauwa ta ce “Kishiya, kishiya Ramlah kinji yadda nake ji kuwa idan naga anyi kishiya a makwabtanmu ma balle a cikin gidana ai har abada bazan yadda da kishiya abokiyar zama ba ce idan kuwa ya kuskura yayi min karshen zamana ya zo a gidan kuma suma sun rasa kwanciyar hankali a zamansu, lallai Ramlah baki san kishi ba. Ramlah tayi murmushi ta gyada kai ta ce “Hauwa kin tabo wani kyakkyawan misali da nake so in baku kince daga ranar da mijinki yayi aure kin bar gidansa, a matsayinki na *yar shekara ashirin da biyar kina nufin idan kika rabu da mijinki kin rabu da yin aure kenan a rayuwar ki har abada? Hauwa Mamman tayi shiru can ta ce “Sai in sami wani in aura. Ramlah ta ce “Saurayi ko bazawari? Tunda ke bazawara ce kinga saurayi ba zai zo neman aurenki ba sai dai wani ikon Allah. Masu mata ne zasu dinga zuwa neman auren ki to su matan da zaki auri mazansu su ba mutane bane da zasu kyale mijinsu ya aureki? Kingafa ko yanzu kin bar sunna don baki sowa dan Uwanki abunda kika sowa kanki ba kin auri mijin wata. To ai haka ne abunda nake nufi da inama zaku yarjewa mazanku su kara aure yafi kwanciyar hankali shine na dade ina son in fada muku abunda yake raina na rasa ta ina zan fara fada muku ku fahimta amma yanzu zan fada muku tunda yanzu mun shiga babban dakin bawa junanmu shawarwari Allah Yasa ku fahimceni kamar yadda na fahimce ku. Hidaya tayi dariya ta ce “Ai yanzu ra’ayoyin mu ya banbanta aminiyata kin baude daga cikinmu kinbi wata baudaddiyar hanya ta gushewar ganewa mun kasa gane kanki. Yaya gashi kiri-kiri ana cutarki kowa yana gani kince ba cuta bace, mufa muna nan akan bakanmu kuma kullum zamuci gaba da fada miki har sai kin gane.
Ramlah tayi dan murmushi ta mike tsaye taje ta rage muryar talabijin din dake kunne ta dawo ta zauna ta dubi fuskokinsu dukkansu sai fara’a suke alamarma dariya take basu, sai itama suka bata dariya ta kyalkyale da dariya suma sai suka yi dariya. Hidaya ta ce “Ai babu abinda zaki gaya mana Ramlah kema kyayi dariya saboda ba’a haiyacinki kike ba tuntuni na fada miki wannan kishiyar taki ta gama dake. Ramlah ta nisa ta ce “Ina da abun cewa ne yasa ma har nake dariya. Ku gafarce ni Hauwa Mamman bari kiji abunda baki sani ba game da mijinki amma ina so ki nutsu kafin ki yanke hukunci dole tasa zan fada miki yanzu ma don kawai ki yarda da bayanin da nake so in wayar muku dakai akai ku ka kasa ganewa, kinsan Amira Nasir? Hauwa Mamman ta zabura ta rike kirji ta ce “Ramlah ina kika san Amira Nasir? Ai ita ce tacacciyar *yar iskar yarinyar dana fada miki *yar Minna ce take yiwa mijina waya tana sonsa amma ban fada miki sunanta ba, nima sai daga baya na binciko sunanta amma ai yanzu ta rabu dashi ko hanyar da yabi ma ta daina bi. Ramlah tayi murmushi ta ce “Haka ya fada miki to ga irinta nan abunda nake fada muku kun kasa ganewa. Da mace tasa mijinta a wani hali na bin matan banza gara ma ka barshi yayi auren. Hauwa Mamman ta gyara zama ta narairaice ta ce “Ramlah meke faruwa ne gabana faduwa yake fadamun gaskiya. Ramlah ta nisa ta ce “Gaskiya basu rabu ba kuma sau biyu muna haduwa dasu a London ni da Haisam duk fitar da yake yi da ita yake fita ina amfanin haka bayan Uwar dukiyar da yake tura mata. Ai ba a London kadai ba jama’a da yawa sun sani kece baki sani ba ana tayi miki kallon wawiya. Kinga da irin wannan harkar gara ma ace ya auro miki ita cikin gida kun zauna tare kamar ni da Hannah dai. Hauwa Mamman ta dora hannu aka ta tsala kuka, Aisha Sulaiman na rirriketa kuka take tana cewa “Wallahi Ramlah gara ke daya auro miki Hannah ashe, yanzu haka Ibrahim zaiyi mun na shiga uku yanzu Ramlah yaya zanyi? Ashe kowa ya sani baku fada min ba? Ramlah ta juya ta kalli Aisha Sulaiman taa ce “Ke kuma da kike ganin kin hana Mukhtar aure ya hanu to kece baki sani ba yana nan tare da yarinyar kuma yakai kudin auren a boye, yana gina mata gida a Abuja can zai kaita inda yake aiki ayi auren karki sani. Hidaya ko ba kawar yarinyar bace take fada mana tare dake ba? To ashe ni da Haisam ya sanar dani ga wacce yake so ya aura sai in masa butulci ince ba zamu zauna lafiya ba. Aisha Sulaiman tahau cire mayafi tana fisge dankwali ta ce “Ramlah da gaske kike ko da wasa na shiga uku na lalace. Ramlah ta ce “Baki lalace ba Aisha darasi ne a kanku domin kunsan kara aure fadar Allah ce babu wacce ta isa ta soke ta ce ba za’ayi ba. Hidaya ta rike baki ta ce “Kai duniya abin tsoro Ramlah na fara tsorata da al’amuran maza yanzu. Ni kuma me Habib yake ban sani ba? Ramlah tayi murmushi ta ce “Ciki gareki Hidaya bai kamata a fada miki maganar da zata tayar miki da hankali ba. Hidaya ta zabura ta ce in akwai ni fadamun Ramlah karki ci amanata babu wani abunda zai sameni don ina da ciki fadamin gaskiya. Tana rufe bakinta sai taga Haisam a kanta ya miko mata wani kati. Ramlah tayi sauri tasa hannu zata fusge sai Hidaya tayi sauri ta fusge tana karantawa taji kamar an daba mata wuka a kirjinta. Katin daurin auren Habib mijinta da za’ayi nan da sati gudane. Ko da wasa Habib bai taba fada mata ba saboda yasan tsananin kishinta shi kuma so yake ya kara aure don haka ya kwabi duk wanda yasan zaiyi aure da kada ya fadawa Hidaya cewa zaiyi aure.
Hidaya ta rike hannun Haisam gam ta rushe da kuka tana cewa “Wallahi saika karbo min takardata a wajen Yayanka na fasa auren. Haisam ya hau dariya yana cewa ni asuwa ke da kika isa da mijinki jeki ki same shi, kiyi hakuri kawai ki zauna ga tsohon ciki ga *ya*ya ina zaki kaisu Hidaya zama da kishiya ya sameki sai hakuri daina ma kuka. Ya juya ya dubi Hauwa da Aisha kowacce tamkar zararriya abunda ya dameta a ranta ya dameta. Babu sallama kowacce taja gyalenta ta nufi hanyar fita. Ramlah na cewa ku dawo ku bari a gama abinci kuci mana, inahh, babu wacce ta kalleta balle susan me take cewa. Direban Hidaya ne ya kawo su, mota kawai suka fada. Ramlah ta bisu tana rokarsu don Allah su kwantar da hankalinsu su bari zuciyarsu ta huce kafin su yanke hukunci karsu yanke hukunci cikin fushi subi komai a hankali. Basu iya ko magana ba saboda makakin bakin ciki kowacce sauri take burinta ta ganta a gida tayi arba da munafikin mujinta maci amana, suka ja mota suka tafi.
Haisam ya jawo hannunta suka shige gida su duka dariya ce ta hana su yin magana. Sunyi minti goma sha biyar suna dariya suyi su huta su sake tunowa su kwashe da dariya haka dai suka yi tayi. Haisam ya ce “Ai duk hirar da kuke ina jinku nayi shiru ban tanka musu ba saboda naji kina basu amsar da ta dace. Hakika Ramlah kin burgeni kin cika mai hankali da tunani da kaifin basira. Kin burgeni da yawa da baki dauki shawarrar su ba amsoshin da kika basu yayi daidai da tambayarsu. Nasan Yaya Habib zaiyi fada don me na fadawa Hidaya to ko me zaiyi yayi ni dai na riga na gama fada saboda ta cika min ciki tun rannan nake ciki da ita. Wai shin ina ruwansu da gidan wata? Banda gulma irin ta mata ina ke ina matsalar wani gida ita wacce aka yiwa kishiyar ta ce babu komai ku kun dage kunce akwai komai, suna bani mamaki wallahi. Ya jawo Ramlah ya rungumeta ya ce “Yanzu haka wani sonki ne na daban ya kara lullubeni. Ramlah ta lumshe ido ta ce “Na gode da yawa. Tana rufe bakinta Hannah ce ta turo kofa ta shigo gami da yin sallama tayi turus ta tsaya cak don ba zata iya karaso inda suke tsaye a rungume da juna ba. Tayi kamar ta bude kofa ta fita sai dai ta daure ta hadiye makakin kishin daya taso mata, nauyi da kunyarsu ta kamata. Haisam ya saki Ramlah daga rungumewar da yayi mata, ya dubi Hannah wacce kanta ke sunkuye a kasa ya ce “Meye kika tsaya acan ki karaso mana. Tayi murmushi kawai ta nufo inda suke ta dubi agogon dake daure a hannunta ta ce “Zanje inyi alwala magaruba tayi. Sai su duka suka nufi ban daki don yin alwala. Bayan sunyi jam’i sun idar sai suka zazzauna akan abin sallarsu kowacce ta bude Alkur’ani tana karantaawa. Har lokacin sallar isha’i. Bayan sun idar suka yi addu’oin su suka shafa. Kafin su idar masu aiki sun gama jera musu abinci kala-kaala akan teburin cin abinci.
Kai tsaye suka nufi dinning table, Ramlah ta fara zuzzubawa a kowanne plate. Ta zuzzuba lemo (juice) a kowanne kofi ta koma ta zauna kowa ya fara cin nasa. Suka dauki lokaci mai tsawo babu wanda yayi magana. Haisam ya dubi Ramlah ya juya ya dubi Hannah ya ce “Yau abincin yayi dadi sosai ko magana kun kasa yi. Su duka suka yi dariya. Hannah tayi masa wani lallausan kallo ta ce “Ka cika neman magana kaine fa kace mudaina magana idan muna cin abinci yanzu kuma ka ce mun kasa magana. Ramlah ta ce “Ai dokar da yasa shi tafi effection saboda yallabai baka iya zaman minti goma baka yi tsokana ba. Haisam ya ce “Kullum dai bakinku daya ne abunda Yaya ta ce haka kanwa take cewa haka abunda kanwar ta ce Yaya sai ta ce haka ne, kanwata babu mai bin bayana a cikinku ko? To shikenan tunda hademun kai kuke nima zan samo me shigarmun inyi kanwa. Hannah ta harari Haisam ta ce “Wacce irin kanwa kuma? Haisam ya ce “Kishiya mana kunga sai ayi bibbiyu kenan ku biyu nima ni da ita sai ta shigar mun, “Ramlah ta tuntsire da dariya ta ce “Kanwata ke yake tsokana ai na gaya miki shi dai yayi tsokana yaji dadi. Haisam yasa hannu yana shafar kumatun Hannah ya ce “Ke da wasa nake miki, ai na gama aure a rayuwata Insha Allah. Kuma ina jin dadin wannan hadin kan da kuke mun. Tsokana nake yi ina ni ina wani kara aure har a lahira na gama karin aure. Ramlah Uwar gidana Hannah amaryata har abada. Su duka suka yi dariya ya ce “Allah da gaske nake, ko kunga nayi muku kama da wanda zai kara aure ku kalleni tsaf a nutse ku kare mun kallo. Suka tuntsire da dariya dukkaninsu har Haisam din.  “Hannah dai dariya kawai take yi bata ce komai ba kai kayi kidanka kayi rawarka. Haisam ya ce “Ni yanzu abin da yake gabana shine inga dukkanninku na baku jari kowacce ta kama sana’a ta kanta, Ramlah yanzu misali idan aka baki jari me kike da sha’awar budewa. Ramlah ta ajiye kofin dake hannunta tayi fari da ido ta ce “Ni a gaskiya ina da burin bude kantin sayar da kayan Senegal na mata da maza sannan inyi wani kanti wanda zan dinga sayar da takalma na kasar waje tsadaddu na mata da maza da yara. Haisam ya ce “To ya isa haka Aunty Ramlah so kike ki bude kantina daban-daban. Idan na kyaleki saiki kirgo min guda goma biyu ma sun isa. Kefa amarya ta? Hannah ta narairaice ido ta ce “Ni burina da ace ina da kudi makarantar Islamiyya zan bude da masallaci da rijiyoyi da bishiyoyi zan shuka ince Allah Ya kai ladan Kabarin Iyayena da suka rigami gidan gaskiya. Haisam ya ce “Allah Sarki shike nan? Hannah ta zubo da hawayen daya cika mata ido ta ce “Shikenan burina. Haisam yasa hannu ya share mata hawaye ya ce “Kar kiyi kuka ajiye wannaan a gefe za’ayi insha Allah a sana’a me kike da burin yi? Hannah ta danyi murmushi ta ce “Ina so in bude katon kanti (Super market) a kusa da nan kuma in bude wani dan ofis na taimakawa marayun yara. Haisam ya ce “Duk kun zabi sana’oi masu kyau, nima bari in fada muku tawa sana’ar a Abuja na gina wani katafaren waje kerarre, kayatacce mai kyawun gaske nan da wata biyu za’a kawo min motoci daga Germany zan fara sayarwa idan mun dawo daga tafiya in Allah Ya kaimu zan kaiku ku gano wajen. Hannah da Ramlah suka yi murmushi dukkansu suka kuma tayashi murna da fatan alheri.
Haisam ya ce “Na gode sai dai kuma na kasa tuno sunan da zan sakawa wajen misali Hannah da zaki bude Supermarket wanne suna kike so kisawa wajen? Kema Ramlah yaya sunan boutik dinki da zaki bude ku dan bani satar amsa sai insan wanne suna zan sawa wajen sayar da motocina. Ramlah tayi dariya ta ce “Aini sunanka zansawa wajena. Haisam senegalise boutique, Haisam ya girgiza kai ya ce “Baiyiba, kefa? Hannah tayi dan murmushi ta ce “Sunanka dana Auntyna Ramlah zansa HaiRam Supermarket. Haisam ya ce “Hairam? Ke kuma laifin me kikayi da kika cire sunanki kara Hannah akan Hairam din sai yafi dadi. Hannah tayi dariya ta ce “HAIRAMHANAH Supermarket. Haisam da Ramlah suka hada baki suka maimaita HAIRAMHANAH sunan yayi dadi gaskiya. Haisam ya ce “To da nawa dana Aunty Ramlah dana Amaryata Hannah dukka sunan daya ne, kunga Hairamhannah super market, Hairamhannah senegalise boutique, Hairamhannah motors da dai sauransu. Yanzu kowaccenku zan bude mata account zan zuba muku miliyan hamsin-hamsin ku fara jarin dashi kafin nan gaba in kakkara muku, nima ina cikin zamana Babanmu ya kira mu ya ce tunda munyi hankali kowannen mu  ga takardun hannayen jarin da ya dinga zuba mana tun muna yara a bankunan kasashe daban-daban da bankunan nan kasa Nigeria, kudade masu yawa sun taru shekaru da yawa bamu taba karba ba ya ce muje mu kula da kanmu da Iyalinmu. Sannan an biyani kudin kwangilar da nayi ta miliyan dari biyu sai naga ya dace nima inzo in bawa kowacce jari ta juya da kanta don tayi hidimomin gabanta ba sai kun jirani ba kullum ina dan sammuku na dan kashewa ba. Ramlah ta rike baki ta ce “Yallabai miliyan hamsin-hamsin fa kace? Hannah ta ce “Fifty millions? Haisam ya ce “Miliyan hamsin kowaccenku. Hannah da Ramlah suka zo suka durkusa a gabansa suka yi ta godiya. Yasa hannu ya tashe su tsaye ya ce babu komai shi ba sai sun gode masa ba. Hannah ta nufi kofar fita ba tare data yiwa kowa sallama ba a tunaninsu kicin zata shiga sai suka ga ta bude kofar fita ta fice da alama kuma kuka take yi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Comment da yawa yana kara mana karfin gwiwan muku posting fa.
Amma sai ku dinga comment kamar bakwason labarin.
Ko so kike muci gaba da rabi anan  rabi  a can!!?

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]