Yar tallah29

           *YAR TALLA-      BOOK4*

                *CHAPTER29*

ZUciyar Saudat ta shiga duniyar tunani da sake-sake ganin al’amuran take
tamkar a cikin mafarkinta suke faruwa, kuma har yanzu bata fidda rai da zata farka a kowane ba Minti sha biyar ya kawo su har kofar gidan Malam Bala, inda Saude ke nuna masa hanya har suka iso, ya faka motarsa a qofar tsohon gidan.
Dukkansu suka fito suka nufi gidan, Saudat na rike da hannun Nabila, Shukura na gefenta, sai Nabil a gefen Momy, Alhaji Ashiru ya zauna ya jira su a mota.
Sallamar da suke ce ta janyo hankalin Inna Laure dake quryardaki tana tattara komatsai, tayo tsakar ‘gidan tana fadar, “Marabanku; sannunku da…”
Turus taja ta tsaya tare da dafe qirji cikin tsananin tashin hankali da kyarmar murya ta soma fadar. “Su waye ku, daga ina?”
Momy ta gyara tsayuwa kafin tace “Ikon Allah abin da mamaki, idan ni baki gane niba, ai ina tunanin wannan ‘yarki ce kya gane ta?”
Tayi maganar tana nuna Saudat.
Inna Laure ta fadi qasa jaBar kamar an tile kayan wanki tana kwalla wa Malam Bala kira, dukkansu sukayi tsaye suna kallonta.
Malam Bala ya fito daga kewaye a gigice, hannunsa rike da buta yana fadar. “Kai Laure wannan irin ihu haka ai saiki sa juwa ta kwashe ni in fadi ba gaira ba dalili”.
Inna Laure ta rinka nuna masa inda Momy take tana fadar. “Malam duba min ka gani, wace ce wannan Kamar Mariya”. ?
Malam Bala ya saki  butar ta fadi wanchakal ya nufo inda suke yana fadar, “Wacce Mariyar ki ke nufi?”
Yana qarasowa inda suke yaja ya tsaya, suna kallon-kallo shi da Momy, alamun firgici da kaduwa sun bayyana cikin idanunsa.
Dr. Mariya tayi mmmushi kafin tace “Kallona da kake tamkar wadda ta fado daga sama, na san ba :zai rasa nasaba da ganin ba-zatar da nayi maka ba a lokacin da daga kai har matarka ku ka saki jiki da na bar muku duniyar shi yasa. kuka wofintar da rayuwar bayin Allah, kuka gallazamusu, kuka cuta musu don kawai ba su da kowa, amma me yasa ku ka manta cewa, duk abin da kuke Ubangiji na nan Yana kallonku, kuma duk daren dadewa sai ya saka wa mai haqqi hakkinsa,
musamman ma bayin Allah wadanda basu da alhakin kowa?‘
Kuka cuta musu, kuka gallaza musu kuka tozarta rayuwarsu daga qarshe ma kuka tarwatsa ” . minsu kowa ya kama gabansa don kawai ka tsani
, uawarsu a kan Iaifin da bata jiba bata gani ba; wannan shi ne sakamakon soyayyar da Kaunar da na maka? Lallai da haka shi ne ‘sakamakon . soyayya to da ba tayi rana ba,
Sai dai da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai idan shi bawan ya zalunci’ kansa, sai ‘ga shi bai bar rayuwata ta tozarta ba kamar yadda kai kaso, Ya daga daraja ta a duniya, Ya kuma cika min burina tahanyar azurtanida ilimida nagartaccen miji Wanda ya fika komai a rayuwa, Ya kuma sake bani wasu ‘ya’yan, sannan daga karshe Ya hada ni da ‘yata gudan jinina, tabbas babu abin da zance da Ubangiji sai godiya. . ’ ‘
Abu daya ya kawo ni wurinkn shi ne ka sanar dani inda dana yake in kuma ba haka ba wallahi sai na zauna kotu da kai, don sai ka bani‘dana, cutarwar da kayi musu kuma wannan kai da Allah, Shi zai yi hisabi a tsakaninku,
-don haka ka sanar dani inda dana yake
. Tsananin firgici da kaduwa su suka girgiza ‘ zuciyar Malam Bala ‘ har ya ji qafafuwansa na Kokarin gaza daukarsa; ya matsa jikin bango’ya  jingina’yana faman maida numfashi a wahalce”
Laure dake durqushe a kasa ta zabura ta mike tsaye cike da qarfin zuciya ta cire kallabin kanta taci damara kamar irin‘sabbin mahaukatan nan ta soma magana tana tafa hannaye“Kam babban abin da malam ya hana, mu zaki gwada wa qaryar arziki tsohuwar karuwa, kin je kin yo hayar kaya shi ne zaki zoki mana bariki? To qarya ki ke, wallahi idan kin fasa zuwa kotun kin raina Allahn daya halicce ki, ke wanda ma ya baki hakuri Allah ya tsine masa, mu din nan sai dai muga bayanku ba dai ku kuga bayanmu ba
. Dr. Mariya ‘ta yi wani qasaitaccen murmushi, ta cire gilashin da ke manne a fuskarta tana kallon Laure kafin ta ce, ‘Ai ita da ma . tabarmar kunya da hauka a ke nade ta, don haka
ban kuma kasa dake ba ballantana har ki kwasa”.
Ta juya kan Malam Bala ta ci gaba da fadar, “Zan tafi Malam, na ba ka nan da sati guda ka nemo min inda dana yake kafin in dauki mataki, ga kuma Saude a hannuna Allah ya jefo min daga sama don haka na rungumi abuna, zan dawo rana irin ta yau don karbar dana, na barku lafiya”.
Inna Laure ta yi caraf ta damke hannun Saude tana fadar, “Wallahi babu inda za kije da ita, nan zaki barta a gidan ubanta, don mijinta yazo yace shi bai sake ta ba, dole kuma’ta koma gidan mijinta Yanzu-Yanzun nan”.
Ido waje Saude ke kallonta’ gabanta na. Faman bugawa da sauri da sauri, Momy kuwa dariya tayi cikin ajikafin tace “Kadadai ace shirme da‘ jahilcin’ naki har ya fara taba kwakwalwarki? Ai k0 shi uban da ya haifi Saude bai isa ya hana in tafi da ita ba ballantana  karabiti”. Kamarki ba
Inna Laure ta Kara hayayyakowa tare dA cukwikwiyo rigar Sauden
Malam Bala yace “Sake ta su tafi” .
Ta juya tana kallonsa a kidime tana fadar “Wallahi babu inda za ta Malam,Dan duk garinnan
banga ubandaya isa yasa ta tafi da ita ba ,Nace ki sake ta k0?” Malam Bala ya fadi a harzuke fuskarsa dauke da tsananin bacin ran da bata taba ganin irinsa ba a tare dashi A dole ta saketa din zuciyarta na barazanar tarwatsewa ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji sanyi, kawai sai ta durkushe a Kasa ta rusa wani irin kuka mai tada hankali.
~ ‘ Momy da Shukura suka tasa Saude a gaba ‘suka fice batareda sunsake bitakantaba. Suna ficewa daga gidan Malam Bala yaja yan qafafuwansa ya nufi: hanyar dakinsa, bai ko kula: Laure ba, abin daya qara firgitata ke nan
Ta Kara .kidimewa zuciyarta cike da firgicin tonon asirinta.
Suna fitowa daga gidan suka shiga mota, Alhaji Ashiru ya ce, “Wai har kunyi me?”
“Momy ta ce, “Mu tafi kawai Alhaji”.
Ya dan waro ido kafin yace “Amma na zata za ku yimin magana da shi ko da fitowa ce ya yi mu gaisa, k0 baku samu mahaifin nata bane?”
Momy ta kwantar da kanta a kan makarin kujerar kafin tace “Manta da su kawai‘Alhaji, muje ai sai da mutunci ake zumunci”.
Bai ce komai ba ya yi wa motar key, Momy tace, “Saudat ta nuna musu gidan iyayen Hamid. Saudat ta’amsa da to jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da kasala.
A Kofar gidan su Hamid maigadi ya sanar musu iyayen nasa sun yi tafiya zuwa Zaria, sai dai Hamid din shi kadai, Momy tace yayi musu magana da shi. Maigadin ya juya ya nufi cikin gidan, bai jima ba ya dawo ya sanar da su yana zuwa. Suna nan zaune cikin mota daga’ gate din gidan, yana sanye da wani farin yadi mai sheki ya daura wa wuyan hannunsa wata tsadaddiyar agogo baka, mai kyan gaske ya dora farin gilashi saman dogon hancinsa da makullin mota a hannunsa, da
alama fita zai yi. Kai tsaye wurin motar tasu ya nufo idonsa a kan Momy tun kafin ya ida Karasowa
‘  yana isowa ya rusuna  ya gaida Daddy, sannan ya gaishe ta yana fadin, “Doctar kece a gidanmu?” ~ ‘Dr Mariya ta fadada fara’arta kafin ta ce “Aiko nice da kaina Malam Hamid, ai dole ne inzo ko dan qaunar daka nuna wa Saudat ya zame min wajibi inzo in yi maka godiya, kuma in maka albishir da cewa Saudat yata ce nice mahaifiyarta  nina haife ta da cikina”  Hamid ya waro idanuwa waje yana fadar, “Yarki kuma DR? Kina nufin dama kece mahaifiyarta‘?” , Momy ta amsa da, “Tabbas nina haife ta da dan uwanta Rabi u”. ~ Wani irin dukulallen farin cikine ya daki zuciyar Hamid. ya daga hannunsa sama yanA yiwa  Allah godiya. Saudat kuwa kallonsa kawai take a . zuciyarta tana jinjina ma soyayyar da bawannan »ke mata ‘ ‘ Momy“ tace “Za mu tafi Malam Hamid, da fatan zumunci mai Karfi? zai shiga tsakaninmu” « Hamid ya amsa da “insha ,Allah”‘ Amma idansa na kan Saudat wadda ke ta faman haske shi
‘ da lallausan murmushi “ Yace “Mamy ki bani adireshinku insha Allahu dana dawo  daga tafiya zanzo
Babu musu Momy ta bashi dan qaramin card din da ke cikin jakarta wanda ke dauke da adireshin gidan da lambar gidan, sannan Dady yaja motar suka tafi Saudat na daga masa hannu har suka Bace wa ganinsa. Wani irin abu ya caki zuciyar Hamid, ya sa dan yatsansa ya lakace ‘yar guntuwar kwallar data taso masa, shi dai ya sani Allah ya jarabce shi da soyayyar Saudat, irin son da
ba zai iya misaltuwa ba, wai yau Saudat dinsa ce ta zama haka? Rayuwa kenan.
Ana kiran sallar azahar suka iso gida, don haka Alhaji Ashiru na sauke su ya wuce masallaci don ya bada farali, su kuma suka shige gidan, Momy ta wuce bangarenta su ma suka nufi nasu Bangaren don gabatar da sallah a cikin lokaci.
Bayan sallar la’ asar kuma Shukura ta koma gida saboda gobe tana da lecture a school.
Kwanansu uku da dawowa ya kama ranar alhamis, Saudat na kwance a falonta ita da Nabil da Nabila tana kallonsu suna home work da aka basu daga makaranta, Momy ta shigo falon kafadarta na rataye da katuwar jaka, ‘sai rigar likitoci sagale a dayan hannun da alama dawowarta daga ofis ke nan. Duka yaran suka zabura suka nufe ta a guje
suna fadar, “Oyoyo Momy, welcome”.
Ita ma da fara‘a a kan fuskarta ta rungume yaran a jikinta tana shafar kawunnansu.
Saudat ta yunkura ta mike ta nufi inda ” ‘ Momy take ta karbi jakar hannunta da lafkwat dinta: ‘da mayafin jikinta ta nufi bangarenta kai tsaye kicin ta nufa ta jero kulolin‘ .abinci a  babban faranti tareda kwalin lemo’, da ruwa masu sanyi ta nufo falon, inda ta samu’ . Momy har tayi wa kanta masauki saman tallausan ‘ kafet din falon, yaran duk sun zagaye ta suna ta_ shirmensu. ‘
Saudat ta ajiye mata kayan abincin a gabanta, ta soma bude  kulolin tana mata sannu da zuwa. Momy ta rike farantin tana fadar.
“Barshi kawai Saudat, kije falon waje
Hamid nanan ya zo zaku gaisa” . . Saudat ta washe baki tana fadar. ‘ ~ “Kai Momy, ashe bai mance dani ba, yau fa kwana uku . ke nan da dawowarmu daga -Dandagora, amma bai zoba shi da yace ‘a * washegari zai zo?”
Momy tace “Ah to, ni kaina da na ganshi a yanzu sai da nayi mita, amma dai yace ba ya garine shi yasa, dawowarsa kenan. Tashi kije kar yaga an barshi shi kadai.
_ ‘ Saudat ta yunkura ta mike ta nufi kan gadonta ta jawa farin mayafinta ta yafa, ta saka takalminta flat Shoe shima fari
A tsaye ta same shi cikin falon ya nannade hannayensa a qirji ya zuba wa qaton hoton da ke jingine a bangon daki ido, nasu Nabila da Nabil ne wanda .aka yi musu a harabar wurin shakatawa da
ke cikin park dukkansu sun yi matukar kyau tamkar ‘ya’yan da ke rayuwa cikin dusar qankara.
Saudat ta qaraso cikin falon da ‘yar siririyan sallamarta, bakinta na dauke da murmushi. Hamid yayi saurin waigowa yana kallon mai shigowarr tare da amsa mata sallamar  Saudat ta tsaya dan nesa da shi tana fadar, “Saudatu ya tabbata kan Yaya Hamid wanda ya manta da ita tsawon kwanaki uku babu shi babu alamarsa”. .
Tunda Hamid ya waigo ya ganta ya kasa koda kyafta idanunsa balle ya janye su daga kanta, girman da Saudat ta Kara da cikar jikinta shi yafi . komai daukar hankalinsa, da kuma shigar alfarmar dake jikinta. Ba komai bane a jikinta, illa wani tsadadden code lace dark blue mai ratsin fari-fari a jiki, dinkin riga da siket, kalar leshin ta dace da yanayin farar fatarta, don haka dinkin yayi matukar kwantawa a jikinta.mayafin da ta yi
Ya zauna kafadarta ya dace da ita, ya fito da sigarta ta nutsattsiyar budurwa.
: Hamid ya lumshe idanunsa ya bude guda yana fadar, “Allah ya huci zuciyar Saudat, wai kinga yadda kika koma kuwa?’ ‘
‘ ‘ Saudat tayi murmushi har da sunkuyawa ta
zauna tana fuskantar katon teburin da aka qawata
da kayan ciye-ciye dana sanyaya makoshi. ~ ~
“ ‘ ‘ Hamid ya durqusa a gabanta yana kallonta
da idanunsa dake fallasa asirin zuciyarsa, ya kira
sunanta .
“Saudat, wallahi ina sonki, irin son da ba zai . misaltu ba, daidai da daqika guda ban taBa ‘ mancewa da keba a rayuwata, kina nan makale a zuciyata wallahi ranar da kuka zo gidanmu a ranar na bar Katsina na tafi Abuja, isowa ta ke nan wallahi. Saudat zuciyata ta gaza hakuri saida nazo  ki yarda da ni don Allah kyakkyawata”.
Dariya ceta kwace wa Saudat saboda ganin yadda duk Hamid din ya bi ya rude kamar wani zautaccce, shi ma ‘yar dariyar yayi yana sosa qeya alamar ya danji kunya shi ma.
A daidai nan ne kuma Dr. Ahmad ya sawo kai cikin falon da‘ yar siririyar sallamarsa, waddai ta makale amakoshi.
Saudat ta dago kanta a dan razane ta dubi ‘ inda ya watso mata Wani razanannen kallo ta cikin siririn farin gilashin dake manne a fuskarsa,
Lokaci guda ya dauke kansa tamkar Allah bai ajiye ’su
Awajen ba, haka ya gifta su ya shige falon cikin gidan.
Saudat ta sauke wani gwauron numfashi tare da maida hankalinta inda Hamid yake
Murmushi ya sakar mata tareda fadar, . “Wannan shine abokin takarar tawa kenan?”
Saudat ta sunkuyar da idanunta qasa tana dan wasa da bakin gyalenta don har ga Allah Hamid yana da muhimmanci a rayuwarta, duk da ta sani sarai ba zata iya hada soyayyar Dr. Ahmad da ta kowa a zuciyarta ba.
Hamid ya yunkura ya mike hannayensa zube a cikin aljihunsa yana kallonta da fararen
idanunsa.
Saudat tayi qasa da idanunta ta kasa hada ido da Hamid din sai kawai  ta tsinci kanta da jin matukar nauyinsa.
Hamid yayi wani malalacin murmushi
Wanda ya tsaya iya labbansa kawai, muryarsa na dan sarqewa yace “Tsananin son da nake miki Saudat, da dumbin qaunarki dake zuciyata ba zai ingiza ni ga take gaskiya ba. Saudat nayi miki rantsuwa da Allah ke ce kadai macen da na taba so a rayuwata, kuma haryau bana tunanin da akwai kwatankwacinki. A ranar da kuka zo gidanmu kuka ganni a ranar aka daura aurena da Kausar ‘yar qanin mahaifina
‘Amma nasa qafa na bar Katsina zuwa Abuja‘ ban“ sonta, banida muhallin da zan iya
:ajiyeta a zuciyata, tunda na. tafi sai jiya na dawo. A yanzu haka mahaifina yayi fushi ,dani , don haka mahaifiyata ta bani shawarar na tafi Kaduna Wurin matata, wannan ne ‘ kadai abin dazai Shirya tsakanina da mahaifina. Yanxu’ haka tafiyar tawa ce zuwa Kadunan shine na kasa daurewa har sai na tsaya na ganki sannan na wuce. Saudat ba zan shiga haqqinki ba, idar har kinji zaki iya aurena a yadda nake a ‘ yanxu na baki sati daya kiyi shawara duk abin da ‘ kika ”yanke zan dawo sai ki sanar dani”.
“’ Ba tareda ya tsaya sauraran abin da zata ceba ya zaro ambulan daga cikin aljihunsa ya dora mata a hannu sannan , ya juya ya fice abinsa.  Saudat  ta mike jikinta a kasale ta ‘ nufi qofar shiga babban falon gidan. Bata ankara ba sai dai ta ji sunyi karo yana qokarin fitowa ita tana qokarin shiga, tayi saurin ja da baya tare da dafe  goshi, kallo daya yayi mata ya Juya ya dauke kai  da sauri ya raBa ta zai wuce. . Saudat tayi saurin rufa masa baya tana ‘ kiransa baida alamar  tsayawa balle harya .sauraré ta hakan ya sata Kara da gudu~gudu ta , sha .gabansa.
‘Don Allah ka tsaya ka saurareni
Ta yi magar tamkar zata rusheda kuka.  Dr. Ahmad ya tsaya a gabanta yasa hannayensa a aljihu tare da kafa mata ido. Saude ta langwabar da kai ‘ “Don Allah kar ka horar dani da fushinka, wallahi ba zan iya jurewa ba” . . Dr Ahmad ya watsa mata harara kafin  yace“Idan harni ban horar da zuciyarki da fushina ba, ai ke kya tarwatsa tawa zuciyar da masifar kishinki kauce ki bani hanya in wuce : Ya qarasa maganar tare dasa hannu yana ture ta daga gabansa
Saudat ta Kara tokare hanyar cikin muryar ‘ son fashewa da kuka ta ce “Haba don Allah yallaBai, Yaya Hamid nefa ba wani ba”.
Dr. Ahmad ya qara watsa mata. wani kallo, “Okey, Yaya Hamid ne shi da yake ba namiji baneba  k0? K0 kuma shi din ba sonki yake ba ko? Da Allah matsa bani wuri malama na wuce”.
Wani irin qululu ya tokare zuciyarta ganin yadda take rarrashinsa yana qara botsarewa.yasa ta  juya da hanzarinta tana sharar kwalla ta shiga ciki.
Dr Ahmad yabita da idanunsa dukda ‘ zafin da zuciyarsa keyi bai hana shi jin tausayinta ba, sai dai shi kansa bai san kalar zuciyar shiba da kishi yakan sa ya kasa sarrafa kansa ba yadda ya
‘ iya haka ya juya ya fice daga falon

Hmmm
Naku har kullum
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

About AIS

Check Also

Yar tallah32

           *YAR.    TALLAH*                *CHAPTER32* Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana tirje~tirje da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *