[Advertisements⬇️]

Gangar jikinsa na aura23 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter 23

Zuciyar Hannah kuwa tunda uwarta ta haifeta bata
taba jin farin ciki irin na yau ba taji duk ta manta
kunci da bakin cikin da ta shisshiga ada. Tamkar
ba’a taba bata mata rai ba a duniya balle tayi
kuka. Haisam ne yanzu wannan a gabanta bai
mutu ba ashe? Kai Allah Shine abin bautawa da
gaskiya mai rayawa mai kashewa mai yin duk
yadda yaso da bawansa. Hannah take jinjinawa a
ranta. Ramlah kamar tafi kowa farin ciki a ranta
kasancewar Haisam bai mutu ba ta sanadiyyar jefa
shi cikin kunci da tayi ta hana shi ya auri wacce
yake matukar so, bayan haka babu wani da namiji
da take so fiye da dashi a duniya har yau. Ramlah
na son Haisam fiye da tunanin duk wanda yasan
soyayya. Wani babban Malami ne ya rufe taro da
addu’a akan Allah Ya kara bawa Haisam lafiya.
Bayan an shafa ne Ramlah ta mike ta ce tana da
magana aka bata izinin yin maganarta. Bayan ta
nemi gafarar Haisam da Iyayen Haisam da Hannah
da duk wasu *yan uwansa da suka fada halin
tashin hankali a sanadiyyar wannan ciwo na
Haisam, sai ta zo gaban Haisam ta durkusa ta
dube shi tayi murmushi ta ce “Haisam ina neman
wata alfarma a gareka idan Allah (S.W.A) Ya baka
lafiya ina so ka auri Hannah saboda a yanzu
Hannah bata da miji ni zan biya sadaki, lefe, kayan
dakin amarya da duk hidimar da za’ayi a bikinku,
nayi kuskure ada dana hana ka auri Hannah yanzu
na gane kuskurena. Haisam yayi wani lallausan
murmushi ya gyada kai don bashi da karfin yin
magana. Sai gaba daya aka dauki kabbara duk
wajen, sai kowa ya fara shiwa Ramlah albarka
musamman Mahaifan Haisam. Hannah ta ji wani
sanyi kamar kankara a ranta abun mamaki Ramlah
ta amince ta aura mata Haisam da kanta babu
abinda take yi a ranta sai godiya ga Allah wani
sabon Imani ya kutso a ranta ta sake gasgatawa
kowa yayi tawakkali ga Allah, Allah Zai saka masa
ta wata hanyar da bai taba zato ba.
Allah Shine
mai iko Shine yake bayarwa a duk sanda Yaso.
Mai hakuri baya tabewa a sannu zaiga biyan
bukata. Duk tsanani kada ka manta da Ubangijinka
yana sane da kai idan ka shiga kunci sai ya
kaddara maka jarabawa ce don ya gwada imaninka
Allahu Akbar.
Mahaifin Ramlah ne ya sake rufe taro da addu’a
ya dinga shiwa Ramlah albarka da fatan alheri a
rayuwarta da sabuwar abokiyar zamanta Hannah.
Jama’a na amsawa da amin daga karshe aka
shafa jama’a suka fara watsewa. Ramlah ta duka
gaban Mahaifiyar Haisam ta ce “Hajiya abar min
Haisam anan gidan ni da Hannah zamu ci gaba da
kula dashi. Ko tantama Mahaifiyar Haisam ma
bata yi ba ta amsa da “To shikenan. Don tasan
barin Haisam a kusa da Hannah babban maganin
wannan ciwon nasa ne. Kowa ya tashi ya nufi
wajen motarsa don tafiya gida, babu kowa a falon
daga Haisam sai Ramlah a kusa dashi da Hannah
da Amratu kanwarsa *yar kimanin shekaru goma a
kusa da Hannah suna zaune a gefe. Ramlah ta
fuskanci Haisam ya gaji da zaman alamar yana so
ya kwanta sai ta ce “Bari in dauko maka filo a daki
ka dan kwanta kafin in hada maka dan shayi
kasha, kasha magani sannan in kai ka daki ka
kwanta. Ta mike ta nufi daki. Hannah ta dago
zata kalli Haisam taga babu abinda Haisam yake
yi sai kallonta tamkar ya sami talabijin a gabansa
ko kiftawa baya yi. Tayi murmushi ta ce “Yaya
Haisam sannu. Ya dan lumshe ido ya gyada kai.
Ramlah ce dauke da filo ta iso wajen da suke gami
da yin sallama. Hannah ta amsa. Ramlah ta ajiye
filon akan doguwar kujerar da Haisam ke
kishingide ta kama shi ta gyara masa kwanciya ya
kwanta sosai. Hannah ta yunkura ta tashi tana
rike da hannun Amratu ta ce “Aunty Ramlah zamu
shiga daki mu kwanta, wanne dakin ne? Ramlah
tayi murmushi ta ce “Haba Hannah aike ba
bakuwa ba ce yanzu, duk dakin da ya yi miki shiga
ki kwanta ai gidanki ne. Amratu tayi caraf ta ce
“Aunty Hannah zo muje dakina mu kwanta zaki ga
*yar tsanata da Aunty Ramlah ta siyomin. Taja
hannun Hannah suka tafi har sun juya Hannah ta
juyo da kyakkyawar fuskarta ta kalli Ramlah da
Haisam tayi murmushi ta ce “Sai da safen ku.
Sannan ta juya suka tafi. Haisam har dan daga kai
yake don leken Hannah ganinta yayi tayi kyawun
da duk a cikin kabilu, kama daga bakar fata har
farar farar fata turawa da Indiyawa bai taba ganin
wacce tayi masa kyau kamar Hannah ba
musamman a yau. Ramlah ta tsaya kawai tana
kallon Haisam taga kamar zaije ya jawo Hannah
ya rungumeta koma ya hadiyeta yadda yake binta
da kallo, sai tayi murmushi ta dan taba hannunsa
ya juyo ya kalleta tayi fari da ido ta kanne ido
daya ta ce “Haisam ya akayi ne ko Hannah ta
dawo muyi hira ne? Sai yayi murmushi ya koma ya
kwanta. Ramlah ta wuce kicin don hado masa dan
abu mai ruwa-ruwa da zai sha.
Bayan Hannah da Amratu sun shiga daki, Amratu
tayi ta nunawa Hannah kayan wasanta da
kasissina cartoons dinta da litattafan makaranta.
Hannah tayi ta taya ta suna wasa da *yar
tsanoninta har tsawon awa guda bayan shigarsu
sannan Hannah ta ce “To Amratu ya isa haka jeki
kiyi wanka ki dauro alwalar sallar isha’i ki fito
nima zanyi wankan da alwalar. Da ke akwai
bandaki a cikin dakin. Amaratu ta fada ban daki
bayan ta fitone Hannah ta shiga. Tana wanka
Ramlah ta shigo dauke da sabuwar doguwar riga
mai rubi biyu ta barci mai tsananin laushi da
santsi ta kawo wa Hannah sai ta bawa Amratu ta
ajiye mata kafin ta fito, Ramlah ta fito ta jawo
musu kofa ta rufe. Hannah na fitowa Amratu ta
mika mata sabuwar rigar bacci dal a leda ta ce inji
Auty Ramalah. Cike da fara’a Hannah ta karbi rigar
baccin ta saka sannan ta tayar da kabbarar sallar
isha’i. Har Amratu ta gaji da jiran Hannah ta idar
suyi kallon kaset din catoon taga Sallar take ta
jerowa har bacci ya dauketa Hannah bata idar ba.
Sai ukun dare sannan Hannah ta idar da nafiloli da
addu’oin da take na goduya ga Allah (S.W.A) da
Ya nuna mata wannan rana da fatan Ubangiji Allah
Ya tabbatar da abinda Ramlah take shirin hadawa
da fatan Allah Ya bawa Haisam lafiya. Sai kuka ya
kece mata don farin ciki. Ta hau gado kusa da
Amratu tasa hannu ta kashe fitila sannan ta
kwanta. Wani laushi ne ya nutsu a cikin tsokokin
jikinta don bata taba kwanciya a irin wanan katifar
ba tunda take. Sanyin na’urar sanyaya daki ne
(split A.C) yake ratsa hudojin jikinta ta lumshe ido
sai ta hango fuskar Haisam dauke da gwarza-
gwarzan idanuwansa yana kallonta. Bata dade ba
bacci mai dadi ya sureta. Alarm din agogo ne ya
tasheta karfe biyar dai-dai asuba tayi, tayi firgigit
ta bude ido taga fitila a kunne Amratu harta shiga
ban daki tana alwala. Hannah tayi murmushi ta ce
a ranta “Birni sai dan birni ga kudi ga ilimi, yarinya
karama tasan ta saita agogo ta farka da asuba
tayi sallah.
Bayan Hannah da Amratu sun idar da sallah. Sai
suka koma gado suka kwanta wani daddadan barci
ya sake sure su. Goma dai-dai Hannah ta bude ido
sai taga gari yayi tangararai. Tayi firgigit ta tashi
zaune taga rana harta ralle gari. Ta fada bandaki
dan yin wanka ta dauki brush dinta a cikin jakarta
daman ta taho dashi. Ban dakin ma abin kallo ne a
wajen Hannah taga komai na tangaran ne ga
madubai a kewaye da bandakin. Ruwan sanyi da
na zafi a shaya da fanfuna abun gwanin ban
sha’awa. Abubuwa da yawa sai dai Hannah ta
taba ta barshi saboda bata san amfaninsa ba bata
taba gani ba. Aljannar duniya kenan gidan Haisam
kamar a turai. Duk inda ka zagaya falo ne iri-iri
wajen cin abinci dakuna masu gadaje na alfarma
abin baya misaltuwa.
Ramlah tayi matukar mamakin Haisam dubi yadda
yake tsananin jin jiki amma sai ta ganshi daram
kamar ya warke sai dai rashin karfin jiki. Babban
abin da yafi bata al’ajabi shine tunda take da
Haisam bai taba tsayawa yana kallon fuskarta
yana yi mata murmushi ba sai a yanzu data kawo
masa Hannah har ma ta ce zata aura masa ita.
Wannan abunda Ramlah tayi wa Haiam yaji
tsantsar tsanar da yake yiwa Ramlah ta fara
komawa soyayya kawai don ta fara son Hannah.
Haisam ya ji duk duniyar nan babu wanda ya taba
masa kyauta mai girma kamar Ramlah yaga babu
abinda ya kamata ya saka mata itama sai ya karbi
soyayyar da take yi masa shekara da shekaru.
Tunda ta hada shi da wacce yake azabar so. Duk
sanda zai kalli fuskar Ramlah sai yaji sanyi yanzu
maimakon haushinta da yake ji ada. Ramlah ta
fuskanci hakan duk inda tayi Haisam na binta da
kallo yana murmushi Haisam yaji dadin wannan
al’amari amma Ramlah tafi jin dadi kamar a
mafarki take ganin wadannan al’amari har Haisam
ne yake daga ido ya kalli fuskarta har yayi mata
murmushi. Turkashi !!!
Kwanci tashi yau kwanan Hannah shida a gidan
Haisam da Ramlah. A kullum da safe Hannah da
Amratu suna fitowa daga dakinsu su iske Haisam
da Ramlah a falo ko wani lokaci ma a daki suke
samun su, su shiga su gaishe su suyi masa ya jiki
su koma dakinsu. Duk lokacin cin abinci Ramlah
tana lekowa ta kirasu, su fito suci abinci a dinning
table, kuku biyu ne suke dafa abinci a gidan, masu
share-share da goge daban. Dan haka babu aikin
da Ramlah take yi a gidan balle Hannah ta tayata.
Sai dai suyi wanka su zauna suna kallon satelite
da kaset. Dinkuna masu kyau da tsada Ramlah
tasa aka dinkawa Hannah. Dan kunne da sarka da
zobe na gwal Ramlah ta bawa Hannah. A kwana
shidan nan ita kanta Hannah tasan ta canja ta
zama *yar birni. Turarruka kala-kala Ramlah ta
sissiyo ta bata. Haisam kuwa jiki Alhamdulillahi
sauki yana samuwa yana tashi tsaye yana dan
takawa daga daki zuwa falo, in ya gaji ya zauna a
kan kujera a falo. Ranar da Hannah ta cika sati
guda da sassafe ta tashi ta fara harhada kayanta
a jaka na tafiya. Dan taga ya kamata ta tafi gida
kuma tun ana marmarinta kuma jikin Haisam yayi
sauki gara ta tafi duk da ba hakan take so ba.
Bayan sun gama cin abincin safe ita da Ramlah,
yau Amratu ta tafi makaranta tun bakwai da rabi
na safe. Haisam daman ba abinci yake ci ba yana
kallonsa yana kurbar shayi. Hannah ta dubi
Ramlah tayi murmushi ta dan sosa kai cikin ladabi
da alamar jin kunya ta ce “Aunty Ramlah babu
abinda zance miki sai godiya Allah Ya saka da
alheri kuma Allah Ya kara bawa Yaya Haisam
lafiya. Tunda naga jikin nasa yayi sauki inaso zan
koma gida yau kar suji shiru su fara tunanin ko ba
lafiya ba. Ramlah tayi murmushi ta ce “Har za ki
tafi ki barmu, bako zai yi halinsa kenan, ai ba laifi
kinyi kokari tunda kinyi mana sati guda mun gode.
Akwai wasu atamfofi nasa an siyomin gasu can a
jaka na kuma zuzzuba kudi a ambulan dubu
goma-goma kowacce na rubuta sunanta a bayan
ambulan din daman ina da jerin sunayenku saiki
rarrabawa *yan kungiyata in kinje. Hannah ta duka
tayi godiya. Ramlah ta tashi ta shiga falon Haisam
ta iske shi a zaune kan doguwar kujera ya mike
kafafuwansa akan centre table taje ta zauna akusa
dashi tana yi masa murmushi ya dago ya dubeta
ya ce “Uwar gida yaya akayi ne? Tayi fari da
idonta ta ce “Ranka ya dade bakuwarmu ce take
so yau ta koma gida ta ce kar hankalinsu ya tashi
in sunji shirun yayi yawa. Haisam yaji wani dum a
ransa ba haka yaso ba yaso Hannah ta dade yana
ganinta yana jin dadi. Can ya nisa ya ce “Har zata
gudu ta barmu baza ta sake kwana biyu ba?
Ramlah ta ce “A’a gani nake gara taje in yaso ta
dawo daga baya kaga ni na daukota daga garinsu
karsu dauka guduwa nayi da ita. Haisam yayi
murmushi ya ce “To shikenan Allah Ya kaita gida
lafiya. Ramlah ta ce “Amin bari in kirata ta shigo
tayi maka sallama. Ramlah ta tashi ta fito falo ta
duba wajen cin abinci taga Hannah bata nan sai ta
nufi dakin Amratu inda suke kwana. A bakin kofa
suka gamu Hannah ta ratayo jakarta zata fito.
Ramlah ta ce “Oh, Hannah har kin fito lallai Kano
ta ishe ki muna sonki ne ke kuma kina gudun mu.
Hannah tayi dariya ta sunkuyar da kai kasa ta ce
“Aunty Ramlah ba haka bane garin namu ne da
nisa shiyasa na fito da wuri don in isa da wuri.
Ramlah ta ce “Haka ne sai kizo ki yiwa Haisam
sallama yana nan a falonsa. Hannah ta ce “To, sai
ta ajiye jakar ta tana biye da Ramlah har zuwa
falon Haisam sai Ramlah ta fito ta barsu. Ta fito
ta nufi dakinta yayin da zuciyarta ta hau dukan
uku-uku tana fargaba game da yadda taga kyau
irin na Hannah musamman yau da tayi ado da
wata tsaleliyar shadda data dinka mata
combination ja da baki ga wannan lallausan gashin
nan nata a tufke a bayanta. Zuciyar Ramlah na
nuna mata Hannah fa tayi miki fintinkau a fagen
kyau idan baki yi da gaske ba duk wannan iya
kwalliyar taki da har mutane suke yaba miki
Hannah zata zo ta fiki iyawa. Kalli yadda tayi wani
kyau tamkar *yar tsanar roba. Sai wata zuciyar ta
ce Ramlah rufawa kanki asiri ki kwantar da
hankalinki karki sa wannan tunanin a zuciyarki har
wani tashin hankali ya biyo baya yadda Haisam ya
kwallafa ransa da son Hannah kema kika kwallafa
sonsa a ranki to in kina so ki zauna kalau ki sami
soyayyarsa to kiso Hannah tunda gashi kin fara
gane kansa yana nuna miki soyayya.
Hannah ta durkusa a gabansa ta ce “Yaya ina
kwana, yaya jikinka? Yayi narai-narai da ido ya ce
“Hannah da sauki. Tashi daga nan kizo nan kan
kujera ki zauna. Hannah ta tashi ta zauna a wata
kujera a gefensa kowannensu zuciyarsa cike da
tsananin farin ciki sai suka ji dama kar su rabu su
zauna din-din-din suna ganin junansu. Kallon-kallo
suke yiwa junansu na tsananin kaunar juna. Yayi
murmushi ya ce “Hannah zaki tafi ki barni ne,
bayan ina ganinki ina jin dadi ko bakyaso inji sauki
da wuri ne!!
 kece fa kwayar magananin da take kwantar
min da ciwon. Hannah ta sunkuyar da kai tana jin
kunyar bada wannan amsar. Ya ce “Yaya naji kinyi
shiru ne? Hannah ta ce “Yaya dole ce tasa ba a

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

son raina nima zan tafi in barka ba. Amma nayi

maka alkawari kullum nayi Sallah zanyi maka
addu’a Allah Ya sauwake maka. Haisam ya gyada
kai ya ce “Nagode amma ina so ki min alkawari a
rana zaki dinga tuna ni har sau biyar, duk lokacin
da kika zo yin Sallah zaki tunani kiyi min addu’a?
Hannah tayi dariya ta ce “Ina tuna ka fiye da sau
hamsin a rana ba biyar bama ko ina ganin ka, ko
bana ganinka. Haisam ya gayara zama ya juyo
yana kallon Hannah sai tasa gyalenta ta rufe ido
alamar jin kunya. Haisam yayi ajiyar zuciya ya ce
“Naji dadin duniya da za ki dinga tuna ni sau
Hamsin a rana.. Yanzu ki fada min kalma daya da
zan dinga tunawa a raina a duk lokacin da
tunaninki yayi min yawa sai ta kwantar min da
hankali. Hannah tayi shiru can ta dago tana
murmushi ta kalli Haisam suka hada ido taga ya
kura mata ido kawai yana kallonta. Sai ta sake jin
kunyarsa ta lullube fuskarta ta sake jawo gyalenta
ta rufe ido ta mike tsaye a hankali ta nufi kofar fita
tana tafiya a hankali. Haisam ya ce “A’a tafiya za
ki yi ko sallama babu, kuma ai baki bani amsar
abinda na roka a wajenki ba. Hannah ta juyo a
hankali ta kalle shi kallo irin wanda yake jinsa har
tsakar kansa ta ce “Abinda nake so kasa a ranka
shine ko da GANGAR JIKINA bata tare da kai
zuciyata tana wajenka. Haisam ya sake dagowa ya
dubi Hannah sai yaga ta daga masa gira tayi fari
da ido ta ce “Kada ka manta soyayya gaskiya ce.
Na tafi na barka lafiya ina kuma yi maka fatan
kara samun lafiya. Haisam ya kasa magana sai
kawai ya bita da kallo harta daga labulan kofar ta
fice. Ya rike baki yayi shiru jinsa yake kamar ba’a
duniya yake ba, kamar a aljanna aka jefashi yau
gashi ga Hannah a matsayin masoya masu shirin
yin aure harma wadannan dadadan kalamai suna
fitowa daga bakinta izuwa kunnuwansa. “I can’t
believe this, Hannah! Hannah ce kuwa. Haisam
yake fada a baiyane. Ramlah ce ta shigo falon ya
dago ya kalleta fuskarsa cike da fara’a farin ciki taf
a zuciyarsa a yau. Ta ce “Yallabai kun gama
sallama da Hannahr ko? Ga Shehu direba ya fito da
mota zai kaita. Haisam ya ce “Munyi sallama da
Hannah Ramlah sai dai ki bata kudin da zai isheta
tayi hidindimunta Aunty Ramlah. Ta dan harareshi,
su duka suka sa dariya ta ce “Kaima Aunty zaka
ce min? Ai na bata kudi ranka ya dade duk abinda
ya kamata in bata na bata, kada ka manta in so
yayi so ra’ayi yana zuwa daya. Haisam ya ce “kika
ce me? Tayi murmushi ta ce “I feel what you feel
saboda ina sonka. Haisam yayi murmushi ya ce
“Ramlah! Ramlah!! Ramlah tayi dariya sannan ta
fita. Ta raka Hannah har bakin mota sai da suka
fita daga get sannan ta daina daga musu Hannu.
Haisam ne ta wundon dakinsa yake kallon Hannah
har suka tafi, yayin da ya ji wani kululun bakin ciki
na rabuwa da ita.
Bayan tafiyar Hannah da kimanin wata taji shiru
babu Ramlah ba Haisam. Gashi babu waya a
garinsu balle ta buga musu taji lafiyar su. Tun
tana boye damuwarta akan haka har Hajir matar
Kawunta ta fara fuskantar halin da take ciki. Ayau
da yamma bayan Hannah ta idar da sallar la’asar
sai ta shiga ta sallo wanka tazo ta hade da wani
sabon dinkinta na material din da ake yayi.
Material din baki ne anyi masa kwalliya da jar
fulawa. Matsatsan dinki ne akayi, a rigar zanin ma
anyi masa kwalliyar iri daya da yankar rigar.
Hannah ta tufke gashinta da jan madauri (ribon)
ta dana daurin dankwali mai kyau. Tasha hoda a
fuskarta da jagira sannan ta sako sarka da dan
kunnenta da zobe na gwal da Ramlah ta bata.
Haka kawai yau da yamman nan taji tunanin
Haisam yayi mata yawa shine take rayawa a ranta
shine tayiwa wannan kwalliya. Ta tsaya a gaban
mudubi ta kalli kanta ta juya gefe ta sake juyawa
baya taga lallai tayi kyau sosai kamar ba ita ba.
Dama Yaya Haisam na kusa mana yaga wannan
kwalliya da tayi.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]