Gangar jikinsa na aura25

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter 25

Www.littafanhausane.com.ng
Murya ta ji ana cewa Hello Hannah, Hannah, ko
ba Hannah ba ce? Haisam ne. Hannah kiyi
magana mana ko bakya ji ne? Hannah ta
kyalkyale da dariya ta ce “Yaya Haisam kaine?
Haisam yayi dariya ya ce “Bakauyiya ashe kina
jina kina tsoron kiyi magana. Hannah ta gaishe
shi ta ce “Kwana biyu shiru banji kayi waya ba
kullum da ita nake kwana a kusa da ni wai ko
zaka kira cikin dare. Haisam ya ce “Oh I’am very
sorry tun shekaran jiya ban zauna ba ina zurga-
zurga a airport jiya kuma a jirgi muka kwana.
Hannah ta ce “Har kunyi tafiyar. Ya ce “Yanzu ma
muna London ni da Ramlah. Hannah ta ce “Lah
Yaya ina Aunty Ramlah take mu gaisa. Haisam ya
ce “Ramlah ta fita kasuwa kinsan da daddare aka
fi yin hidindimu a turai da kasashen larabawa.
Hannah lefen mu fa Ramlah ta tafi suyowa lefen
auran Haisam da Hannah fa. Hannah tayi dariya
ta rungume filo. Haisam ya kashe murya ya ce
“Banji kince komai ba Hannah ko daman auren
dole za’ayi miki bakya sona? Tayi fari ta yamutse
fuska ta ce “Cewa zaka yi ko na daina sonka ne
bawai ko bana sonka ba, tunda kasan ina… Sai
tayi shiru. Ya ce “Yaya kika yi shiru, da kina me?
Hannah ta ce “To ai shikenan a bar maganar.
Haisam ya ce “Ai sai kin karasa, so nake daman ki
fadi wannan kalmar shi ya sa na tsokano zancen
kina me? Hannah ta ce “To yanzu dai so kake inyi
rashin kunya Yaya da kunya ince ina… Ta sake
yin shiru bata karasa ba. Haisam yayi murmushi
ya ce “Hannah kenan aure fa zamu yi yaya za’ayi
aure da kunya ai da kin dan fara rarrageta kafin
in fizgeta gaba daya in yasar. To ni bari in fada
miki abin da nake so ki fadamin kika kasa.
Hannah ina sonki. Taji wani abu ya disa a ranta,
dadi ya lullubeta tayi ruf da ciki akan katifarta ta
dora kanta akan filo tana sauraron daddadar
muryarsa. Tayi shiru bata amsa ba ya ce
“Hannah, ko bakya jina? Cikin shagwaba da kashe
murya ta ce “Yaya ina jinka shirun da nayi wani
abune ya disu a zuciyata yake zagayawa ta
kwakwalwata nake kokarin warware abun da yake
kokarin ya cushe min. Ya lumshe ido ya ce
“Kamar yaya fa? Ta nisa ta ce “Ina cikin wata
matsananciyar soyayya wacce ta zame min ciwo a
raina na fara zama mutum mutumi, gangar jikina
na wani wajen zuciyata kuma tana wani waje. A
kullum kuma a koda yaushe ina sake-saken
wasikar jaki idan ina ido biyu, a bacci kuma ina
mafarkan da nake daukarsu tamkar tatsuniya. Sai
gashi a yau tatsuniyata ta fara zama gaskiya.
Shine nake tunanin shin a mafarki nake jinka ko
kuma a ido biyu? Haisam yayi murmushi ya
ringisa akan kujerar shakatawa da yake a bakin
swimming pool din wani katafaren Hotel da suka
sauka a london yake. Ya ce “Hannah this is real,
not a dream so our dream come true. I love you,
of cours I do. You mean much to me Hannah. I
missed you so much. Kafin Haisam ya rufe
bakinsa sai yaji muryar Hannah kamar daga sama
cikin sanyayyiyar murya ta ce “Yaya Haisam na
soka, ina sonka fiye da tunaninka fiye da duk
wani mutum a duniya. I love you so much. Ya
gyara zama ya ce “Hannah har fiye da tsohon
mijinki daya rasu, haba Hannah ko dai don kinga
ya rasu ne? Su duka suka kyalkyale da dariya
Hannah tama rasa irin amsar da zata bashi. Haka
Hannah da Haisam suka kasance suna hira mai
dadi har karfe biyun dare sannan suka yi sallama
suka ajiye waya. Kowannensu juyi kawai yake yi a
kwance don murna bata barsu sun iya yin bacci
ba. Kullum haka Haisam yake sai ya tabbatar
Hannah ita kadaice shima shi kadai sai ya buga
mata waya su kashewa junansu zuciya.
Bayan tafiyar Haisam da sati uku *yan uwan
Haisam maza suka zo neman auren Hannah suka
bada kudin komai da komai sadaki ne da lefe
kawai suka rage ba’a bayar ba. Murna wajen
Hannah da Haisam abin baya misaltuwa. Watan
su Haisam daya da sati biyu da tafiyarsu sannan
suka dawo. Cikin ikon Allah sai ga Ramlah tayo
tsarabar ciki, kowa murna yake musamman
Iyayen Haisam suna jin dadin yadda rayuwar
Haisam ta fara gudana kamar ta kowa. Duk inda
ka ganshi fara’a yake wasa da dariya da mutane
kamar yadda yake a da. Ga wata uwar kiba da
yake yi da fari baza kace wannan kashi da ran
bane. Ramlah ma kamar tafi Haisam samun canji
a rayuwrta saboda itama mafarkinta ya zama
gaskiya. Tana samun kulawar Haisam suna zama
suyin hira, suci abinci tare su kwanta gado daya, in
tayi kwalliya ya daga ido ya kalleta ya ce tayi
kyau. Wannan ba karamin canji Ramlah ta samu
ba. Mai hakuri yakan dafa dutse yasha romonsa
inji Bahaushe.
Bayan su Haisam sun dawo da kwana uku dangin
Haisam mata suka cika hadaddun motocinsu na
alfarma suka nufi Dashi garin su Hannah da lefe
da sadaki. Daman Hannah ta sanarwa da Kawunta
 ranar da zasu zo dan haka suma suka kuke
suka harhada suka sissiyo kayan dadi suka
hadawa baki abinci da abin sha irin nasu na *yan
hutu. Harda Mahaifiyar Ramlah akazo danginta
wasu kawai dan suga Hannah suka zo. Cikin
rashin sa’a basu sami ganin Hannah ba don tun
bakwai na safe Hannah ta gudu ta tafi can garin
Magarya gidan wata tsohuwar Kakarta ta buya
don kunyar surukan take ji.
Dangin Hannah sai suka zama baki bude son
tsananin mamaki ganin yawan lefen Hannah
tunda suke basu taba ganin irin akwatinan nan ba
balle kayan dake ciki. Wasu runduma-runduman
akwatina ne masu santsi har guda shida bi da bi
ta karshensu *yar kit ce a dankare take da gwala-
gwalai da fassion mai tsada irin na turawa.
Leshina da shaddoji da kayan tsukewa abun
bazai misaltu ba takalma da jakunkuna hadaddu
mayuka kuwa da turarruka ba sai na zaiyana ba
daman can ya siyo mata balle yanzu, akwatinsu
suma daban. Iya Haule surukarta na wajen
karben lefen Hannah sai ta zama abun kallo wasu
kuma ta zamar musu abun dariya gaba daya saita
rikice ta hau surutai. Ita abun ya zamar mata
kamar wani rufa ido yanzu duk wannan kayan na
Hannah ne, yanzu Hannah ta dage ta tafi ta barta
tayi kudi kenan baza ta iya ganinta ba balle ta
sata aiki. Allah kenan haka Yake ikonSa. Ansa
ranar daurin aure sati biyu kacal suka ce kuma a
ranar suke so a zo a tafi da amarya ba sai an bata
lokaci ba. Daman sun taho da kudin sadakinsu da
kudin dinki duk suka bayar, makudan kudi suka
jifgewa dangin Hannah a gabansu. Wasu suka dau
kukan murna wasu suka rafsa buda suna kirari.
Dangin Haisam sunji dadin yadda aka tarbe su a
garin su Hannah. Kamar za’a hadiyesu anata yi
musu marhaban da wasa da dariya suka rabu
akan nan da sati biyu zasu dawo su tafi da
amaryarsu.
RANAR DAURIN AURE.
Ranar Juma’a ne ranar daurin auren Haisam da
Hannah da misalin karfe ukun ranar za’a daura
auren bayan sallar juma’a. Garin Dashi ya cika
makil da jama’a, taron da ba’a taba yin irinsa ba
a garin. Manya-manyan masu kudin Kano sun
halarci daurin auren Haisam, abokan Babansa da
*yan Uwansu abun sai wanda ya gani harda
gwamnan Kano na wannan lokacin ya halarci
wannan daurin auren. Dangin Hannah na nesa
dana kusa sun hallara, *yan garin kuwa da
wadanda aka gaiyata da *yan gaiyar sodi duk
sunzo su ganewa idanuwansu kar suji ana fada su
basu gani ba. Babu abinda zaka dinga hangowa a
garin sai wasu jifga-jifgan motoci bakake masu
bakin gilashi sai kuma fararen shaddoji da
tsadaddun yadika a jikin manyan masu kudin da
suka halarci daurin auren. Kamshin turare har
cikin gidajen *yan garin *yan jaridu tududu na
nan Nigeria dana Niger suna ta dauka a hoto da
bidiyo kaset. Ga Mahaifin Haisam dana Ramlah a
kewaye da jama’a. Haisam kuwa ko hangoshi ma
baza ka iya yiba saboda jama’a kowa so yake ya
gaisa dashi kowa yana so Haisam ya ganshi yasan
yazo don duk dangartakarka da Haisam ya ce
zaku bata in har baka zo masa wannan daurin
aure ba. Kafin karfe hudu har an shafa fatiha an
daura auren Haisam ya zama mijin Hannah.
Allah Ya bada zaman lafiya, *yan daurin aure
maza sun fara shiga motocinsu masu babura da
kekuna suma sun fara hawa suna kama gabansu,
anci, ansha lemunan gwangwani da ruwan kwalba
kudi aka dinga rabawa a wajen daurin auren.
Haka ango ya dinga danko kudi yana rabawa
mutane don murnar da yake ciki a ranar saida
Babansa ya ce ya isa haka sannan ya daina.
Maroka duk sun cika aljihunsu da kudi da goro da
alewa ga ruwan sanyi sun jika makoshinsu. Kowa
yana sanya albarka da fatan zaman lafiya ango da
amarya.
Bayan maza sun watse motocin da zasu dauki
marya da kawayenta da *yan uwanta don rakata
gidan mijinta suka karaso kofar gidansu Hannah
cikin gidan makil yake da mata ko Hannah baka
hangowa mai bidiyo kaset dakyar ya nemo
amarya ya haskata. Hannah ta caba ado da wani
rantsattsen leshi baki mai adon rawayar fulawa
tasa goggoro rawaya takalmi da jakarta baki.
Fararen hannayenta da kafafuwanta sunsha
fulawar lalle. Kirjinta da kunnuwanta da
hannayenta dambara-dambaran gwalagwalaine.
Babu abin da zaka ji idan ka matso Hannah sai
kamshin turaren wuta (Dukan) don tsuma da tun
ana saura wata guda auren, Kakarta ta dinga
tsumata ciki da waje abunka da Azbinawa sunsan
sirrin shirya amarya tayi tsaf ciki da bai. An dilke
fatar Hannah an gurjeta da kayan gayaran jiki
tayi sumul-sumul ta kara jawur. Abunka da
farare jawur jawur zaka dinga hangowa a cikin
gidan, gashi yalo-yalo har baya dangin Hannah
dai-daine bakake duk jajaye ne.
Motar da za’a dauki amarya tafi kowacce girma
da kyau. Hannah ta shiga ita da Hajir matar
Kawunta da sauran sa’anninta *yan Uwanta dan
ita bata da kawaye *yan Uwanta ne kawayenta.
Tsofaffi suka dinga duruwa sauran motocin kana
shiga sai kaji wani sanyi ya daki hancinka. A.C ce
ta gauraye motocin. Hatta manya-manyan bus
din da aka turo masu A.C ne da labulaye a
wundunan. Duk yawan motocin da Haisam ya
turo sai da wasu suka rasa saboda yawan jama’ar
Da suke so suje Kano suga gidan Amarya. Motoci
suka fara tafiya sai Hannah ta kece da kuka tana
dagowa mutane maza da mata hannu. Har aka
iso Kano Hannah kuka take su Hajir suna
lallashinta tayi shiru. Can ta tuna da Mahaifinta
dama ace yana nan da rai mana wannan daula da
tazo mata data taimaka masa, haka yayi
rayuwarsa har ya mutu a cikin talauci sai kuka ya
kece mata. Sai da magariba suka isa gidan
Amarya a wata Unguwar jigajigan masu kudin
Kano gidan Hannah yake mai suna Nassarawa
G.R.A Rigiji gafji Haisam ya tantsama gida duk
layin babu mai girman na Haisam da kyau. Aka
wangame jifgegen get din gidan motocin duk
suka shigo farfajiyar gidan, amma duk da haka ga
fili nan fetal wasu motocin ma fiye da biyar zasu
iya shigowa ciki saboda filin farfajiyar gidan
babba ne. Fulawoyi ne a shuke a jikin katangar
gidan ga tsuntsaye nan da dawisu da talo-talo a
zube a farfajiyar gidan suna ta shawagi. Sanyi
kalau ciki saboda wasu zagayayyun duwatsu aka
gina masu bulbulo da ruwa yana tashi sama.
Kasan da ake takawa abun a kalla ne balle cikin
gidan. Gidan bangare biyu ne iri daya ga wani
dankareren gida a tsakiyarsu. Sai aka nuna musu
gidan Hannah na gefen dama suka duru a ciki
wai! Wai!! Wai!!! Ai suna shiga ciki suka ga ashe
basu ga komai a waje ba. Sanyi da kamshi ne zai
fara dukan fuskarka sai walkiyar tiles da fitulu su
fara walle maka ido sannan ka fara cin karo da
kayatattun kujeru a wani katafaren falo ga wajen
cin abinci mai dauke da kujeru da tebur a
tsakiyarsu, gefe guda kuma wani falo zaka taka
wata matattakala tayi kasa shima a gefe. Ga
makeken kicin nan mai dauke da manya-manyan
furij da furiza ga cooker gas da kayan kicin gaba
daya koren launi ne aka hada. Hatta cokulan dake
kicin din koraye ne har lokokin kicin din.
Dakuna uku ne a gidan daya a kasa kowanne da
bandakinsa a ciki da gada dan kamfani da mudubi
da waduruf. Biyu kuma a sama makada-makadan
hadaddun gidaje ne yafi na kasa, suma da
bandakunansu a ciki da wani katafaren falo a
saman. Duk kusurwar gidan an ajijiye fulawoyi
irin na robar nan masu kama dana gaske. Ga
kayan kallo da na jin kida a faluka, kowanne daki
kuma akwai talabijin ana hada ta da tauraron dan
Adam (settelite). Tunda Hannah ta shiga gidan
kukan dadi take a zuciyarta kuma tana hamdala
tana yiwa Allah kirari tana gode maSa. Allah
Akbar. Karfe takwas dai-dai bayan duk sunyi
salloli sai Haisam yayiwa Hannah waya ya ce ta
shirya ita da kawayenta kawai banda tsofaffi da
yara zai turo motoci azo a dauke su matar
gwamna ta shirya musu liyafa a Tahir quest palace
har mutane sun fara zuwa tayi sauri. Hannah ta
shaidawa kawayenta nan fa duk suka fara shiri,
ita kuwa ta fada wanka ta fito ta tarar Haisam ya
aiko mota da wasu kaya da takalmi da jakarsu da
ribon duk kalarsu daya ya ce inji matar gwamna
ta ce ta saka. Kayan kansu abin kallo ne wata
shadda-shadda, leshi-leshi mai surfani riga da
zani anyiwa zanin kwalliya dankwalin kayan kuma
an nadoshi kamar goggoro irin kayan nan ne da
ake dinkowa daga Senegal to wannan na
musamman ne sai irin matan gwamnonin ne
suke siyansu. Hannah ta saka kayan nan ta tufke
gashinta da ribon kalar kayan ta dora goggoron
kayan bayan hoda da jagira da janbaki da tasha
tazo ta saka tsadaddun sarka da dankunne irin
kalar kayan, ga takalmi da jaka ta dana. Sai kowa
ya bude baki yana kallon kyawu daga Allah.
Hannah ta zama kamar wata tauraruwa mai
haske a cikin taurarin masu disasshe haske. Sai
walkiya take, Hajir ta fesheta da turarurruka
designer sai kawayenta suka take mata baya suka
fito suka shiga motocin suka nufi Tahir quest
palace dake Lamido cresent.
A bakin get din hotel suka iske Haisam da tulin
abokansa suna zazzaune akan motocinsu suna
jiran isowar su Hannah. Hannah na isowa suka
bude baki suna kallon ikon Allah. Ko a mafarki
basu dauka zasu ga amaryar Haisam kyakkyawa
kamar balarabiya ba. Musamman da suka je
daurin auren suka ga wannan kauyen sai duk
suka raina bikin suke cewa banda soyayya ma me
Haisam zaiyi da matan kauyen nan, a bayan
idonsa amma fa. Ashe wannan *yar kauyen ta
ninka matansu na birni haduwa. Suna ganin
Hannah kamar idan akayi mata Hausa baza ta iya
mayarwa ba tsabar babu wata surarta guda daya
data yi kama da Bahaushiya. Ta karaso ita da
kawayenta wajen da  suke, tayi *yar
siririyar dariya ta duka kadan ta gaishe su duk
suka amsa. Haisam kam ko amsawama ya kasa yi
sai murmushi yake ya kura mata ido. Ya mika
mata hannu wai su gaisa sai Hannah tasa hannu
ta rufe ido. Abokansa suka hau cewa ai yanzu
Hannah amarya komai yazo karshe babu kunya
Haisam ya zama mijinki. Haisam ya diro daga
kan mota ya rike hannun Hannah abokansa da
kawayenta suka take musu baya suka dunguma
zuwa wani katafaren dakin taro (conference hall)
inda ake gudanar da liyafar, ashe jama’a jingim
sun taru isowar ango da amarya kawai ake jira.
Hall din haske ne tar kamar safiya ga wani sanyin
na’urar sanyaya daki wasu dogayen tebura ne
tafka-tafka a jejjere a cikin dakin taron jama’a
maza da mata a zazzaune. Kwalayen lemune da
kofunan tangaran da robar ruwa a gabansu, gefe
guda kuma masu kida ne da gangunansu a gefe
*yan police band suna dan kadawa a hankali kafin
a fara gudanar da biki. Hannah na shiga taga
idanuwa cununu akanta gaba daya an tsaya ana
kallonsu. Tebur guda Ramlah ce da kawayenta
hadaddun *yan boko duk sun zubo mata ido.
Hannah ta dago ta kalli Ramlah sai taga Ramlah
tayi mata murmushi itama ta mayar mata. Koda
kuwa ta hada ido da sauran kawayen Ramlah sai
taga harararta suke da kallon banza. Hannah ta
sunkuyar da kai kasa suka wuce hannunta gam a
hannun Haisam suka nufi kan wani kayataccen
dogon teburi akan wata matattakala (high table)
da kayatattun kujeru guda biyu irin na ango da
amarya. Anan suka zauna sannan kowa ya dau
tafi. Abokan ango da kawayen amarya suma suka
sami kujera suka zazzauna. Babban abokin
Haisam wani mai surutu mai suna Jibril (jibson)
shine yake jawabi a lasfika. Bayan ya bude taro
da addu’a ya ce ga matar mai girma gwamna nan
da tawagarta suna shigowa wacce ta hada wannan
taron itama tazo taya ango da amarya murna
kowa ya zauna yayi tsit ana kallon kofar shigowa
wadanda basu taba ganinta a fili ba suna so suga
yaya take a fili wadanda daman sun taba ganinta
suna so suga wanne irin kayane a jikinta
musamman mata masu tsegumi irinsuuuuu ana jira aga
wanne irin leshi yau zata saka, wacce irin jaka
kuma zata rike. Dan daman an san Uwargidan
mai girma gwamna akwai iya tsala kwalliya kuma
irin ta hadaddun *yan boko, ga gayu da kyau.
Hmmm

About AIS

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *