Yar tallah25

                 YAR.     TALLA👼

                  CHAPTER2⃣5⃣
Tace
Na saki qafa don karya fito ma ya ’hango ni na san halinsa sarai, bai da kirki don bacin yan kirkin na kansa na san da da bugu zai maida ni gida, na saki qafa na zagayo ta’ bayan gidanmu tun daga nesa na hango Bala zaune saman wani dan kututturen ice yana jirana Na karaso da sallamata tare da’ gaishe shi, ya mike tsaye yana amsa min da fara’a a ‘fuskarsa ya bani wurin da’ yake na zauna shi kuma ya tsaya daga tsaye yana fadar. ‘
“Sannunki da zuwa mai kyau, dama ’ .zuciyata ta bani kina hanya”.  Nayi murmushi kawai ba tare dana
tanka masa ba Bala yace, “A gaskiya Mariya abin da
yasa nace kizi nan saboda mu tattauna wata magana ne, kin ga dai kunyi jarabawa, result
kawai kuke jira yanzu kin kammala firamare dinki ya kamata a zo a tsayar da maganar“ auremnu haka nan, ni dai na fara gajiya, , mahaifina har yamin maganar auren da kansa, : . tunda bakin gwargwado dai kin san inada sana,a kuma zan iya, rike ki da ita ke bama keba,
ko’ mata. hudu zan iya riKeWa don haka banga amfanin zaman haka ba, k0 ya kika ce?” . Na danyi jim ina dan nazari, ni kaina zan so auren fiye da zama haka duk da ban san meye qunshe a cikin auren ba, amma ina
sonsa musamman da masoyina Bala. Na dago a hankali ba tare dana bari
mun yi ido hudu ba na soma magana.
“To amma ai kasan Yaya Sani ya fada maka karatu zanyi, kuma duka gidanmu so suke ma idan na gama sakandire in wuce makarantar asibiti”
Bala ya katse ni ta hanyar fadar, “Assha! Assha Haba Mariya da hankalinki’ yanzu saiki barikinaji kinagani aturaki wani karatu to idan kin gama karatun saiwa ya aure ki? Kin san dai yadda masu karatun nan  ke tsufa basa samun masu aurensuba sai tsaffin, Alhazawa. Gaskiya kiyi tunani da kyau Mariya,don yadda ki keda kyan nan da siga , ‘ kyanki aure kawai, amma Wallahi idan aka tura ki karatu an kashe ki, kuma an wargaza ” miki rayuwa”.
‘ Ni dai nayi sukuti ina saurarensa bayaninsa na shigata ta ko’ ina, ban ankara ba
sai dai naji saukar kara a jikina, na zabura na zabga ihu. Yaya Sani ya cukwikwuyo gyale na
kamar wata Akuya ya shiga zabgata da karan a
hannunsa ina ihu har sai daya karkarye a jikina. Bala ya‘ rude ya shiga riqe shi yana magiya, Yaya Sani ya dago a fusace, “Sakar ni mutumin banza idan ka sake rike ni wallahi za kaga abin da zai faru, munafuki, maciyi amana, yanzu ashe har zaka iya taimaka wa wurin lalata tarbiyyar qanwata? To Allah ya isa amma ka sani babu ni babu kai har abada, kuma wallahi idan na Kara ganinka da ita hukuma ce zata raba mu. Ke kuma muje gidan zakici ubanki yau”.
Ya jani kamar wata Akuya yana duka tun saman hanya har muka iso gida.
Ya wurga ni gaban Umma, ta zabura ta rike ni da hanzarinta tana fadar, “Meye haka kai kuma ka keyi, baka da hankali ne?” . ’
Yaya Sani ya soma magana cikin tsananin Bacin rai, “Umma yarinyar nan Sai kinsa mata ido, lalacewa zata yi wallahi, Umma yanzu wai har ta san ta shirya taje su hadu dasaurayi ta debi gyale ta same shi don tana‘ yar iskar yarinya?”
_ ” Umma ta dauki sallallami cike da firgici  tace “A,ina ka gansu dan nan?” ‘
‘ ’“a bayan gida na gansu ita da Bala dan gidan Malam Nata’ala mai tumaki, tana zaune suna zace”
. “Yau na shiga uku ni Binta, yanzu abin ‘_fada kike son kija mana ne a gari Mariya? Ina ‘ganinki sumi-sumi ashe kin iya munafurci . ’ Tasa kafata haureni, “Matsakibani. wuri munafuka. Da kayi mata dukan mutuwa  inji uban daya aike ta wurinsa, kuma Babanku na dawowa kamar bisa kunnensa akayi, sai naga ta iskanci” .
‘ Haka Umma tasa Yaya Sani yayi min jan bugu kamar zai kashe ni, tana kallo ta sa masa ido, sai dai saukina guda ba a fada wa Baba ba, don nasan idan shine wataqila sai ya nakasani,amma dukda haka na bugu.  gashi Umma ta. juya. ‘ min baya, ba ruwanta dani, bata kula ni, bata tankamin dan idan natanka matama bata‘
Amsawa, ta cire sanya ni aiki, hatta girki ta daina sani na shiga tashin hankali, , fushin Ummata  ya qara jefani cikin damuwa
amma dukda haka banmantada Balaba a zuciyata har, kullum burina in fita . in ganshi, amma abin yaci tura, an daina aikena,. ’makarantar allon ma ba a barina zuwa, ga shi makarantar bokon babu‘ muna jiran sakamako
‘Kwatsam ranar asabar ina kwance a daki da yamma, Ummana ta dago labule, “Ke tashi ki shirya ki tafi makarantar allo”.
‘ Tana rufe bakinta ta saki labulen tayi
gaba abinta.
Wani dadi ya kama ni, na buga wani  uban tsalle ‘yau zanga masoyina, na nufi Kuryar daki na dauko hijabina da alkur’ani mai ‘girma, na zura takalmina nayi gaba “‘Amma abin haushin ban ga Bala ba wurin daWowa ma har ta qofar gidansu na biyo, amma ban ganshi ba Haka na dawo gida raina a Bace, ina ‘ “ dawowa kuma na iske wani bakin labari, Yaya Sani ya sama min makarantar kwana. Hankalina yayi maSifar tashi don kuwa yanzu na cire zuciyata da karatu, aure kawai nake so, na shige daki kamar maitakaba inaji anata lissafin abubuwan da za a siya min, ni dai jinsu
kawai nake,amma nasan saidai akai waniba dai Mariya ba.
Da daddare na kasa haquri ji nake kamar zuciyata zata tarwatse, da kyar na samu bacci ya dauke ni. Abin haushi kuma bamu daina haduwa da Bala ba, sai dai abu kamar wasa naga an fara yi min siye-siye katan din indomie, kwalayen madara, gwangwanayen ldii, complex, busasshen dambu da na fura da garin
‘ rogo, tuwon ruwa da sauran dai abinci ‘Ni dai kallonsu kawai nake ban san abin da ake ciki ba, sai da naji rade-rade cikin satin nan za a kaini makaranta, ai k0 kamar na taka rawar hauka don ranar da kaina na shirya da daddare najé har gidan su Bala na aika yaro ya kira min shi, nayi sa’a kuwa yana nan. Ya fito da zumudinsa yana fadar, “Dama yanzu nake shirin na fito duk ma yadda za a yi mu hadu daké mu hadu”. , . Na gyara tsayuwata ina kallonsa, murya ‘ ta a raunane na soma magana,‘ “Ka san ina
cikin matsala Yaya Sani makaranta zai kai ni bodin wallahi ’ ‘
Ya tsaya da sauri yana kallona hankalinsa a tashe kafin yace kuma Mariya, ke kuma sai kika ce yaya?”
Nace, “Ni dai wallahi banso, amma ban kai ga fadawa kowa ba”.
Bala ya danja numfashi kafin yace “Ai wannan wauta ce Mariya, inda kina son kasancewarmu a tare sai ki cire kunya da tsoro ki’fito fili ki fadi abin dake zuciyarki, na san dai babu mai izawa a saki wannan karatun sai Yaya Sani duk shine keda abin, kuma shike iza Umma, amma nasan ai Baba ba zaiqi goya miki baya ba”.
Na dan yi jim ina saurarensa, ina juya maganganunsa a zuciyata, can na hango Yaya Sani da wasu abokansa sun nufo inda muke. _ Tun kafin na ida tunanin abin yi naga Lawwali abokin Yaya Sani ya kwaso da gudu da qafa ya kwashe Bala ya fadi qasa.
Ai ban san lokacin dana kwasa da gudu ba, Yaya Sani ya kwaso ya biyo ni muka yi gida, ina shiga soro nayi karo da Baba yana ‘ shirin fitowa, ya rirrike ni yana fadar, “Ku tsaya, kyale ta karka sake ka buge ta, ai shi kangararren yaro duka ba ya shiryar da shi sai
dai addu’a, inda kun sanar dani wannan labarin tun wuri da ba a kai haka ba, kyale ta kawai. Wuce ki shiga ciki”.
Ya sake ni na shige gida.
Kai tsaye na wuce zan shiga dakin Ummata ta tsaida ni, “Tsaya karki sake ki shigar min daki, ki zauna nan don ban hada shirgina da karyar maza zauna nan”.
Sunan da Umma ta kira ni dashi yafi komai tarwatsa min zuciya, naja na tsaya jikin bango ina mazurai.
Yaya Sani ya shigo yana kallona, kallo mai cike da tsana, yaja tsaki.
‘ “Kin dai ji haushi, sakarya jakkar yarinya wadda bata san abin data keba. Wallahi ji nake na tsane ki, kuma idan har baki sauya hali ba, ba zamu taBa shiryawa ba, kin kuma daura aure da wahala wallahi”.
Umma taja tsaki kafin tace, “Hmmn! In dai maza ne ai gata nan gasu nan, wallahi in dai a karatun maza ne yarinya zasu biya miki iya yadda kanki zai iya dauka, karka so ka tona zuciya ta kaji yadda take zogi da har ban son in waiwayo in kalli yarinyar nan, duk ki rasa ma yaron da zai hure miki kunne sai
Bala? Dana can ni yaron bai kwanta min  ba, na tsane shi ban sonshi wallahi”.
Yaya Sani yace, “Ai shi kenan yau sai ya gane kurensa, don Lawwali a yau sai ya nakasa shi”.
Yana fadar nakasa naji tamkar ya soka min mashi a Kahon zuciya, ai ban san lokacin
dana fasa wani ihuba na durqushe a gurin na hau birgima. Ran Yaya Sani yayi masifar Baci yayo kaina da itacensa ya fara dukana.
Wallahi Saudat ban san lokacin da bakina ya bude na hau surfa masa zagi ba, kira nake,’ “Allah ya isa wallahi ban yafeba, ai dama na san baka qaunata, kuma karatun banyi, tattara kayana zan yi wallahi in bishi”.
Mamaki da takaici su suka hadu suka sa Yaya Sani ya tsaya da dukana yana kallona inda Umma ta hau sallallami harda kukanta tana fadar, “Yanzu Mariya saboda wannan dan iskan kike bude baki kina zagin dan uwanki haka? Yau na shiga uku ni Binta, Mariya idan baki kwashe kayanki kin bi yaron nan ba kin raina Allahn daya halicce ki, ki tafi kibi shi, ni dai in har ina raye baki isa ki auri yaron nan ba
Idan kikaga kin aureshi saidai in bana numfashi,mutuka yarinya” ., ’
‘ Saudat abu wasa-wasa har dare ya tsala sosai sannan mahaifina ya dawo,naji yana fadiwa wa Umma wai wurin mahaifin Bala yaje ya samu bayanan.
, Umma tace, “To idan ka same shi me zaka ce masa Malam.”
Yace, ,“Babu ruwanki, na riga na gama yanke hukunci, kibar ni kawai”.
Umma tace “Tona  barka Malam”.
Haushi ya kama ni banji hukuncin da Baba ya yanke ba, amma na kwana da shirin ,gari na wayewa zan tattara kayana in bar gidan, a wautata  amma da hauka irin ta zuciyar data kamu daso.
Kiran sallar farko Saudat a kan kunena akayishi ba wani bacci nayi ba,gyangyadi ne kawai, na lallaBa na tashi na dauko biro da takarda na rubuta wa Bala wasika zan tafi garin “ Kano ta dabo tumbin giwa yaro k0 dame ka zo an fika zan sauka tasha in zauna in jira shi na gama rubutun na’ lunke takarda na lallaBa na shiga. dakin Umma» can _ cikin; quryarta don a lokacin ita tana dakin Baba, na
dauko buhun kayana na Ciro kudin da Bala ke bani na Kirga naira dubu biyar ce wadda a lokacin ta kai darajar dubu hamsin a yanzu. Dadi ya kashe ni na dauki hijabina na saka na rage kayan cikin buhuna don in iya dauka, sannan na kinkima na fito, babu wanda ya ganni har zauren gidan, danayi sararaf na
.zare na bude na fice abina. Garin tsit sai mutane jefi-jefi, sauqin abin ma hasken asuba ya fara na kwasa da qafa har bakin titi, na tsaida mashin ledis na hau na tafi tasha na kuwayi sa’a  na samu mota ta kusa cika, sai dai abin takaici, ina qokarin shiga motar naji ana kwallo min kira, na waigo inga mai kiran nawa, Kawu Ummaru ne shaf na manta da yana zuwa tasha saida Kuli-kuli.
Naji tamkar in zunduma da gudu ya Karaso yana fadar, “Ina. zuwa_ da wannan kinkimeman buhun haka naga kina qoqarin shiga motar Kano?”
‘ Kin san marar gaskiya k0 cikin ruwa sai . yayi gumi  ga shi dama ni can ba ma’abociyar
Karya bace ban ma iya taba, nayi tsuru-tsuru ina muzurai.
Sai naga ya kamo hannuna yana fadar, “Wuce muje gidan, mu tafi maza”.
Na turje nasa masa kuka, hankalin kawu ya tashi ya tsaya yana kallona kafin yace -“Lafiyarki kuwa?”
‘ Da wautata na sanar dashi gudu zanyi don anKi aurar min da Bala, kinji wauta‘ fa
wai ni duk a sona na son ya barni in shiga’ mota in tafi, naji karan motar na. fadar, “Kano
saura daya! Kano saura daya! !”

*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
Mu hadu tomorrow daidai wannan lokacin

About AIS

Check Also

Yar tallah32

           *YAR.    TALLAH*                *CHAPTER32* Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana tirje~tirje da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *