Yar tallah22

           *YAR TALLA~BOOK3*

                *CHAPTER22*

Saude ta sulale qasa tana wani
gunji kuka mai kama da. gurnani ji ta ke numfashinta na  sama‘sama
kamar zai dauke, ta rushe da Wani irin kuka mai daga hankali, ta zabura tayo waje tamkar marar hankali ta tSallake mutanen dake waje da gudunta. Tana jin mahaifinta na Kwalla
mara kira, amma ba ta tsaya ba Dr wanda ya gaji da zama a motar ya fito ya jingina da motar yana lallatsa wayarsa ya ganta ta fito a guje,hankalinsa yayi ‘ masifar tashi ya nufe ta yana KoKarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani irin gunjin kuka. Dr ya rikice cikin tsananin rudani ya rike ta yana fadar, “Me ya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne? ki fada min.”  Saude ta Kara rushewa da wani kukan ba ‘ tare data :saurara ba ta shiga qokarin fadar, “Na mutu… .“ , na lalace. yallaBai * an daura min aure da Garba . “Innalillahi wa” inna ilaihi raji ’”un Abin‘
da Dr Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa kansa saman motar gabadaya
ya ma rasa a wace duniya yake
Malam bala ya qaraso da hazarinsa yana fadar keko wannan diya Allah ya wadaran halinki yanxu saboda dibar albarka shine zaki kwaso a guje kina ihu kamar wata tabin iska shin ba,a gaya miki yanxu muryarki al,aura baceba iyee?
Sauce najin abinda ya fada ta sake rushewa da kuka tana fadar wayyo Allah na shiga uku na lalace malam bala ya dauki sallallami kafin yace anya saude da hakalinki kuwa yanxu budewar idon taki taki har takai kiyo waje kina kururuwa? To maza tashi ki shiga ciki mutuniyar banza mara mutunci zaki tashi ki wuce ko saina jefeki
Saude ta tashi da sauri ganin yana niyyar jefeta da wani hogen daya rarumo ta fada cikin gida tana kuka sai a lokacin Dr ya dago idanuwansa da suka kada sukai jajir cikin dasashshiyar murya yace kayi haquri baba don Allah inason magana dakai
Malam bala yace Ohoo daman kaine mai hure mata kunnen ko?
, . Dr. ya girgiza masa .kai, yana jin zuciyarsa tamkar zata ballo ta fito  yace,‘ “K0 daya ni dai ne wanda ta ke aiki a ‘ gidana, inda aka kai ta aiki” Malam Bala ya ce “Auho, to bismillah
mu shiga daga soro ai ban fahinta ba, mu shiga in kira maka innar tasu ku gaisa’Ba musu Dr. ya bishi~suka shiga cikin soron gidan, sannan Malam Bala ya shiga cikin gidan ya sa Inna Lami qanwarsa uwa, daya uba daya yace ta kira masa Laure ta taho kuma da tabarma Yana tsaye ta shiga ta fito masa da tabarma tare da fadar, “Lauren tana zuwa” ‘ ’ Malam Bala ya, juya ya dawo ya ‘ shimfida masa tabarma suka zauna, Dr, ya dubi Malam Bala suka gaisa sosai cikin girmamawa  Sannan Dr ya qara gabatar da kansa Baba nine wanda Saude ke aiki a gidana, na maido ta. ne saboda wani muhimmin abu wanda maganar aurenta da ta sanar dani a «yanzu ya tarwatsa komai amma Baba kayi haquri da abin da zan fada maka a yanzu kai
_ masa kyakkyawan kalla da kuma, kyakkyawar ” . fahimta
Baba kai ka haifi Saudat kafi kowa  sonta, kafi kowa sanin ciwonta, kuma amana ce a gare ku abin tambaya a gobe kiyama idan ku ka cutar da ita ku ka wofintar da rayuwarta wallahi sai Allah ya kama ku a kan hakan duk dakuwa kukukahaife ta. ‘ Baba, Saudat tana da masu sonta da aure
a nan garin, da kuma ni  kaina, sannan  Saudat yarinya ce qarama Baba bai kamata ku_ tankWare rayuwarta ku zaba mata mijin da bai cancanta da ita ba don kawai saboda, wani dalili naku kayi haquri Baba na san kuna da hakkin zaba mata mijin da yayi muku, amma Baba’ zaba ” mata mijin da ya‘ dace da rayuwarta don Allah don Annabi Baba ka dubi girman Allah kayi wa rayuwar yarinyar nan
adalci ‘ Tunda Malam Bala ya sadda kansa bai dago ba, komai yake tunani oho! Inna Laure‘ wadda take labe a tsaye hannunta dafe da kofa . tana sauraren duk bayanan Dr. tace, “To muna godiya Alaramma, Allah ya biya. Sai a tashi a tafi umma ta gaida assha, kuma abin da . :ka yiwa “yarmu Allah yasa ayi wa taka, mun . kai diya aiki ka hure mata kunne ka lalatata ka
maida mana, ka iske kuma za a yi mata aure kana Kokarin hanawa kai shaidan wato dandin bai ishekaba ko? To ta fada mana komai, kuma ba abin da za muce maka sai muce ka je Allah Ubangiji yayi mana sakayya”.
Dr Ahmad wanda ya ji maganganunta tamkar: saukar markade, ya dago da sauri yana kallonta cike da mamakin maganganunta ya
Kasa cewa komai, sai Malam Bala ne ya
Daga kai yana fadar, “Ya Isa haka Laure, koma cikin gida don Allah”
Inna Laure tace, “Ka bar ni da wannan‘  babbab shaidanin mai munafurcin kashe aure ya maida mana diya karuwa, kuma saboda rashin imani ya biyo ta har gida ya ce kar a yi mata aure‘ tunda bai gaji da lalatar ba. Malam ka
kalli Saude sosai na rantse maka da Allah cikine da ita”. ldanuwan Malam suka yo warwaje saboda tsabar dukan da maganar tata tai masa a
Kirjinsa. Cikin rudu ya mike yana fadar“Laure ki shiga gida haka wuce ki tafi” Ganin maganganun nata sun yi tasiri a  zuciyar Malam yasa ta juya tana matsar kwalla a munafurce ta gefe tana kallonsa “
Malam ya dubi Dr. Ahmad zuciyarsa na huci yace “Malam mun gode kwarai amma don Allah ina rokonka ka tashi ka tafi don Allah”. .
Dr ya danne mamakin daya cika masa zuciya, cikin qarfin hali ya bude baki da niyyar yin magana.
Malam ya daga masa hannu cikin tsananin fushi ya ce.
“Babu abin da za ka fada don Allah don
Annabi ka tashi ka fita kona samu zuciyata ta sassauta”.
‘ Dr. ya mike tsaye cikin halin jarumtaka,
don gabadaya zuciyarsa’ rugurguza ‘take
tamkar zata Balle Kirjinsa ta fito fili. Ya danne
abin dake yunkuro masa kafin ya iya Karfin
halin fadar “Kayi hakuri Baba, wallahi tallahi na
rantse maka da Allah ban aikata abin da kuke zargina da aikatawa,ba kuma na amince zan tafi amma don Allah ka bani minti biyu in magana da Saudat a gabanka
Malam ya zaburi masa “Kai Malam kaga ka bar nan tun muna shaida juna, don
wallahi Saude ba zata sake fitowa ba sai idan za,a tafi da ita dakinta, kaji na gaya maka”.
Dr Ahmad yaji tamkar anwatsa masa tafashashshen ruwan zafi mai qona zuciya. Ya lumshe idanuwansa yana jin tamkar mala’ikan mutuwa ya taho ya zare masa ransa koya’ huta, ya bude idanuwansa da kyar
‘wadanda suka ida rikicewa baka ganinkomai ‘ cikin shi sai tsananin ja tamkar garwashin wuta.
Ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro ‘ gabadayan canjin da suka yi masa saura, yasan bazasu haura dubu hamsin ba, ya ajiye a kasa
‘ tare da fadar kayi hakuri a bata wannan canjin insha
Allahu ko tana gidanta ne zanyi mata aike”  Ya juya ya fice yana kokarin dauke kWallar dake neman~zuraro masa . Malam ya duka ya dauki kwalin yana . faman juyawa a hannunsa, Laure dake labe tana jira taji yadda zasu  qare ta zabura tayo ‘ cikin soron tayi caraf da kudin tana fadar yauwa “‘KaWo su nan Malam”. ‘
Shi harma ta bashi tsoro ya sakar mata
~ ya tsaya yana kallonta, ta soke a zani tana . fadar
“Allah yaga tsimurmular da muke muna ta fama da Tv Stand ba kayan kallo yanZu k0 kaga
wadannan sai a siyo ma ‘yar baba irin wannan talabijin din wadda ake lika wa jikin bango da ‘ kafet din tsakiyar daki su kadai ne dama ba a siya ba”
. Malam Bala yace“Haba Laure, yarinyar nan ita aka bawa kudin nan, kuma kina sane daga katifa da zanin gado da labule babu abin da aka sai mata, yanzu wadannan ba ‘ sai a Kara a sai wani abun ba?”
Inna Laure tace, “Haba Malam ka sani fa sarai irin mutumin da ‘yarbaba ta aura, dan masu da shinefa dan gidan hali, ne zasu rike; mana ita da mutunci? Ita ko Saude Garba ne fa ka sanni na sankabe, karce ta san kar to mu wahalar da :kanmu na me? Dakunan fa naji ‘yan jere na fadar daki daya ne ya ware mata mai girma, to me za mu zuba a cikin daki daya? Ai dama
Dan gado ne da katifa toga katifar nan ko zuwa gaba ai: idan Allah ya hore sai muyi mata gadon k0 ya kace Malam‘?” ’
Malam Bala ya ce, “Shikenan aje a yi k0ma . ‘ me za a yi. ni dai na rabu da yaran nan lafiya
nan da awa daya za a wuce da su gidan Yaya Maje”. . ‘ Laure ta amsa da, “An gama Malam ’Sannan ta juya ta nufi cikin gidan ta bar shi yana kwashe tabarma.
Tunda Dr Ahmad ya fita ya fada , motarsa ya kifa kansa saman sitiyarin motar bai sake dagowa ba,» duniyar gabadaya «ta shiga juya masa, ya rinka jin tamkar ana sa guduma ana sassaka masa kirji
Ya dauki tsawon lokaci a kife tamkar matacce jijiyoyin kansa suka tattashi rado rado abunka ga jar fata, kamar an zana su, wani irin ciwonkai mai zafi ya sauko masa, ya. dagO‘ kansa da Kyar wanda yake jin yayi masa bala’in nauyi ya mika hannunsa a kwabar jikin .motar ya dauko biro da takarda yayi wani dan rubutu layi biyu ba tare da ya fita ba, ya kira yaro cikin dasasshiyar muryarsa ya ce, “Kasan Saude?” ‘ “‘
.Yaron yace, “Yar talla, wadda ku ka zo
yanzu tare?
Dr. ya ce, ‘Ita don Allah karBi ka kai
mata, ka tabbatar ka ba ta hannunka da nata, kar fa ka ba wa kowa kaji?” ‘
Yaron ya amsa da, “To”. Sannan ya juya ya nufi gidan a guje.
Dr. Ahmad ya maida murfin motar ya rufe ya yi mata key, ya ja sannu a hankali ya bar unguwar.
Saude wadda tunda ta shigo gidan ta fada dakinta wanda aka maida shi na zuba tsummokara ta zube a Kasa ba tare da ta damu da dadattin dayayiba, tashiga rusarkukamai ‘ tada hankali ji take gabadaya ta tsani rayuwar.
Yaron ya shigo tsakar gidan inda jama’a keta hidimarsu ya tambaya, “Ina! Saude?”
Inna Lami ta nuna masa dakinta, yaron ya nufi dakin, ya iske‘ ta kwance Kasa~ tana sharBar kuka, yace “Ga shi inji mai mota a waje ya ce na kawo miki”.
Saude da ke kife tana kuka a dago da kanta a hanzarce tana kallon yaron ta karBi takardar hannunta na kyarma tana qokarin warwarewa kamar tasan abin da aka rubuta ta zuba wa kyakkyawan rubutun ido wanda take jin tamkar shine ta ke gani, yaron ya juya ya tafi ya barta tana kallon rubutun da ba zata iya karantawa ba, illar jahilci”. Ta fada ta qara durkushewa ‘ta dukunkune takardar ta soke
Ta qara fashewa da wani sabon kukan mai ban tausayi.. Yaya Rabi’u ya fado mata a zuciya, ta tuna rayuwarta da shi, da irin yadda yake rudewa idan yaga hawayenta ya yi ta rarrashinta, rayuwa ke nan, ga ta yau tana kuka bata da wanda zai ce kiyi shiru balle har ya rarrasheta.
Yau tayi’ kuka kamar ikon Allah idanuwanta suka kumbura suka yi luhu-luhu, ga bangaren kanta daya dauki ciwo a dole ta saurara da kukan saboda yadda take jin kan nata kamar zai rabe biyu.
Ta tashi zaune ta jingina da bango ta ‘ rafsa uban tagumi tana tunani mai tarwatsa zuciya, Inna Lami ta tah0 dakin ta turo mata robar tuwo wanda aka yaba wa miyar taushe tace, “Ga shi nan idan kin gaji da kukan ki dauka kici da sauri, don yanzu za a wuce daku gidan uban wanka”.
Ta wurgo mata bakar leda, “Ga wannan atamfar uban wanka ceda takalma ‘yan Maradi da abaya wanda zaki saka a tafi,  maza don bake za a tsaya jira ba”.
Tana gama fada ta juya ta yi gaba abinta ta bar Saude na bin ledar da tuwon da kallo, a
yanzu idanuwanta sun KeKashe babu abin da suke sai zogi da radadi mai ciwo k0 motsin kirkibatayiba, har Inna. Lami tadawo ta ~ dauki sallallami, “Wai Saude ya kikeso da mune, kefa kawai akejira,karma kici tuwon
kanki kidaukikayan kisaka mushine ‘ matsalarmu”
Tayi tsaki ta juya abinta.
Saude taKi motsawa daga inda ta ke don yadda ta ke ji. zuciyarta k0 kashe ta za suyi ba za’ta saka kayan ba, har yanzu ji take kamar a mafarki ne komai ke faruwa. Ba ta fidda rai da zata farka a kowane lokaci ta ganta a gidan Dr. Ahmad ba  don haka ta soma linke takardarda
Dr. Daya aiko mata ta daure a
haBar riga tamau. ‘ Inna Lami ta dawo ta tsaya daga bakin Kofa cike da masifa tace “To sai ki fito tunda ba zaki sauya kayan ba, wlh ko,a tsirara ne sai mun kai ki, ehe”. .
Saude tayi maza tana faman muzurai, tana faman kaiwa da kawo wa, idonta ya sauka inda su ‘Yarbaba suke tsaye da .qawayenta, sun sha anko ana ta shewa.
Yar baba ta watsa mata harara tare dajan
dogan tsaki
Saude ta sunkuyar dakanta bataredata kula ta ba, Inna Lami ta ce ‘Taho nan, ‘Yar baba muje ai muku nasiha gaba daya
Tasa hannu ta rike ta Saude na biye da ‘ susuka shigadakin da Laure take.
Ba wata’nasihar kirki bace duk habaici ne take yaba wa Saude, tayi abinta ta gama sannan lnna Lami tatisasu gaba har~ wurin Malam Bala shima nasiha ce dakuma ‘jankunne kada waddatasake talullubo zaninta wai da sunan yaji balle wani abu wai shi jaWarci, duk wadda ta sake ta kashe aurenta, to saidai tasan indazata nufa sannan yayi musu ,. fatan alkhairi daga nan aka dauke su da motoci ’zuwa gidan uban wanka, shi ma’yayi musu nasihar tasa. Ana gama sallar magaruba ” .motocin kai amarya suka zo, qananan motoci ~ masu shegen kyau guda biyar, mijin ‘Yarbaba yaturo dasu na daukar amarya.
Shi kuwa Garba gurgu a kori kura ce kwara guda da ita za a dauki amaryar adauki ‘yan gidansu don haka mutane duk suka kwashe suka nufi motocin‘ daukar ‘Yarbaba da. Kyar ..
aka samu wasu mutum biyu dattijai wadanda zasu raka Sauden.
Haka aka kwashe aka tafi da amaren, Saude ta lumshe idanuwanta kukan ma yaKi yiyuwa, idanuwan sun qafe sai radadi suke, zuciyarta sai faman bugawa ta ke da sauri da sauri tamkar za ta tarwatse.
Direba yaja wani dogon birki kiyyyy! Ya tsaya a kofar gidan, ginin kasa wanda  aka shafe da farar kasa, tsohuwar daya ta riko hannunta.
“Fito muje ‘yar nan sannanki shiga da qafar dama, da kuma bismillah”.
Saude daina ‘ jin maganganun nasu ne tamkar amSa kuwwa a kunnenta, fuskarta na . rufe da hijabi suka shiga cikin gidan mai dogon zaure wanda doguwar kwata ta raba biyu. Suka isa tsakar gidan ‘yan tsaffin na fadar, “Gafaranku dai masu gida”.
Babu wadda ta kula su daga cikin matan
gidan sai‘ yan yara ne keta tsallen murna, an kawo musu amarya su suka nuna musu dakin nata aka shiga da ita, cikin dakin wanda duk
cikin gidan shi kadai ne yaci arzikin filasta da siminti, aka goga masa ‘yar farar
Qasa ciki
babu komai a dakin sai tsohon yadin zanin gado da fuloluwansa guda biyu, dakin ya sha sabuwar ledar Kasa an kuma zagaye bangon dakin da sabuwar sitara sai ‘yan kayan ma’aikacinta a gefe.
Tsohuwa Iya ita da kawarta’ hare suka zaunar da Saude a gefen katifar ba tare da sun zauna ba, sukace, “Tomu zamu wuce Saude sai muce Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya, a yi ta dai hakuri da rayuwa a duk yadda ta zo watarana sai labari, mu dai mun wuce”.
Saude dai dake kife saman katifar k0 dagowa ba tayi ba ballantana su sa ran za ta tanka suma basu saurari tankawar tata ba suka fice abinsu. A soron gidan suka hadu da ango an sha sabon farin yadi da sabuwar hula, bakinnan an cika shi da dusar goro, fuskar nan tasa babu annuri sai sambatu yake, “Yo harni za a yaudara? Ai karya ne wallahi, duk wanda yaci tuwo dani miya ya sha. Yauwa bayin Allah dama kuna biyo, ku koma ciki yadda kuka Kunso tsohuwar karuwarcan kuka kawo min haka zaku koma ku dauko ta ku koma da ita, ba a gidan Garba ba, k0 da kuka
ganni haka nakasasshe to ban gaji da rayuwar duniya ba”.
‘ Tsohuwa Iyah ta tafa hannaye tana fadar, ‘Muhammadu dan Abdullahi, Malam Garba me yayi zafi haka?”
Garba ya taso mata, “Abin, dake cikin wuta, nace abinda ke cikin wuta kinjini yanxu Ai kinga tsohuwa ina ganin girmanku karki sa in dankara muku ashar ku shiga ku fiddo ta in ba haka ba wallahi zanyi abinda ba a tunani,don dukan mutuwa zansa ai muku a cikin gidannan harda ita tsohuwar karuwar ku fiddo ta in kulle dakina kuma ko tsinke
babu abinda  zai fita bayan ita in kunje ku fada wa
tsohon banzan uban nace kece masa nace na bashi nan da kwana uku
k0 ya aiko min da duk abin daya san na kashe
ko kuma in sa kayan dakin a kasuwa ku fada masa na sake ta saki uku”.
Daga nan ya juya yana tsangala qafarsa ya bar su a tsaye baki a sake
Hare ta dafa Iya tana fadar, “Yau munga takanmu ni hare kinga koma kifitoda yarinyar nan mu maida ta hannun iyayenta, ” wannan nakasasshen banzan zai iya fiye da duk abinda ya fada”
Don daman ance gurgu yafi mai qafa iya shege
Iya tace, “Aikuwa na gani bari in fito da
ita”. Ta Juya ta koma cikin gidan.

Hmm jama,a ya abin yakene ku biyoni gobe daidai wannan lokacin donjin yaddah zataci gaba da kayawa
Naku har kullum
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKEN ZAZZAU*

About AIS

Check Also

Yar tallah32

           *YAR.    TALLAH*                *CHAPTER32* Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana tirje~tirje da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *