[Advertisements⬇️]

Yar tallah5 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

*YAR TALLAH*

           CHAPTER5
*Mun tsaya inda inna laure*
*Tace to yar iska gama kallon nasa kixo ki amshi kudin don ko ubanki bai isa ya hana kiyi tuwonnan ba ballentana wani banza jaki can zakizo ki karba ko kuwa sai naxo Na miki dukan mutuwa*
Anan muka tsaya
*Zamu tashi a*
Rabiu ya turata alamar taje ta karba
Laure ta maka mata rankwashi akai wanda yasata fasa wata uwar qara sbd azaba
Ta wurga mata kudin tana fadin munafuka naga alamar watarana sai kin nemi kifi karfina a cikin gidannan
Dole saina gyara miki zama ta haureta da qafa
Zaki tashi ko sainaxo na casaki? Yar iska kawai lauyayyar banza kawai
Saude ta yinkura ta tashi gamida ficewa tana kuka
Rabiu ya rakata da idanu yana tausayin kansa rayuwarsu na bashi tausayi
A ganinshi babu yaran da suka taba samun kansu cikin halin kunci kaman yanda shi da qanwarsa ke ciki yanxu. Yace ya Allah gamu gareka
Laure ta wurga masa murfin kwano ya zabura gamida dawowa hayyacinsa yayi gaba yana tattara kwanukan
Laure tace daka barta ta tafi kaita tunani ai gwara ka bita can kuyita
Kwakwale kwakwalenku dan iskan banza da wofi kawai
Maganar ta soki rabiu yai saurin wuceta sbd yaddah maganar ta daki zuciyarsa matuqa ji yake kamar bata taba masa abinda ya qona masa zuciya irin na yau din ba
Saude ta dawo daga siyo iccen ta zauna ta hura wuta gamida daura ruwan tuwo a lokacin har ta fara sarewa da wahala a jikin murhun ta soma jinyar qafafuwanta ta samu daqar ta kammala tuwon da miyar kuka a bakin murhun taci nata ta miqe tayi alwala ta shige dan akurkin dakinsu domin jero sallolin da batayiba
Washegari aka tashi da azumi don haka saude ta samu sauqin wahalar sosai
Dukda aikace aikacen gidan da tayi itada yayanta bata wata sha wahala ba
Saida azahar inna laure tasata dauki markaden tiya uku aka kai markade aka markado shi ta sake daukoshi akai ji take tamkar wuyanta zai karye sbd nauyi
Data kawo markadenma qin sauke mata tayi ta barta dashi akai
Saude tasa kuka don Allah kiyi haquri ki saukemin inna kaina zai karye
Laure dake zaune tana kwadon zogale ta dubeta a harzuqe kin fara ko? Wato nabar kwadon zogalen naxo na sauke miki sbd inajin tsoronki ko?
Ta maida kai taci gaba da kwadonta tana fadin bankadaddiyar yarinya masifaffiya
Iklima dake kwance gefenta tace laure bani ruwa insha karya azuminnan zanyi bazan iya kai azuminnan ba
Laure tace a,a ko aike kikasa kanki tuntuni nake fadin ki ajiye ki ajiye kikaqi waike sai kinyi.
Ta miqe gamida dibo mata ruwan cikin randa mai sanyi ta kawo mata ta miqe tasha iya shanta tayi wurgi da modar
Laure tace a!a mai makon ki bani in mayar sai kiyi wurgi da ita
Iklima tayi tsaki ta janyo kwanon kwadon dake gabanta ta soma ci
Laure taja kwafa sannan ta miqe ta dauko modar ta mayar sai a lokacin ta nufi saude data dafe wuyanta da takeji tamkar zai karye
Laure tace shin zaki tace ko na tace? Donna lura wuyanki ya isa yanka
Saude ta wuce ta nufi rijiya sannan ta dibo ruwan ta taceshi tas tana
gamawa rabiu ya dawo daga markaden qosai
Da alamar shima a gajiye yake
Laure ta dubi saude maxa ki hadamin wuta ki hadamin kaskon suya ki hadamin murfi biyu dayan murhun kuma ki dora ruwan koko
Ba yaddah ta iya haka taci gaba da hada hadar hada wuta babu ko tausayawa
Laure ta soya kosai sannan ta sheqa koko cikin bokiti
Qarfe shida tace su dauka sukai makarantar malam hadi tasan almajirai zasu siya
Rabiu ya dauki kokon ita kuma
Saude ya dora mata kosan
Laure ta kwala musu kira suka dawo
Tace kuma ban yarda da ku daukarmin ko kayan sile ba kuje ku dawo kayan buda bakinku nanan zan ajiye muku suka amsa da to sannan suka fice
Cikin ikon allah kuwa suna zuwa ana kiran sallah
Alhaji bashir wani tsohon mai kudine a cikin layin yaxo zai shiga masallaci ya tsaya wurinsu ya zaro dari biyar ya miqawa rabiu yace ya kirga kosan da kokon ya bada sadaka,,,dadi ya cikasu shi kuma ya shige masallaci abinsa
Rabiu ya kirga kayan gaba daya na dari hudu da hamsinne
Yayima almajiran wurin sadaka da koko da qosan
Ana gama sallar alhajin ya fito rabiu ya fada masa ko kayan nawane yace tosu riqe canjin
Sannan yace musu kullun su rinqayin sadaka da koko da qosan zai rinqa biya
Ya zaro wata dari biyar din ya basu rabiu ya amsa cikin ladabi suka cika da murna
Alhaji bashir din yace kuma ku dinga diba kunaci kunji?suka amsa da to sannan ya wuce abinsa
Suma suka wuce gida rabiu ya canja kudin ya dauki canjin yankan da suka rage yaba laure sauran kudinta dadi ya cikata za,a ringa siyan kayana kenan kaga babu bandaro (kwantai) kenan ta dubi
Saude jeki maza ki dauko muku koko suka tsugunna a tsakiyar gidan tamkar almajirai sukasha sannan saude ta miqe ta dauko musu sanwar dimamen daya rage tun na sahur sukaci suka koshi duk da kuwa miyar kukar tayi tsami ta lalace amman a haka suka cinye tuwon tas. Gaskiane da hausawa sukace da babu gwara ba dadi
Sun gamaci suka tafi sallar asham a masallaci suna dawowa su duka suka kwanta a gajiye kamar matattu
Qarfe uku na dare laure ta tashesu wai su tashi susa sanwar tuwon saidawa na asuba
Saude tasa kuka saboda bacci da gajiya dake cinta
Laure ta haskata da cocila au kukama kika lallai yarnan bakida hankali maza ki taso  inanan ina jiranki? Ta qarasa kuka ta daura hannu aka tana fadin muhammadu dan Abdullahi
To malam zoka gani da idonka saude na zagina
Malam bala ya zaburo tamkar shayayye
Zagi kuma laure wani irin zagi ba dadin ji?ya hankade labulen dakin ke ba magana ake miki ba yar jakar ubannan shine kika zauna kinama mutane kuka
Idanda uwarkice ta dawo  ta sanyaki aikin ai bazakiyi kukanba ko?
Fitonan inji wanda kike zagi
Saude tahau rantse rantse abinka da yarinta kuma ta rikice sai fadi take wallahi baba karya take ban zageta ba na rantse da Allah ban zageta ba
Malam yace shin zaki fito ko saina shigo dakin?
Rabiu yace kayi haquri don Allah baba wallahi bata zageta ba
Malam yace au karya tayi mata kenan?
Ta zabura ta boye bayan rabiu tana kuka tana bashi haQuri amman bai sauraretaba yasa hannu ya fisgota daga bayan nasa ya jata a qasa kiyyyyyyyy
Har waje ya janyo igiyar guga ya shiga laftarta ta ko ina bugu bana hankali yake mataba  baya ko duban inda zai doka sai ihu take tana roqonsa
Rabiu ya duqar da kansa qasa baya ko iya motsi hawayene kawai masu zafi dake diga daga idanunsa
Saida yayi mata dukan bala,i ya farfasa mata jiki sannan kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo ruwa cikin gugar ya sheqa mata ta sauke nannauyen numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon siyarwan don lokacin sahur ya gabato

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hmmm su malam bala manya
Mu tara gobe daidai wannan lokacin  donjin ci gaban book din tareda.        Niii
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]