[Advertisements⬇️]

Gangar jikinsa na aura10 - Bankinhausanovels
Mon. Mar 27th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter 10

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Haisam ya dada kyau sosai
hanakalinsa ya kwanta ya zama
mai kudi baya ga albashinsa
account Mahaifinsa ya bude
masa yana zuba masa ribar da
suka ci a kamfaninsu duk wata
yake warewa *ya*yansa, ga
Hannah ba laifi ta girma wahalar
da take sha a gida ta ragu
abubuwa da yawa ta fara
takawa Iya Abu da *ya*yanta
burki, tana kwatar kanta dole
wasu abubuwa suke raga mata.
Don haka kallo daya zaka yiwa
Haisam kasan dan gidan wani
gawurtaccen mai kudi ne
saboda suffarsa ta ya*yan hutu
ce, fari ne sol fatarsa mai haske,
yana da dara-daran ido da
dogon hanci, mai yawan gashin
ido dana gira gazar-gazar. Wani
dan siririn
gemu ne ya zagaye dan
madaidaicin bakinsa (qauter
million) gashi dogo mai *yar
madaidaiciyar kiba. Haisam yana
daya daga cikin irin mazan da
kowacce *ya mace take
mafarkin samun irinsa. Gashi a
makarantar *yan mata masu ji
da kudi da kyau ga gayu. Don
haka kullum Haisam sai ya sami
wasikun *yan mata akan
teburinsa a ofis dinsa sun jefa
masa, wai suna sonsa, soyayya
mai tsanani kuwa sai kawai yayi
dariya ya yaga ya zubar koda
kuma
ya hadu dasu bazai nuna musu
yaga sakonsu ba, *yan aji shida
ne suka fi yi masa wasikun
amma
wasu *yan aji biyar din suna
rubuto masa. Shi gani yake duk
hauka suke zasu gaji su daina,
gasu
kyawawa dasu amma baya
ganin kyawun, *ya*yan attajirai
amma shi bai dame shi ba, shi
kawai ya zo ya cika burin daya
kudira ya tafi ne. Senior Juwairiya
itace shugabar dalibai (Head
girl)
Juwairiya kyakkyawar gaskece
fara sol harma akan ce suna
kama da Hannah, gata
Mahaifinta
wani babban manager ne a
wani banki a Lagos, tana ji da
gata da dukiya ga tsananin
kokari tafi
kowa kokari a shekarar. Amma
sai Allah Ya jarabbeta da
tsananin son Auncle Haisam tun
ba yau ba gashi kuwa da yawa
daga cikin Malaman
sun mutu a sonta, ita bata son
su tafi son Haisam. Ta aika masa
da wasiku sunfi a kirga amma
shiru ko
alama Haisam baya nuna mata
Ma yaga wasikarta.
Data gaji da aika masa wasikun
saita dinga aika kawayenta
baro-baro suke tararsa su gaya
masa,
amsar daya basu cewa yayi duk
yarinyar data sake tararsa da
sakon Juwairiyya sai ya sabar
mata. Don haka Juwairiyya ta
rasa yadda zata yi ta shawo kan
wanda take so. Ranar wata
litinin da daddare an fito
karatun dare (prep). Juwairiyya
ta sami kan wata baranda ta
zauna tana tunani don ita son
Haisam harya fara dasa mata
wani ciwo da yake
damunta a zuciya har take kasa
karatu sosai gashi kuwa tafi
dukkan *yan makarantar kokari,
don haka nema aka nadata
shugabar dalibai.
Zaman da tayi wucewar Haisam
kawai take so ta gani sannan ta
iya bacci. Salaha Nura ita ce
babbar
aminiyar Juwairiyya tazo
giftawa zata tafi ajinsu taga
kawarta a zaune a baranda ita
kadai, taje
wajenta ta dade a tsaye a kanta
Juwairiyya bata sani ba. Ta
dafata sannan tayi firgigit ta
dago,
Salaha Nura ta zauna a kusa da
Juwairiyya ta ce “Juwairiyya
tunanin meye kike, ke kadai
kowa
yana aji? Juwairiyya ta nisa tace
“Allah Salaha ina son uncle sosai kamar zan mutu.
Salaha ta tuntsire da dariya ta ce
“Uncle Haisam wai? Shegu
sunan da kuka saka masa kuma,
to Juwairiyya yaya zamuyi, kin
rubuta a rubuce yaki, kin
aikemu ya zazzagemu idan kikaje da kanki  qila ya yarda
Kwarjini yake mun bazan iya
tarar sa ba. Inji Juwairiyya.
Salaha ta ce “To maye abunyi?
Juwairiyya ta zunguri Salaha ta
nuna mata Haisam ne ya
tunkaro inda suke daga staff
quaters ya
karaso inda suke. Suka duka
suka gaisheshi cikin ladabi, ya
ce “Oh shugabar dalibaice da
labour
prepect? Suka ce mune Sir, ya ce
“Wato kun kora yara aji ku
kunzo kun zauna kuna hira ko?
Kamata yayi kufi kowa karatu
yanzu tunda kune masu shirin
yin WAEC da NECO da JAMB ko?
Suka amasa da “Eh ba hira muke
ba wani muke jira, Juwairiyya ta
marairaice murya ta ce “Amma
na ganshi yanzu zamu tafi
daman fatana in ganshi kawai.
Haisam ya
gane abun da take nufi sai
kawai yayi sauri ya katseta ya ce
“Idan zaku tafi gashi kuje S.S 1A
Science class ku bawa Hannah
Abubakar Imam. Ya mika mata
wata leda a daure ya juya ya
nufi ofishinsa ya shiga sannan
ya rufo kofar.
Juwairiyya ta ce da Salaha,
“Kinga abunda nake gudu ko
shariya ce da wannan mutumin
ko fuska
baya bani da zan gaya masa
abunda yake damuna.
Salaha Nura ta ce “To wai ni na
lura meye tsakanin Uncle Haisam
da Hannah Abubakar Imam ne?
Kamar duk makarantar nan yafi
kulata komai Hannah haka zaki
ji yana ambata kamar shi ya
rada mata sunan. Juwairiyya ta
ce “Ance abokin wanta ne wai,
kuma saboda Rauda Shitu
kawar Hannah
ce ita ai kanwarsa ce. Salaha
Nura ta ce “To kanwar abokinsa
ai zai iya sonta. Salaha ta karbe
ledar da ya bawa Juwairiyya ta
kwance sai suka ga magunguna
na ruwa dana kwaya ne, na
zazzabi dana tari ya saya mata.
Salaha ta tabe baki ta ce ”Abbas
“Lallai magunguna ya sayo mata
tafi karfin ma tasha na clinic din
makaranta kenan. Juwairiyya ta
ce “Zo muje nasan abunda zan
hadawa yarinyar nan, Salaha ta
taso suna tafe suna zancen suka
nufi ajin su Hannah. Juwairiyya
ta ce “Ba Uncle Haisam ya ce
kada wata ta kuskura ta kara kai
masa
sakona ba to ni kuma Hannar da
yake ji da ita daga yau ita zan
dinga aike wajensa. Salaha ta ce
“Kwarai kuwa haka za’ayi muga
ko itama zai korota din. Ta
wundo Juwairiyya ta leka ta ce
“Ina Hannah Abubakar? *yan aji
suka ce “Gata can a seat dinta a
kwance bata da lafiya, ta ce “Ko
ciwon ajali take ta taso ta
zagayo tazo ina kiranta. Nusaiba
ce ta
tasheta ta ce “Hannah kije
senior Juwairiyya na kiranki.
Hannah ta daga ido da kyar ta
ce “Bazan iya tashi ba bani da
lafiya, jikinta zafi kau kamar
wuta. Jijiyoyin kanta sunyi rudu-
rudu don ciwon
da yake yi mata. Juwairiyya ta
daka tsawa ta ce Hannah ta taso
Allah Yasa asibiti ne a kanta ba
jinya ba. Nusaiba da Rauda suka
rirrikota suka tasheta tsaye,
Juwairiyya ta daka musu tsawa
ta ce musu munafukai su saketa
ta zo da kanta. Haka Hannah ta
fara tafiya tana rirrike bango ta
fita ta zagaya bayan aji inda
suke. Juwairiyya ta mika mata
ledar
da Haisam ya bayar a bata suka
ce “Gashi in ji saurayinki.
Hannah tayi jigum tana mamaki
can ta
ce “Waye saurayina? Salaha ta ce
“Zaki sanshi munafuka.
Juwairiyya ta mika mata wata
takarda ta ce “Ki kaiwa Uncle
Haisam kice ina jiran amsa
yanzu
kice nace miki karki sake ki
dawo babu amsa.
Hannah ta fara tafiya jiri yana
daukarta ji take kamar zata fadi
saboda yini tayi cur a kwance
babu
ko dan tea a cikinta. Ta isa
ofishinsa ta kwankwasa yayi
mamaki da yaji ana kwankwasa
masa kofa yanzu, ya tashi ya
bude sai yaga Hannah a tsaye.
Mamaki ya kamashi ya ce
“Hannah lafiya? Keda baki da
lafiya kika iya tahowa? Hannah
ta cije baki
gami da rike bango kamar zata
fadi ta ce “Aikoni wajenka aka
yi. Ya ce “Aike kuma, waye ya
aiko ki? Ta mika masa wasika ta
ce “In ji senior Juwairiyya da
senior Salaha sunce dole in taho
musu da amsa
kar in zo babu amsa. Ya bata rai
ya karbi wasikar ya bude ya
karanta. Wasika ce irin ta kullum
daga
Juwairiyya ya ceci rayuwarta
tana sonsa. Haisam ya cikuikuye
ya wurgar ya ce “Sun baki
magungunanki? Ta ce “Ah ina
jin sune anan, ya
karba ya bubbude yana tsiyaya
mata a murfi yana
mika mata sai ta karba tasha. Sai
da ya tabbatar ta sha dukka
sannan ya daure ledar ya mika
mata ya ce ta wuce daki ta
kwanta gobe idan taga baza ta
iya fitowa aji ba tayi
kwanciyarta zai sanarwa da
duty master. Daga karshe ya ce
“Sai da safe Allah Ya
baki lafiya, Hannah ta ce “Amin.
Har ta juya zata tafi sai ta tuna ta
juyo ta ce masa “Me zan cewa
senior Juwairiyya? Ya ce “Ki ce
nace tazo ta karbi amsar da
kanta. Hannah ta amsa da to
sannan ta tafi. Daman su
Juwairiyya na zaune a wata
baranda suna hango su. Hannah
ta zo wucewa suka kirata tace
musu ta kai masa ya ce amsar
taje da kanta ta karba. Salaha ta
ce “Jeki to. Juwairiyya ta nisa ta
ce
“Kinga Haisam ko wallahi
wulakanci yake shirin yimin
tunda ya ce inje da kaina ni
nasan ba wata maganar
amincewa zai yi min ba. Saboda
ai na gani cukuikuye wasikar
tawa yayi ya yar a kasa, ya buge
da bata magani ai dole ma son
Hannah yake.
Salaha ta ce “Amma kuwa sunan
yarinyar nan gawa don sai taci
ubanta a makarantar nan, mu
*yan S.S.3 muce muna sonsa
yaki ya so junior mu ai bazai
yuba. Je ki kiji abunda zai fada
miki don muci uwarta da hujja.
Juwairiyya ta mike ta nufi
ofishin Haisam tana wani
karkade riga tana gyara fuska.
Tayi sallama gami da tura kofar
zata shiga ya dakatar da ita da
hannu ya ce “Tsaya daga nan
baranda kiji abunda zan fada
miki. Don me kike sake yimin
aiken wasika bayan nace kada
wanda ya sake zomin da
wasikarki. Kuma wanne rashin
tausayi ne da zaki taso yarinya
marar lafiya ki aikota, duk
daliban makarantar nan, sai
Hannah?
Me yasa sai ita zaki aiko
Juwairiyya? Juwairiyya ta tsuke
fuska ta ce “Amma Uncle Haisam
duk aiken dana keyi baka taba
kirawoni kace me yasa nake
aiko kawayena ba sai dai
kacewa *yan aiken duk wacce
ta sake zuwa zaka sabar mata.
Me yasa baka
fadawa *yar aike ba a wannan
karon saini ka kira?
Haisam ya fusata ya daka tsawa
ya ce “Ina tambayarki kina
tambayata? To bari kiji yauce
rana
ta karshe da zaki yimin haka. Ki
rike darajarki da mutuncinki a
matsayinki na *ya mace
budurwa.
Idan dole sai kinyi soyayya a
makaranta ba karatu ya kawo ki
ba to ga sauran Malam da suke
rububin sonki amma ni bani da
ra’ayin soyayya, this is the last
warning bana son sake ganin
sako daga wajen ki sai anjima
kije.
Wani jiri-jiri Juwairiyya take ji ta
juya ta tafi tana kwafa. Salaha
tazo ta tare ta a hanya tana
cewa “Meye na hangoki a
baranda,
ofishinsa ma ya hanaki shiga?
Juwairiyya ta ce “Ke dai muje in
baki labarin yadda muka yi.
Daman
lokacin tashi daga prep yayi duk
dalibai sun dungumo daga
ajijuwansu sun doshi
dakunansu. Don haka zUwairiyya
da Salaha Nura sai suka nufi
hostel a hanya ta zaiyana mata
duk yadda suka yi
da Uncle mai kyau wato Haisam.
Washegari talata da sassafe
bakwai da rabi a lokacin dalibai
suke firfitowa daga dakunansu
zuwa ajijuwansu domin daukar
darussa. Uncle Haisam a tsaye
yake kem a bakin get din hostel
yana kallon masu fitowa daga
ciki. Mamaki ya kama dalibai
ganin sabon al’amari meye
Uncle Haisam
yazo ya tsaya anan da sassafe
haka ba shine da duty ba, ba
ranar inspection ba kuma,
kowacce
idan ta ganshi sai ta duka ta
mika gaisuwa ta wuce “Good
morning Sir. Can ya hango
Rauda da Nusaiba da Pamella
suna tahowa daga nesa ya
dauka Hannah ce sai da suka
karaso yaga babu Hannah a
cikinsu. Bayan sun gaisheshi ya
ce “Yau
kuma ina Hannah ko jikin ne?
Rauda ta waiga gaba da baya
taga babu kowa sai ta matso
kusa dashi ta ce “Hannah ba
lafiya tana cilinic a kwance acan
ta kwana, gabansa ya yanke ya
fadi ya ce “Zazzabi ne
ya rufeta? Nusaiba ta ce
“Wannan yafi zazzabi Yaya,
Rauda ta ce “Su senior
Juwairiyya ne suka yi mata
duka da tsakar dare kusan
dukkan S.S 3 sai da kowacce ta
doki Hannah jiya ina ji a sume ta
fadi da kyar Matrons suka zo
suka hana su. Muma bamu san
me tayi musu ba. Kuka mu ma
muka kwana munayi.
Nan da nan Haisam ya canja, ido
ya kada yayi jawur gashin
jikinsa ya mimmike kai kace
muku-mukun
sanyi ake. Amma duk da sanyin
safiya zufa yake yi. Ba tare daya
ce tak ba ya juya ya nufi clinic
inda
Hannah take a kwance ya same
ta rikkicif bata sanma inda
hayyacinta yake ba. Abinka da
farar
fata sai sawun bulalunda suka yi
mata jawur a jiki, har wuyanta
da fuskarta shatin bulala ne
lambar.
Ya dade a tsaye yana kallonta
kawai yasa hannu ya cire mata
wani ganyen Maina daya makale
mata a wuya a sanadiyyar duka
sai yaji jikinta zafi kau kamar
wuta, yaja mayafin dake kan
gadon ya
lullubeta. Babu kowa a clinic din
Nurse din ma bata nan, ya juya
ya fita a fusace ya nufi ofishin
principal. Ya shiga ofishin gami
da yin sallama ya sami waje ya
zauna bayan sun gaisa ta dubi
Haisam ta ce “Haisam lafiya yau
na ganka rai a bace duk
wannan fara’ar taka? Ya ce
“Dole raina ya baci saboda
kusan kashe wata yarinya akayi
a daren jiya a makarantar nan
*yan aji shida ne suka daki wata
*yar aji hudu da tsakar dare
kamar zasu kasheta tana cilinic
a kwance “Principal ta zabura ta
ce
“Subahanallahi,
ta danna
kararrawa masinja ya shigo tace
maza yaje aji shida ya kira mata
Juwairiyya.
Haisam da pricipal na zaune
sunyi jigun kowa yana tunani a
zuciyarsa. Can saiga Juwairiyya
ta karaso ita da wani Malami
mai suna Sahabi tazo ta durkusa
a kasa ta gaishe da principal,
principal ko ansawa bata yi ba
ta rufe Juwairiyya da fada tana
cewa “In har ba zaki iya hana a
aikata laifi ba a makarantar nan
banga amfaninki ba a matsayin
shugabar dalibai. Haisam ya ce
“Madam ai ita ce ta gaiyato
sauran *yan aji shidan suka
hadu suka yi dukan. Principal ta
ce “Oh har da ke head girl ku ka
hadu aka kusa kashe yarinya,
kiyi kneel down yau sai kun
yabawa aya zakinta. Uncle
Sahabi yayi caraf ya ce “Madam
tsaya kiji, Juwairiyya ta fadamun
duk abunda ya faru daman nan
zamu taho wajenki muka hadu
da masinja a hanya, a gaskiya
yarinyar ce bata da kunya wai
cewa tayi zata yi dambe da
Head girl shine Juwairiyya ta
danyi mata bulala uku labour
prefect tayi mata biyu. Ga
yarinyar can ma a
aji tana daukar darasi babu
wani zancen kisa. Haisam ya
fusata yayo kan Sahabi da fada
yana cewa “Karya zanyi musu?
Yarinyar da duk makarantar nan
babu mai shirunta da ladabi
yaushe zata ce zata yi fada da
Head girl? Kawai baza ka tsaya
kayi bincike ba don sun gaya
maka karya da gaskiya shine
zaka yarda, kaje clinic kaga
jikinta a farfashe bata san ma
inda hayyacinta yake ba.
Sahabi ya ce “Madam don Allah
ki raba mana rigima ki aika
clinic a dubo idan akwai wata
marar lafiya.
Babu kowa ta warke ta mike,
ba’a gabanmu Hannah tazo ta
wuce ba dazu ko ba Hannah ba
ce
wacce kake cewa an kusa
kasheta? Kuma kai duk wannan
hakilon da kake akan Hannah
saboda kai
saurayinta ne fa yasa kake
wannan. Sauran da ake duka ka
taba magana? Principal ta lura
maganar nan babba ce sai
manya sai ta ce da Juwairiyya ta
tashi ta tafi aji zata aiko ayi
kiranta. Fusakar Juwairiyya cike
da murmushi ta fice, principal ta
kalli Haisam ta ce “Kwarai tun ba
yau ba ansha fada mun kana
soyayya da Hannah. Dokar
makarantar nan an hana daliba
da Malami yin soyayya. Yanzu
na gane manufarka don an doki
budurwarka shi ne yasa kayi
magana ko? To daga yau zan sa
C.I.D
kada ka kuskura in sake jin ance
kana soyayya. Haisam ya fusata,
ransa ya baci, zuciyarsa ta hau
tafarfasa. Ya dakawa Sahabi
tsawa yaje har gabansa yana
nuna shi da hannu ya ce “Kai
Sahabi karya kake yi ni nafi
karfin ka yi min sharri kai da
Juwairiyya zaku gane kuranku a
makarantar nan.
Ni kake cewa ina son Hannah
ko? Bayan da bakinka kazo ka
sameni kana rokona in hadaka
da kanwata Hannah kana sonta
naki nace kabarta tayi karatu
ashe kana kullace dani kasa aka
yi mata wannan dukan ko? Ke
kuma principal kin goyi da
bayansu sun daki *yar mutane a
banza ko? To ni
sai na daukarwa Hannah fansa
da kaina. Ya kada kai ya fice
Sahabi ya juya ya kalli Principal
ya ce “Kinji kuma ta inda ya
lauya magana ko? Ta ce
“Kyaleshi bayan kai ma Mr. Ojo
ya fada mun cewa son Hannah
yake don haka kaci gaba da kula
da
su. Haisam ya nufi staff quaters
ya shiga gidansa ya
zauna a falon yana huci kamar
ya kashe kansa
yake ji saboda tsananin bakin
ciki yau ko darasi ba
zai je yayi ba. Yini yayi cur a gida
ya kudiri niyyar zai dauki fansa a
kan duk mai hannu a cikin
wannan
al’amarin, wai Sahabi ne zai yi
masa haka Sahabin
da ke zuwa har gida ya ce ya
taimakeshi ya shawo
masa kan Hannah taki kulashi
shine yau ya ce
shine yake son Hannah, wai
Juwairiyya da kanta
take cewa rashin kunya Hannah
tayi mata zata yi danbe da ita
wai shine tayi mata bulala uku,
ita
kuma principal da kanta take
bin bayansu bayan
tasan Hannah tasan halinta
tasha yin kwatance da
ita a assembly akan tafi kowa
da’a da ladabi shine
har ta yarda da kintsin da suka
yi mata ko da kyau,
haka Haisam ya dinga nanatawa
a zuciyarsa. Haisam bai fita daga
gida ba sai da yamma misalin
karfe biyar ya shigo cikin
makaranta a lokacin
dalibai suna prep din yamma ya
wuce kai tsaye
ajinsa don yaga jikin Hannah, a
zaune ya ganta a
kan kujerarta ba laifi jikin,
burdin bulalar ya dan
warware zazzabain ya sauka sai
dai bata iya bude idanuwanta
sosai.
Ya ce da ita. “Hannah ya jikin?
Cikin sanyi murya ta
ce “Da sauki, ya ce kinsha
magungunan naki? Ta ce
“Eh ina sha. Wani masinja ne ya
leko ajin ya ce
Malam Haisam ka zo inji
principal. A fusace Haisam
ya ce “Meye kuma? Dan aiken ya
ce “Waya aka bugo maka zaka
dauka a ofishinta, ya ce “Gani
nan
zuwa Haisam ya juya ya dubi
Rauda da Nusaiba ya
ce “Ku dinga kula da Hanna ku
tabbatar tana cin abinci, kunji
ko? Suka amsa da “To zamu kula
da
ita, sannan ya fita ajin ya nufi
ofishin principal yana
isa ofishin yayi sallama ya shiga
ya gaisheta a murtike. Ta ce
“Yayanka ne Habib yake son yayi
magana da kai nace ya sake kira
nan da minti biyar
za’a kira… Kafin ta rufe bakinta
wayar ta fara kara
Haisam yasa Hannu ya dauka ya
gaishe da Yaya
Habib yaji da kyar Habib yake
amsa wa rai a bace
Yaya Habib ya ce “Kai Haisam mu
fa ba yara bane kanana kana ji
ko? Saboda me zaka dinga
mana
wasa da hankali? Kace shekara
uku zaka yi a
makarantar nan sannan ka bari
yanzu shekara uku
sun cika, last week da ka zo aka
gaya maka cewar
ka bar teachin dinnan ka dawo
gida ga
kamfanonin Baba aiki yayi mana
yawa muna neman ma’aikata,
ka ce da zarar ka koma kafin
karshen watan nan zaka dawo
gida kabar koyarwa gashi munji
ka shiru. Kujerarka na nan na
jiranka ga Ramlah nan na
jiranka itama.
Har anyi bikina da Jidda har ta
haihu *yar mutane na zaman
jiranka kazo ayi bikinku. Wai
shin me ka zamar da mune, har
nawa kake da zaka dinga juya
mu? Don
haka karka sake nazo
makarantar nan da kaina ka
rubuta takardar barin aiki kabar
koyarwan nan ka
dawo gida muna nan muna
jiranka. Kai baka kishin dukiyar
Ubanka sai gwamnati me
gwamnati zata
baka da kake mata wannan
wahala, me kake nema ka samu
wanda a gidanku baza a baka
ba? Haisam ya fusata ya ce “Ka
gama maganarka? To bari in
fada maka gaskiya ba zan bar
koyarwa ba ina nan
bazan dawo gida ba, ya kifar da
kan waya ya fice,
principal ta bishi da kallo har ya
fice.
Cabdijan aradun Allah za’a
kwasheta da zafi,,, kar dai a ce
Haisam son Hannah yake.  Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]