Gangar jikinsa na aura24

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter24

Karku  manta shiga www.littafanhausane.com.ng
Don karanta complete chapter din

Ta fito tsakar gida wajen girki ta taya Hajir aikin abincin dare don taga hayaki na tashi tasan an
hura wutar itacen abincin dare. Tana fitowa Hajir ta zabura ta mike tana cewa “La! La!! La!!! Hannah me zan gani wacce irin kwalliya kika caba yau kamar mai shirin barin kasar? Kai amma gaskiya wannan atamfa mai kyau ce ni ban taba ganin irinta ba. Tasa hannu tana
taba kayan jikin Hannah. Ta ce “Kai ai laushi garesu wannan ba atamfa ba ce. Hannah tayi dariya ta ce
“Ba atamfa bace material sunansa kinsan a wajen *yan birni kaga abubuwa iri-iri a gunsu. Hajir ta ce
“Lallai kuwa wannan matar ta caba ki da kayan alatu iri-iri.
Hannah ta nufi wajen garin tuwo ta dauki rariya zata yi tankade Hajir ta rike rariyar ta ce “Hannah ba za ki bata jikinki da gari ba ga kayanki bakake barni kawai in
karasa tuwona tunda har na gama miya na dora ruwan tuwo talge kawai zanyi in tuka na gama. Ga kujera can a gefe jeki ki zauna ni ina zaune ai yanzu sai ki huta ni
inyi. Hannah ta ce “Ni ai zaman haka kawai bana so saboda tun ina *yar karama na saba da aiki barni
kawai ba komai inyi miki tankaden. Hajir ta ki fur suna ta jayayya daga karshe Hannah ta hakura ta koma
gefe ta zauna tana kallon Hajir tana aiki. Hajir ta dago ta kalli Hannah ta ce “Kwanan nan sai
inga kamar kina yawan damuwa da tunanai ko dai wani abu yana damunkine Hannah? Hannah tayi murmushi ta ce “Babu abin da yake damuna. Hajir ta ce “A’a Hannah
fadi gaskiya ko sai na miki baro-baro ne? Ai dole kiyi tunanin Haisam musamman kin baro shi bashi da lafiya. Su duka suka kyalkyale da dariya. Hannah ta ce
“Don Allah ya akayi kika gane ni? Da gaske abun ya fara damuna ni dai fatana ace lafiyar sa kalau ba jikin bane ya dawo. Hajir ta ce “Insha Allahu lafiyarsa kalau
ita lafiya ita ke buya. Amma lalle Haisam ya samu shiga fiye da kowa har yafi marigayi samun waje.
Hannah tayi dariya ta ce “Ni dai baza ki ji a bakina ba.
Hajir ta ce “Jiya kuwa Ahmad yake ce min a kalla masu sonki a garin nan sun doshi mutane biyar da suka
same shi suka yi masa zancen don Allah ya basu izini su zo su nemi aurenki wai in sun zo wajenki bakya fitowa. Hannah ta bude baki don mamaki ta ce “Don Allah da gaske kike yi? Hajir ta ce “Wallah da
gaske nake. Hannah ta gyara zama, ta dafe kirjinta ta ce “Me Kawun ya ce musu? Hajir ta ce “Cewa yayi har a dangi an fara damunsa ya kamata kiyi aure ga masu sonki ki
zabi daya ya ce min shi gaskiya baya so ki sake aure a kauyen nan yafi son ki auri Haisam, to amma gashi yau kusan wata biyu bai zo ba bai aiko ba. In har ya bashi wasu lokuta bai aiko ba zai shawarce ki, ki zabi wani tunda har akwai samarin da basu taba aure ba a wadanda suka same shi da zancen suna sonki.
Hannah tayi ajiyar zuciya tayi shiru ta rasa ta cewa sai tsananin bugun da zuciyarta take yi. Ta ce a ranta “In har Haisam ya kara wata bai zo ba to nasan akwai matsala.
Ko ya hakura da sona ne?
Kai Haisam ba zai hakura da
sona ba. Yaya zanyi yanzu in har Kawu ya zo ya sani a gaba ya ce in fitar da wani in aura? Sallamar Kawu Ahmad ce ta katsewa Hannah
tunanin da take yi. Ya shigo da saurinsa ya suri tabarma sannan ya juyo ya kalli Hannah ya ce “Ki dauko gyalenki ki kawowa baki ruwa a sabon kwanon sha da
kofina masu kyau.
Hannah ta amsa da “To Kawu. Ta juya suka hada ido da Hajir. Hajir ta ce “To ko Haisam ne dan halak yaki
ambato ya iso garin gabannin magariban nan? Hannah ta ce “Banji a jiki na ba, Haisam ba zai zo yanzu ba. Ni har gabana ya na faduwa Allah Yasa dai ba masu
neman auren nawa bane aka sami wani dan…… ya canjawa kawu ra’ayi. Hajir ta ce “Kai haba dai tashi ki kai ruwan kiga ko waye. Dakyar Hannah ta mikewa saboda sanyin da jikinta yayi ta shiga daki ta yafo dan yalolon gyalenta ja ta dauko kwanon sha da kofuna biyu ta zo ta wanke su tas ta cika da ruwan randa mai sanyi ta nufi zaure. Kanta a sunkuye a kasa tayi
sallama ta ajiye kwanon sha a gaban bakin sannan ta gaishe su ba tare da ta dago kai ta dubi fuskokinsu ba.
Wata murya ce ta amsa mata gaisuwar kamar a mafarki muryar da take muradinta. Ta dago kai da
sauri ta dubi mutumin sai taga Haisam dinta ne a gefensa Kawu Ahmad. Sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai ta ce “Sannu da zuwa Yaya.
Ta yunkura zata tashi ta shiga cikin gida sai Kawu Ahmad ya ce “Hannah ki kawo ruwa a butoci guda biyu don magariba ta kusa yi. Hannah ta amsa da “To Kawu. Ta shiga gida. Ai kuwa da murna ta karasa wajen Hajir.
Hajir na ganin yadda Hannah ke murna sai ta ce “Hannah ko dai addu’ar tawa ce ta ci, Haisam ne ya zo?
Hannah taje ta rike mata hannu ta ce “Hajir wallahi shi dinne kuwa, ko mafarki nake yi ne? Hajir ta ce
“Gaske ne Hannah Allah Sarki ya cika alkawari ya zo, daman Kawun ki yafi sonki dashi. Daman ina jin jikin ne ya hanashi zuwa Hannah ta ce “Kai gaskiya babu alamar jinya a tare dashi yayi fari ya murmure daga ramar da yayi, kinga kibar da yayi kuwa? Ba za ki ce ya taba yin
wani ciwo har an fasa masa kukan mutuwa ba.
Hajir ta ce “Don Allah? Hannah ta ce “Ai yau duk kunyarki saikin leka kin gaisa da mijina. Su duka suka tuntsire da dariya. Hajir ta ce “Hannah ko *yar kunyar nan
babu wannan karan lallai anayi da Haisam, ai kuwa zanzo mu gaisa. Hannah ta wuce ta debo butoci ta wanke su tas ta ciko su da ruwa ta nufo zauren da suke zaune.
Daf da ta shiga zauren taji Haisam na cewa “Zan yi tafiya zan dauki kimanin watanni biyu a turai amma
ina neman izini zan turo magabatana su zo neman auren Hannah. Ina fatan dai Hannah ta gabatar dani a wajenku daman ko? Kawu Ahmad ya gyada kai ya ce “Kwarai kuwa tun sanda naje Nigeria zan daukota tun daga can ta fara bani labarinka. Kai ka dauki dawainiyar karatunta harta gama sakandire.
Sannan data dawo daga Kano tafiyar nan ta kwanan nan ta fadamin kakaf yadda akayi. Allah Ya saka da alheri.
Haka Allah Ya kaddaro muku Shine Yake yin yadda Yaso da bawanSa. Babu komai ka aiko magabatabka ai ba sai anyi wani dogon bincike ba ai kunsan juna tuntuni. Hannah tayi sallama ta shigo zaure ta ajiye butocin a gefe kanta a sunkuye a kasa ta koma cikin gida. Bayan sunyi alwala, Masallacin dake kofar gidan suka shiga suka yi Sallah tare da jama’a. Hannah ma anan cikin gida tayi Sallah bayan ta idar ta sake rangada kwalliya a fuskarta ta gyara daurin dankwali, ta sami waje ta zauna tana jira akirata taje ta gana da abin kaunarta. Amma abu daya ya tsaya mata a rai
take ta nanantawa da Haisam ya ce zai tafi turai sai bayan wata biyu zai dawo. Ita kuwa anya zata iya daurewa har sai ta sake yin wata biyu kafin ta sake ganinsa?
Son Haisam ya sake yaduwa a zuciyarta fiye dana da a kullum yana like a zuciyarta ko sakon daya bata iya yi ba tare da tayi tunaninsa ba. Kawu Ahmad ne ya shigo ya ce “Hannah za ki iya zuwa ku gaisa shi kadai ne a zaure ki kunna fitilar kawai don zauren da duhu.
Ya ce a yau zasu koma Kano ba zai kwanan ba ni kuma zanje wajen Baba Shu’aibu in fara sanar masa da zancen aurenku. Hannah ta amsa da “To Kawu.
Kawu Ahmed ya fita. Ta mike ta shiga daki ta dauko fitila ta nufi zaure tana takawa dai-dai tana rangwada. Tayi sallama ta ajiye fitila a gefe.
Haisam ya dago kai da sauri yana kallonta harta shige lungu can gefe ta takure ta tsuguna sannan cikin
ladabi ta gaishe shi. Yayi murmushi ya amsa mata. Ya ce “Hannah kamar zan gudu da ke kika tafi can
nesa kika takure, ga nan gefen tabarma kusa dani ki zo ki zauna mana. Koda yake Hannah kin manta da Uncle Haisam tun wata shekara ko. Hannah tayi dariya
ta kubce mata, Haisam ma yayi dariya. Hannah ta taso tazo gefensa ta zauna. Ta daga ta dube shi suka hada ido yayin da wata kibiyar so ta caccaku a zuciyoyinsu, Hannah ta lankwashe murya ta ce “Yaya jikinka?
Ya kura mata ido can ya ce “Ai tun ranar da na hada ido dake na nemi ciwon narasa, kuma tun ranar da
nace miki good bye na tafi na fara ciwo. Hannah tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa ta ce “Ina fatan har abada zan dauwama a wannan matsayin daka bani.
Mamaki ya kama Haisam ya ce a ransa “Hannah ce take fada min haka ko mafarki nake, a zato na sai
nasha bakar wuya da Hannah kafin ta fara sona sai kuma nayi da gaske kafin ta waye da irin wannan
soyayyar ta *yan birni. Ashe ni Hannah a waye take harta wuce tunanina. Ga iya kwalliya cas kamar
*yar birni, ga wani kallo da take yimin ko wata *yar birni me digiri bata iya ba. Hannah ta katse masa tunaninsa ta ce “Naga an doshi wata biyu ban ganka ba sai na shiga fargabar kode ciwon ne ya dawo maka. Haisam ya ce “Ciwo ya tafi kenan Insha Allahu tunda Allah Ya kawo min maganinsa. Hajiya ce dai ta hanani zuwa wai a rame nake tafi so in zo miki da kibata. Zaki fi murnar ganina wai. Hannah tayi dariya. Haka suka shafe fiye
da awa guda suna hirar so da kauna kowa na fadar kalmar da zata dadawa dan Uwansa. Yau jinsu suke kamar a aljannah suke dan zamannan da suka yi.
Daga karshe Haisam ya shaida mata cewar zasu tafi New York jibi shi da Ramlah zasu hado kayan lefenta kuma Ramlah ta ce ace mata itama Honey moon dinta ne wannan fitar don tunda suka yi aure ko Abuja basu taba zuwa tare ba kafin amarya ta zo itama taje
nata.
Hannah ta yi murmushi ta ce “To Allah Ya kiyaye hanya Ya dawo da ku lafiya. Haisam ya ce “Abunda za ki ce kenan? Hannah ta ce “Me zance wanda yafi wannan? Haisam ya ce “Kice asha hony moon a hado min lefe mai kyau. Kuma in cewa Ramlah in Allah Ya yarda kema za ki zo ki fita da angonki Hony moon lafiya.
Hannah tayi dariya ta rufe ido ta ce “A’a Yaya Haisam ka rufamin asiri karka fada mata haka ni na isa in fadawa Auntyna haka? Haisam ya ce “To meye Ramlah kanwa da kawa ta dauke ki, bata da wata hira da ta wuce tayi min hirarki shi yasa nake jin dadin hira da ita yanzu. Hannah tayi shiru tana tuno yadda Bello Madu yake yi mata. Hakika Ramlah tayi dabara a sannu zata samu soyayya a wajen mijinta kamar yadda Bello Madu ya fara samun shiga a wajena saboda kawai yana yi min hirar Haisam.
Haisam ya miko mata wata katuwar ambulan tasa
hannu biyu ta karba ya ce “Inji Ramlah ki rabawa *yan kungiyarku tunda kece shugabar kungiyar ashe.
Hannah tayi dariya ta ce “Ashe ka sani wa ya gaya maka? Ya ce “Ramlah ta bani labarin yadda kuka yi kakaf. Ya miko mata wata katuwar leda ya ce wannan nakine inji Ramlah. Ya miko mata wata kwalin waya mai tsada ya ce “Wannan wayar tafi da gidan kace zaki ga direction dinta a jiki da cherger in an kawo wuta ki dinga sawa a caji. Hannah tayi kasake tana kallonsa tana tunanin ya za’ayi ya bata waya a kauyen nan bayan babu service a garin. Haisam ya gane abun ya daurewa Hannah kai sai ya ce “Wannan wayar THURAYA ce tana yi a wajen da babu service dan haka duk sanda na bugo miki in dai da caji kuma a kunne take zan sameki ina fatan duk kinsan yadda za ki yi.
Hannah ta ce “Na sani Yaya, ai satin da nayi a Kano Amratu ta nunnunamin a tata. Kudi ne a shake a wata *yar jaka ya mika mata ya ce “Dallar America ce wannan saboda ban da kudin Niger amma Dalla za’a iya canjata a ko ina, ki dinga kashewa. Ki bawa Kawunki duk yadda kika ga dama a cikin kudin.
Kada ku sake ku sayi ko cokalin cin abinci na aure. Sabon gida nake gina muku mai bangare biyu naki dana Ramlah yadda  kowa da bangarensa a sati ma wani ba zaiga wani ba. Idan kuwa kika bari suka suyo miki wani abu asararsa za’ayi. Turawa ne suke gina gidan, haka su zasu zuba kayan ciki irin kalar data dace. Bana son abinda za’ayi asararsa kinji.
Farin ciki mai hade da mamaki ya rufe zuciyar Hannah ta tsaya kawai tana kallon Haisam. Can tayi ajiyar zuciya ta ce “Yaya naga gidan naku ma mai tsananin kyau ne kuma sabo gashi da girma me yasa zaka sake gina wani? Yayi murmushi ya ce “Haka Ramlah ta ce ita ma in hada ku kada in warewa kowacce bangarenta ni dai a tsarina da ra’ayina naga gara in bawa kowacce bangarenta. Kuma
kinsan ko harshe da hakori ma ana sabawa ni kuma gani bani da hakuri idan naga za’a taba min *yar
kanwata Hannah, ina tsoratarwa da cewa zan iya kashe duk mai shirin jefata a cikin tashin hankali a rayuwarta.
Suka kyalkyale da dariya gaba dayansu.
Haisam ya mike tsaye yana shirin tafiya, Hannah ta durkusa gwiwowinta a kasa ta ce “Yaya na gode madallah Allah Ya saka da alheri. Sai ta fara hawaye shar daga idanuwanta ya ce “A’a Hannah kukan me kike yi ne? Kada fa in kasa tafiya in naga kina
kuka.Ya sa hannu a aljihu ya ciro wani farin hankici ya mika mata ya ce ta goge fuskarta kuma baya son ganin hawaye a fuskarta. Ta taso tana rakashi yana mata hira
mai dadi akan ta kwantar da hankalinta ba zai iya kaiwa wata biyun bama zata ganshi ya dawo.
Kuma ko da basa tare zuciyarsa na gareta. Direban da ya kawo Ramlah shine ashe ya kawo Haisam. Hannah ta ce “A’a ashe tare kuke kaki shigowa kasha ko ruwa ma?
Shehu ya ce “Ba komai suna da ruwa a mota. Ya durkusa har kasa ya gaishe da Hannah. Taga abincin
gwangwani iri- iri da lemon gwangwanaye ga robobin ruwan
swan nan a cikin motar sai taja bakinta tayi shiru. Don da har zata ce sai sun tsaya sunci tuwo. Taga masu cin irin wannan daula ya za’ayi su iya cin tuwon su miyar
kuka lami sai wake aka watsa a ciki. Haisam ya ce da direba ya bude but ya shigar da kwalayen da suke but din cikin zaure. Kwalayene manya-manya guda uku, makil suke da kaya. Daya na ruwan swan ne, daya na lemo iri-iri ne da kifin gwangwanaye da biskit da alawoyi karamin cikinsu kuma cike yake da kayan shafe- shafe na kwalliyar *yan mata, hoda, jan baki, mayukan shafawa a jiki dana gashi dana hannu. Daman Haisam mai son irin wadanan abubuwanne shi yasa ya siya mata mayukan gyara ta sake yin fes. Ga turarurruka designers abun baya misaltuwa tsadaddu.
Hannah ta langwabar da kai, ta rike murfin motar Haisam kuma na zaune a cikin motar gidan gaba. Yayin da Shehu direba ya tsaya can kofar gida yana jira su kare sallamar. Ta yiwa Haisam wani luguiguitaccen kallo cikin murya sanyayyiya ta ce “Yaya Haisam na gode. Ban san wacce kalma zanyi amfani da ita wajen nuna maka godiyata ba, tun ina karama kake fama dani har yau ba ka daina ba Ubangiji Allah Ya saka maka da alherin Sa. Ya ce “Kina bata bakinki wajen gode min, balle harki dinga tunanin kalmar da zaki yi amfani wajen nuna min godiyarki. Ni a tunanina duk abinda nayi miki dole ne a wajena ba sai kin gode
mun ba ki dauka aikina ne ai dole inyi miki. Hannah tayi dariya ta ce “Haba Yayana ni na fara saka haka a zuciya? na gode dai zance. Daga karshe suka yi sallama akan zai bugo mata waya. Yana tsokanarta wai yaga duk ta rame ko bata son aurensa ne, za’ayi
mata auren dole. Hannah ta kasa bashi amsar wannan tambayar ta bishi da kallo direba yaja motar suka tafi.
Yana dago mata hannu itama tana daga masa. Bata shiga gida ba sai da ta daina hango fitilar motarsu.
Kawu Ahmad da matarsa har sunfi Hannah mamaki da tsananin farin cikin wannan kyaututtukan na Haisam da matarsa. Raba dare suka yi kawai suna kallon dukiya suna sumbatu. Hannah kuma ta shaida musu cewar ya ce bai yadda a siya mata ko da cokali ba na kayan daki shi zaiyi komai. Nan Kawu Ahmad ya sake jin wani sabon farin ciki ya lullubeshi. Sai wajen sha biyun dare sannan Hannah da Kawunta da matarsa
suka shiga dakunansu don su kwanta. Hannah na shiga nata dakin ta jawo kofa ta bame sai kuwa ta dauko kwalin wayarta ta fara karanta yadda ake amfani da ita. Abun ka da Nasara ya rubuta
dalla- dalla yadda ake amfani da ita in har ka iya karanta turanci zaka fahimta nan take karfe daya dai-dai
aka kawo wutar lantarki. Hannah ta mike daga kan katifarta taje ta jona caja a soket ta jona wayar sai nan da nan taga ta fara caji. Murna ta rufeta ta koma ta kwanta. Taji bacci yaki zuwa sai tsananin tunanin Haisam. Ta ga da wannan kwanciyar da take tana ta tunani gara ta tashi tayi *yan nafilfili ta godewa Allah da Ya bata abin da ta dade tana nema.
Bayan tafiyar Haisam da kwana hudu. Hannah na kwance a dakinta misalin karfe goma sha daya na
dare taji wayarta ta hau kara ta zabura ta tashi zaune ta jawo wayar tana kallo taji bata daina karar ba. Sai ta ce a ranta ko Haisam ne yake kira. Ta jawo kwalin wayar da sauri ta sake karanta direction din taga inda ya kamata ta danna idan ankirata. Wayar dai ringin take ana sake radialling. Hannah ta dannan wajen da ya kamata ta dannan don amsawa.

About AIS

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *