Yar tallah21

                  *YAR TALLA*

                *CHAPTER21*

         *ASHA KARATU LAFIYA*

Dr yayi wani tsallen murna yana fadin kai thank u very much dad ya sumbaceshi kamar wani yaro momy tace “tunda dad dinka kadai ya siyi bakin to  sai ta zage ta yi magana har sai munce ya isa haka.
Dr. yace, ‘Wlh A a Saura ke Momy.”
Dariya suka sa masa Momy tace ‘Ai kyauta ta tsakanina da ita ne babu mai ji bare ya gani.”
~ Dad yace, ‘Ai kuma bamu yarda da wannan wayon ba mu gani a qasa.”
Momy tace, ‘Ai tsakanin ‘ya da uwa babu mai shiga don ni yanzu na bar maka wannan da baya girma yau na dawo nan. ”
Dad yace ‘Ba komai ai dama tare muke koya kace my son?“ Dr. ya ce ‘Ai k0 dai Dad fada mata mu dai mu
gani a qasa ; Hajiya tace, ‘Hummm! Kan ku akeji “Ta janyo
hannun Saude tana saka mata wani zobe tare da abun hannunsa, sannan ta bude sarkar ta sanya mata da kanta ta cire mayafinta tasa mata yan kunnanyen
Masu shegen kyau. * Dr ya kaure da tafi‘ yana fadar ‘Kai Mamy
gaskiya baki ya siyu.” Dad yace, ‘Sai ku taso muje muyi lunch
Gaba daya ba musu duka suka mike hannun momy sarqe dana Saudat, Dad kuwa yana dafe da kafadar Dr suka nufu dinning area
A tare suka ci suka sha ana ta barkwanci basu suka bar gidan ba sai bayan sallar Magariba. Zuwan Saudat. gidansu Dr. Ahmad yau ya Kara mata darasi a rayuwa iyayensa sun nuna mata qauna tamkar zasu goya ta abin daya karayar mata da  zuciya wanda ya sata kuka mai cin zuciya kenab
‘ Dr Ahmad dake tuqi ya dago ya kalleta kadan sai a lokacin ya lura da kukan da take ya maida kan shi saman. titi muryarshi a sanyaye yace, “Kukan me kike kuma?”
Tamkar bazata tankamasaba, saidatayi dakyar ta iya tsayar da kukan nata kafin tace, ‘Dole ne inyi kuka Yallabai ta yanda  kaiwa iyayenka qarya don kawai ka cimma wata manufa taka, ni dama na sani tun farko ka tsane ni kana san ka ‘kore ni amma ka rasa hanyar da zakabi kar Hajiya ta bata ranta,ne amma nida kabi ta ni ba sai kabi ta wannan hanyar ba ta nuna kana sona ba, don hanyace ta tarwatsa rayuwata wallahi, idan daga nan ka sauke ni ba zaka qara ganina a gidanka ba har abadan ‘ abada” ‘
Ta qarasa maganar tare da qara rushewa da wani sabon kukan ‘
Dr ya taka birki tare da sauka daga saman Iitin ya . koma gefe ya_faka motar ya kunna fitilar dake cikin
Motar ya jirkito yana kallonta gaba daya ya tattara duk _ wata nutsuwarsa a kanta, cikin sanyin muryarsa ya kira Sunanta.
“Saude kenan wallahi tallahi tunda nake ban taba tunanin tarwatsa rayuwarki ba kullum fatana shine in ga rayuwarki ta inganta dubi idanuwana Saudat kalleni don Allah.’ Ya fada. tare da riKo hannunta wanda ya tilasta mata kallon nasa.
Tayi saurin sauke idanuwanta saboda wani irin kwarjinin dayi mata ga alamun damuwa nan bayyane kwayar idanunsa Dr yaci gaba da fadin
“Ki kalle ni sosai Saudat idan har kin san abin da ake nufi da. so to zuciyata na dauke da dumbin soyayyarki da qaunarki’, kuma duk abin da ki ka ji ina fada da gaske nake a shirye nake da auren ki a kowane Yanayi.” Saude ta yi saurin dagowa a razane tana kallon shi,
tsabar rudu da kaduwar da tayi yayi bala’in firgitar da ita, a nutse yake kallonta ba tare daya sake magana ba cak kukan Saude ya tsaya ta soma magana tana kallon tsabar idanuwansa, cike da kaduwa ga muryar har ta soma: disashewa saboda kukan da tayi cikin sarqakKiyar murya ta soma fadar.
“Dan Allah don Annabi ka rufa mini asiri kar ka Sake furta wannan kalmar wadda zata. zamo makamin rugujewar rayuwata wallahi kafi qarfina ta kowace
fuska, kai basa an aurena bane karkama sake fada” don Allah don Annabi.”
Dr. ya lumshe idanuwansa ya harde a tsanakke ya soma magana ‘Ba kya sona kenan Saude Juyo ki kalle ni ki fada mini ba kya sona, fadi kawai
Saude taji tamkar yana buga lugudan tashin hankali a zuciyarta ta runtse idanuwanta tana jin tamkar zuciyarta za tayi bindiga.
Dr. ya sassauta murya tamkar mai shirin‘fashewa da kuka yace ‘Saudat wallahi ina son ki, so kuma irin na gaskiya wanda babu wasa a cikinsa, kuma wallahi a shirye nake dana fuskanci kowace ‘irin jarabawa ce a kanki, ki amince min don Allah inamai tabbar miki ba za kiyi nadamar damqa mini zuciyarki ba. ’
Shi yasa na fara kai ki wurin“ iyayena kafin in furta abin da ke zuciyata,‘ duk da basu san wace ce keba, amma abun zai zo da sauki don gari na wayewa gobe zan mai da ke Katsina idan kuma kin amince na nemi auren ki ’
Cikin kuka Saude tace ‘Ta yaya zan mince in jefa rayuwata cikin matsala? Wace ce ni da zan iya kishi da matarka? ‘Yar wace ce ni a qasar nan da zan so miji kamar ka? Yallabai kafi karfina kai ba sa an aurena ba ne wallahi.’
Dr ya ce‘Niba wannan na tambayeki ba Saudat ‘ shi aure  sa a da sa a ne? Wa ya fada miki? Ai shi aure cancanta ce kawai, Kuma da ki ke maganar kishi da Asma, wace ce ita, ta isa ta hana abin da Allah ya“
Qaddara ne? Saude nina ganki kuma nace ina so kuma mutum ko aljan bai isa ya. hana ni sonki ba har sai idan kece kikace bakya sona, kuma insha Allahu na san ba zaki fada
ba, haka ne?”
Yayi maganar tare da matsar yatsun hannunta wadanda ke cikin hannunsa, Saude ta runtse idonta tana jin wani abu na yi mata kai komo a zuciya. To k0 shi ne son? Ta tambayi kanta.
Dr. ya girgiza ta tare da fadar, ‘Bude idon ki Saudat ki kalli masoyin ki ki furta abin dake ‘ zuciyarki, shin kina sona zaki aure ni?”
Shiru ya ratsa wurin ta kasa cewa uffan. Dr. cikin sarkewar murya yace, ‘Don Allah kiyi magana kice wani abu, please Saudat. ”
Kunya da nauyinsa suka dabaibaye ta ta samu ta duke da qyar kafin ta iya magana cikin wata rikitacciyar murya tace, ‘Toka sake ni in fada.”
‘ Da sauri ya saki hannun nata yana fadar, ‘Na saki fadi.”
Saudat ta dan yi jim tana tunanin abin da zai iya Zuwa ya dawo anan gaba don haka cikin raunanniyar murya ta soma magana.
“Yallabai niba sonka ne ba nayi ba, asali ma kai abun alfahari ne ga duk macen data same ka ballantana  makaskanciya mai tsananin rauni. YallaBai zuciyata ceke cike, da fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo, wallahi ina tsoron tashin hankali ban son abin da zai sanya rayuwa ta damuwa koya yake.’
Dr. ya ce, ‘Haba Saudat ai matukar ina “ciki Kin gama zubar da hawayenki a kan damuwa, sai
dai k0 hawayen soyayya wanda farin ciki ke sawa a ‘ zubar dasu saboda shauki irin na soyayya.’
Kuka da dariya suka kwacewa Saude Iokaci guda, ‘tasa tafin hannu ta rufe fuskarta,
Dr. ya yi murmushi . tare da Juyawa ya yi wa motar key yasata a hanya suka cigaba da tafiya
Ba tare da waninsu ya sake magana ba.
Horn din da taji yana wa maigadi shi ya tabbatar ~ mata sun iso  Cinna hancin motar cikin gate din gidan yayi daidai da bugawar zuciyar Saude dif zuciyarta  tatsaya da aiki a take.
Ina ga k0 Asma ce zata fito, Saude taji muryar Dr na fada wanda bata ma fahimtar me yake fada saboda tsabar rudu da kaduwarda take ciki.
Saude ta runtse idanuwanta ganin Asma ta nufo motar tasu, Dr yaji tamkar ya juya sai dai babu dama don kuwa tuni masu gadi sun riga sun rufe gate kuma k0 kafin su sake budewa ya tabbatar ta iso.
. Don haka ya yi dabarar bude motar ba tare daya gyara fakin ba ya fito yasa key ya kulle motar ya nufe ta tun kafin ta Karaso yana fadar
“Saukar yaushe  My dear.”
,, Turus yaja ya tsaya saboda k0 kallon shi bata yiba ta wuce shi ta nufi wurin motar, gaban Dr yayi wata masifaffiyar faduwa ba wai don yana tsoron Asma ba, a a saboda Saudat don ya lura tayi matukar ’ ‘firgita da ganin Asmar matuqa don haka Jikinsa  a ‘ sanyaye yabi bayan ta
Tana qarasawa gaban motar taja ta tsaya ta miqawa Dr. hannu, ‘Bani key ” Ta fada cike da gadara.😏
Dr. yaja ya tsaya a gabanta cikin nuna halin ko’in kula yace, ‘Bazan bayar ba kina da ajiya a ciki ne?”
Cike da mamaki Asma ke kallonsa kafin ta iya bude baki tace, ‘ba zaka bayarba ni kake fadawa haka Ahmad? Hmmm! Da kyau ba zanyi mamaki ba tunda ka dauki ‘yar iska kun fita kun gama yawan iskancinku kun dawo ai dole zaka sawa mota key tunda Allah ya toni asirinku. .
Amma ka sani daga rana irin ta yau ka gama marmarin fita da kowace. karuwa don saina sa tayi nadamar da baza ta taBa qarawa ba wallahi, dan ba irin Asma ake wa irin wannan tozarcin da wulakantar ‘ ba a cikin gidanta, mayaudari, munafuki kawai.’ Tana maganar tana kwance dankwalin kanta.
Ta hau daura damara a qugunta tamkar mai shirin shiga filin dambe ta durkusa ta kwashi duwarwatsun da aka baza a harabar gidan ta hau jefa su a gilas din motar tana fadar.
“Wallahi yau sai dai k0 ni ko ke a gidan nan ‘yar iska wallahi sai nayi ajalin ki, karuwar banza.”
Dr. dake tsaye ya yi saurin rike ta yana fadar, ‘Wai meye haka Asma kina da hankali kuwa kike abu kamar ba. educated ba, wannan ai hauka ne kike da
RaShin hankali a gaban mutanen da suke a qarkashin ki wannan ai kanki kike jawa abin fadi a duniya.’
Asma ta kwace daga riwon da yayi mata tana haki tace ‘Kai da Alla ni rufe min baki kai har wani mutunci ne ka ‘sani bacin wanda ka zubarwa kanka a bainar jama’a, ai idan akwai wani sakarai marar hankali to bayan ka yake, mutumin da ya maida ‘yan aikin gidansa abokan cin garinsa, ai sai yanzu na fahimci abin dake korar duk ‘yan aikin dana kawo maka, kuma wallahi ba zan taBa rufa maka asiri ba sai duniya ta san abin daka aikata, kuma yarinyar nan yau saina halaka ta.
Bai ankara ba ta rarumi wata qatuwar adda wadda ake aske fulawowi da ita, ta sauke madubin motar, wanda yayi daidai ta fasa qara Saude wadda ke zaune a gaban motar.
Dr. yayi saurin rike Asma yana fadar, ‘Waike wace irin mahaukaciya ce wallahi zaki jawa kan ki aikin dana sani, dan na rantse da Allah idan ki ka kashe yarinyar mutane wallahi sai nayi shari’a dake
Da sauri ta kalle shi bakinta a sake cikin sarkewar murya take fadar, ‘Za kai shari’a dani Ahmad akan karuwar? Lallai kam dana nuna maka kai Karamin dan bariki ne. To bari in kashe ta sai kai qarar tawa.”
Dr. ya qara rike ta gam kafin yace “Asma ya kamata ki shiga hankalin kifa dan kin sanni sarai bazan lamunci wannan haukan naki ba, don ban ga abin da a kai ba, wanda zai sanya ki wannan jakancin ba idan mun fita da Saudat saime ‘yar aikina ce ina da
Right din fita da ita muyi siyayyar abin da ake buqata. dan me zaki nemi tarwatsa mini tunani haka kawai?”
Asma ta girgiza kai, ‘Lallai Ahmad ka cika dan akuya yanzu akan karuwar Nanne ka ke kirana da jaka, lallai kam anayi, kun tafi siyayya ne shi yasa kuka . tafi ku biyu babu bak0  direba, kuma ta zauna a gaban
° mota. Kai gaskiya ne ai naga hakan, amma sai dai abin daka manta k0 ranar da ka fara ganina a duniya da hakorana talatin ka gan ni cur, ballantana ka maidani
. Karamar yarinya, wadda bata san abin da takeba.
Kuma wallahi tallahi na rantse maka da Allah sai nayi ajalin ‘yar iskar yarinyar nan jaka sakarya
daqikiya ballagaza wadda iyayenta suka sadaukar da ita saboda abun duniya, wallahi daga yau ta gama karuwanci da kowa.”
Dr. yace, ‘Hmmm! Asma kenan kina bani mamaki yanzu har iyayenta sun miki laifi dan sun Sadaukar da ‘yarsu tazo tayi miki abin da kika gaza Min a rayuwar aurenki ashe har sun miki laifi?”
ldanuwanta a warwaje ta soma fadin, ‘Ban gane ba? Dama na dauke ta aiki ne don ta maye gurbina?”
Cikin rashin damuwa yace “Yes k0 kin dauka ‘abinci shine kawai matsalata niba mutum bane?  Dole
kwai wani abun da nake buqata bayan wannan, dole ‘
lna buqatar kulawa ta mace, sai dai bata gurbatacciyar hanya wadda take haramun ba, don sanin kanki ne niBa mazinaci bane shi yasa na yanke hukuncin auran  Saudat don naji dadin maye gaba daya gurbin ‘
naki wanda sabgogin yau da kallum suka saki ka “watsar.”
Cikin tsananin firgita da razana Asma ta kwace daga rikon da yayi mata tana fadar, ‘Kutumar ubannan Kai karya kake wallahi tallahi karya kake Ahmad ba ka isa ba na rantse maka da Allah babu ‘yar matsiyatan data isa ta shigo cikin gidan nan batare dana nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane.’
Dr. Ahmad yace Ai ko sai dai kada a Kara; domin zuciyar Ahmad ta riga ta yi nisan da mai rai ba zai gane iya adadin gudunta ba, kuma ina mai tabbatar miki k0 da malaman dake Barno da Nijar. malamankine ba ki isa ki hana wannan lamarinba. Da fatan kin gane  Asma ta hauja da baya da baya tana fadar ‘Ni. .ni Ahmad wallahi qaryarka ta sha karya wallahi baka isa , ba Ta durkusa tana kokarin daukar addar a qasa, wadda ya kwace daga hannunta.
‘ Dr ya kalle ta yana fadar, ‘Wallahi idan kika matsa kusa da motar can a bakin auren ki ’
Yaja wani dogon tsaki ya juya yayi gaba ya barta ‘ ta fasa wani gunjin kuka ta durkushe a gun Dr ya fada motarsa sai dai ganin halin da Saude  ,ke ciki ya daga masa hankali kuma yaga masifar” dauriyarta don gilas din motar da ya fashe sai da ya yanki goshinta, jini ya zuba sosai duk ya bata mata fuska, hankalin sa  ya tashi ya tayar da‘ motar ya fice
daga gidan ba tare daya sake kallon inda asma take ba, ya nufi asibiti da ita. Suna zuwa kuwa aka karbe ta akai mata dressing
din ciwon aka rubuta mata magunguna, sannan suka baro asibitin. A cikinsu babu mai magana kowa da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Can Dr. ya dan waigo
ya kalli Saudat sannan ya maida kallonsa a kan titi cikin sanyayyar muryarsa yace.
“Don Allah don Annabi kiyi haquri Saudat kada dan wannan abun ya daga miki hankali k0 kadan, ni dai nace ina son ki kuma ni zan zauna dake ba Asma ba. To insha Allahu na yi miki alqawarin farin ciki da jin dadin rayuwa a duk inda suke zan nemo miki su, fatana ki’ rayu cikin farin ciki da walwala, kar ma abin datayi dinnnan yadameki kinji?”
‘ Kai kawai ta daga masa alamar eh, amma qasan zuciyarta cike yake da tsabar rudani da tsoro.
Dr. ya ~ tsaya ‘Gidan Abinci’ yayi take away sannan ya dawo suka wuce. Kai tsaye daki ya kama a wani hadaddan hotel mai tsadar gaske kwana daya, ya bata makullin dakin mai lamba 12, sannan ya ajiye mata ledar take away din ya gwargwada mata komai a cikin dakin Wanda yake da qaton falo da bedroom sai bandaki da dan wurin hutawa.
Sannan ya dube ta a nutse, “Dafatan dai babu wata matsala?”
Saude dake tsaye tana kallon shi ta sunkuyar dakai qasa muryarta a sanyaye tace, “Babu.”
Dr. ya ce ‘Okey zan wuce mu jeki rufe dakin  ki tabbatar kin kulle sosai sai Zuwa da safe,,insha Allahu zan dawo sai mu wuce Katsinan a tare kinji ko?” “
, Saude ta dago da idanuwanta wadanda suka ciko da kwalla ta daga masa kai,
Dr. ya dan tsura mata idanuwa jikinsa a sanyaye yace ‘Saudat hawaye nake gani a idanuaki meye kuma?”
Saude ta sadda idanuwanta tana wasa da yatsun hannunta ba tare da tace uffan ba
Dr Ahmad ya Kara matsowa daf da ita cikin sanyayyar muryar shi ya kira sunanta
“Saudat me yasa kike san tayar min da hankali ne?
‘Me yasa ba kya son ganin nutsuwa ta? Kinfi son ki
ganni a firgice ne, iye Saudat?” Kai kawai ta girgiza masa ba tare da ta kalle shi ba Yace, ‘To meye? Ba kya san in tafi ne in zauna tare
. dake. ” Da sauri ta daga masa kai don kuwa abin dake
zuciyarta kenan, don gani take tamkar idan ya tafi ba zata sake ganinsa ba.
Ya yi murmushi wanda ya bayyanar da haqoransa kana yace “Ki sha kurumin ki My dear insha Allahu babu abindazai faru kedai kiyita addua kawai kinji?” . ‘
A hankali ta daga masa kai ya ce ‘Yauwa ko kefa, ‘ kikwanta ki hutakinji, kiyibarci mai dadi saida safe. ”Yaja mata hanci yana dariya sannan ya fice.
Saude t a maida qofar ta rufe ta koma ta jingina da ; kyauren idanuwanta a lumshe zuciyarta na bijiro mata ’ da wata irin matsananciyar soyayyar
Dr. Ahmad wanda take jin a yanzu tamkar ta bishi ta zauna a tare da shi, farin cikinta da fargabarta ba zasu musaltu ba. Farin cikinta dai shi ne ta samu namiji daya tamkar da goma ajin duk wata isasshiyar mace. Fargabarta kuwa itace. Shin kuwa zai iya auren ta don ita ta san ya riga yafi qarfinta ta kowace fuska, to idan maya ‘ aureta  ya zatayi da matarsa Asma, don yau taga. A kwayar idonta
A hankali taja Kafafuwanta ta nufi bedroom din kai tsaye bandaki ta nufa ta dauro alwala ta fito tayi sallar isha,i sannan ta tashi ta haye saman“ madaidaicin gadon daya sha shimfida ta alfarma ta zauna ta jawo take away din da ya ajiye mata ta bude taci abin da za ta iyaci Sannan ta kwanta, ba dan tana jin barci ba sai dan ta samarwa gangar jikinta hutu
Tunda ta kwanta ba ita ta farka ba sai Karfe shida saura ‘yan mintina, ita kanta tayi mamakin tsawon lokacin data dauka tana barcin, don haka ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah, sannan ta zauna tana lazimi tsawon lokaci sai data gaji don kanta ta mike ta koma ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin gida da irin abin da zata iya fuskanta a can din. Rayuwarta ta baya a gidan ta dawo mata tare da tunanin masoyinta Hamid, har yau har gobe tana jin son shi a zuciyarta,“saboda shi ne mutum na farko data
Fara so a rayuwarta kuma shine mutum na farko daya fara burin taimaka mata
Kwankwasa kofar da ake ne ya sata saurin tashi ta tashi ta bude qofar, Dr. ya shigo yana sanyé da shigar wani sabon yadi milk colour, mai laushin gaske an yi masa aikin hannu a jikin rigar Yana .sanye da hula sai takalminsa na fata
‘idonsa na sanye da siririn farin gilas, gaba daya kamshin turarensa ya mamaye falon.
Saude ta durkusa tana gaishe shi cike” da girmamawa,
Dr. ya amsa yana fadar, ‘Daga yin knock sai ki bude kofa ba tare da kin tambayi k0 waye ba baki san nan batel bane? Komai na iya faruwa fa.”
Muryarta a sanyayé tace, ‘Ai na san kai ne
Dr. yace ya a kai ki ka sani? Ta dan yi jim kafin tace ai kace min zaka zo da safe. Ya dan yi wani murmushi kafin yace ashe baki da mantuwa kinsan in bayan dana manta ban nuna miki yanda za kiyi
kisa a kawo miki break ba da bazan zo nan ba sai wurin sha biyu da wani abu
Yaja ya zauna tare da tura mata katuwar jakar dake hannunsa yace duba kiga kayan nan idan sun miki saikisa yanzu sai mu tafi.’ Saude ta zauna saman  kafet tare da janyo ledar gabanta ta shiga bubbudewa a  ~ sanyaye ’
Dogon wando ne baki irin mai kama qafafuwan nan an masa adon pink color sai rigarsa
» Shima ma pink mai adon baki, rigar mai yankakken gaba wanda ake kira da V neck
Rigar mai dongon hannu ce,,,sai wata duguwar riga har qasa itama pink colour ita ma mai dogon hannu, tana da yankakken gaba sai siririn mayafinta.
~ Ta ajiye kayan ta janyo wani qaton kwali ta bude” takalmi ne a ciki baki da ‘yar qaramar pose irin wadda ake makalawa a hannu, ‘yar qarama, sannan ta Ciro wata ‘yar jaka, saitin kayan shafawa ne a ciki hade da sabulu da turare kayan sun bala’in
Burge ta har cikin ranta, shi kan shi ya fahimci hakan ‘
a idanuwanta, don haka muryar shi a sanyaye ya ce. “Sun yi kyau k0?” Murmushi kawai tayi ba tare data tanka ba, ya
mike tareda fadar kije ki shirya dame zakikarya ?
Me za,a  kawo miki?”
Saude ta sunkuyar da kanta tare da fadar, ‘Komai aka kawo min.”
Cikin zolaya yace, ‘Ba dai komai ba k0 zaki ci shinkafa da miyar kwadi?”
Da sauri ta kalle shi ido waje, ya yi wani siririn murmushi kafin yace ‘Yes nan ba abin da ba sa dafawa har miyar dodon kodi.’ Saude ta Bata fuska
tamkar zatayi amai tace ‘Nidai a,a ‘ Yayi wata dariya irin wadda ba ta taba sanin ya iya ta ba da alama yanda tayi maganar cikin shagwaba yayi masifar burge sa tare da daukar _ hankalinsa, ya matso daf da ita yana kallonta da
yace, ‘Dan qara‘ maimaitawa muji please. ’
Kunya ta kama ta ta juya da sauri tayi ciki ta bar shi nan tsaye harde da hannu a qirji yana kallonta
har ta bacewa ganinsa, ya yi wani murmushi tare da
‘lumshe idanuwansa ’
Saude na shiga bedroom din ta fada saman gadon dakin ta rungume filo cike da murna haka kawai taji wani irin farin, ciki ya baibaye ta, ta lumshe idanuwanta tana mai son tuno wani abu can
‘ kamar wadda aka tsikara ta zabura ta mike da gudugudunta ta fada bandaki ta watso ruwa a gurguje ta
‘dauro alwala ta fito ta yi nafila raka’a biyu tare da roKon Ubangiji ya kare ta daga sharrin Inna Laure, don tanaji ajikinta wannan karon idan akahanata auren
Dr. mutuwa kaWai za tayi.
Tana gama addu’ o ’inta ta mike ta janyo ‘yar jakar kayan shafawar ta fito da su ta matsa mai lotion a jikinta, sannan ta shafa hoda ta sa abun
‘ gyaran gira ta gyara girarta, har ta soma sai da tasa
. maskara ta gyara ta, sannan tasa brown eye a girarta tabi bakinta da sassalikan jan baki pink colour; sai ka rantse da Allah kalar lebanta ne haka.
Saude ta mike ta janyo kayan ta saka dogon
‘ wandon: wanda ya kama ta tsam-tsam sannan ta
”’ kawo rigar ta sanya, wadda tabi illahirin jikinta ta
lafe, Saunan ta kawo dogUwar rigar ta dora ta
Warwaré gashin kanta ta Kara daure shi sosai, ta yi masa tamkar gammo a baya, ya zama tuntu sannan ta » ‘ kawo gyalen rigar tayi kamar rawani da shi.
Ta Ciro takalmi mai tsini ta saka, ta dauko pose din ta saka sarkar da mahaifiyar  Dr. ta bata a ciki saboda rigar ba a hada ta da sarka sai dai ta bar dan
kunnen a kunnenta tare da abin hannu da zobe
Ta dauki turaren ta faffesa a  ko’ina na jikinta,
Sannan ta tsaya gaban madubi tana qararewa kanta kalli, Barakallahu Masha Allahu ni dai abin da zan ‘ iya cewa kenan don a gaskiya na san Saude ta hadu  ita kanta bata san tana da wannan kyan haka ba Masha Allah.
Ta fito daga dakin cikin nutsuwarta, Dr Ahmad dake zaune saman kujera yasa kayan abincin a gabansa bai san lokacin daya mike ba yana kallonta, hatta qaraso gabansa ta durkusa a gabansa.
“Sannu da hutawa YallaBai.”
Dr‘ Ahmad ya koma ya zauna jiki a sanyaye sannan ya amsa da yauwa sannu Saudat, kin sha kyau wallahi irin wannan haduwa haka.
Murmushi kawai tayi, Dr ya dake dan karya bada kansa yace Bismillah maza ki karya mu tafi tana murmushi ta janyo tiren kayan abincin ta bude  tea   flask, ne sai kayan hadinsa, sannan soyayyan kwai da agada, sai wani kwanon
tangarab shi; kuma farfesun zallar tsokar kaza ne
‘ Saude ta dauki kofi ’guda biyu ta hada masu
ruwan tea din sannan, ta miqa masa DR  ya tsaya  yana kallonta kafin ya ce ‘Waya fada miki ban ‘karya ba?”, ‘ Murmushi kawai ta yi tare da qara mika masa kofin, yasa hannu ya karBa ya hada da kofin  da hannunta ya riKe yana Kokarin ya hada ido da ita, yana muryarshi a sanyaye yace Thank you. ”
Saude ta zame hannunta ji take tamkar ta zabga da gudu, tayi ta maza ta dake ta dauki kofin  tea din ta soma tsotsa tamkar wadda babu makoshi a bakinta.
Duk abin da take
Dr yana kallonta baice mata
Kala ba, tayi ta tsatsar abincin, sai da ta gama sannan ya mike ya dauki makullin motarsa ya dube
ta‘Muje ko?’
Da to kawai ta amsa ya yi gaba sannan ta bi shi a baya, ya tsaya ya yi ‘yan abin da zaiyi cikin hotel din sannan ya fito suka shiga mota suka dauki hanya kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa.
Dr. ya miqa. hannu ya kunna masu karatun Alkur‘ani mai girma.
Don haka Saude ta koma jikin makarin kujerar ta” ‘ kwanta ta. lumshe idanuwanta tana sauraron karatun,‘ zuciyarta kuwa ta harba zuwa gida, fargaba mai~
tsanani ta shige ta tana tsoron makircin Inna Laure ‘ tana tsoron abin da zai iya zuwa. ya dawo.
= hanya. Babu mai magana a cikinsu kowa da abinda“ yake saqawa a ransa
A haka barci barawo ya sace ta, ba ita ta farka ba sai da taji yana tayar da ita an kusa zuwa Welcom to Katsma, saude tayi firgigit ta bude idanuwanta wanda hakan yayi daidai da bugawar zuciyarta.
Innalillalhi’ tayi saurin fada da qarfinta.
Dr ya yi saurin kallonta da hanzarinsa yana , fadar lafiya? Ta’ dan ja numfashi kafin tace, ‘Wallahi ji nayi gabana ya yanke ya fadi, Dr. ya’ juyo ya dan kalle ta kafin ya maida kallonsa kan titi yace, ‘Ki rinka maimaita innalillahi wa inna ilaihirrajiun
. insha Allahu ko ma meye zai zo miki da
sauki.’
Saude ta amsa da to, sannan ta nuna masa kwanar unguwarsu kafin a qarasa welcome to Katsina, haka ta rinka nuna masa hanya har suka iso kofar gidan nasu, gaban Saude ya Kara wata muguwar bugawa .. ganin manyan rumfuna a kakkafe a kofar gidan da ‘ ‘yan tsirarun mutane a ciki.
Saude ta dafe kirji, ‘Wayyo Allah na k0 dai Babane ya rasu?”
Dr yayi saurin kallon Kofar gidan kafin yace
“A a ba mutuwa bace, dan ga buhun goro can a gefe’ « Saude ta sauke wata ajiyar zuciya kafin tace, ‘Ina Jin ko‘ yar Baba aka daurawa aure yau.’ Dr; ya lumshe idanuwansa ya bude a hankali kafin yace, ‘Watakila, ki shiga ki gani sai‘ki min sallama da Baban.
Saude ta amsa da to tare da bude murfin motar ta fice.
Tun kafin ta fito dama hankalin mutanen dake zazzaune ya dawo kan hadaddiyar motar ta Dr wadda ta dauke illahirin hankalinsu, duk da ba zaka ; iya ganin wanda ke ciki ba saboda bakin gilas din dake a motar
Saude na fitowa daga motar kallo ya koma kanta, sai kace ba mutum ‘yar uwarsu ba, mutanen dake zazzaune a rumfar ba zasu wuce goma ba  tun daga nesa ta dan gane mutum uku mahaifinta neda ‘ kuma qannansa guda biyu, sauran kuwa bata san k0 su waye ba 
Saude ta qaraso  ta durqusa har kasa ta gaishe ‘ su, tamkar zasu kwanta mata suke amsawa, saboda ’ tsabar girmamawa; amma ban da mahaifinta wanda ya Kara kafe ta da idanuwansa muryarsa a sanyaye yace, “Wace ce wannan kamar Saude?”
Saude tace, ‘Nice Baba.”
innalillahi ’Yanzu Saude  kece kika koma haka? Ina Dillaliyar da suka tafi dauko ki dazu?” . Gaban Saude ya fadi cikin sanyin jikinta tace, Ai kobasu kai ga zuwa ba, Allah yasa dai lafiya?“
Malam Bala yace, ‘Yanzu dai tashi ki shiga Ciki  Kawu Isiya yace ‘Wai wace Sauden ce kake fada ban fa game ba?”
Malam Bala yace, ‘Saude dai wadda aka tura a dauko a can Habuja amarya ita.” ‘
Kawu Hamisu yace, ‘To wancan mai motar fa daya kawo ta?”
Bata saurari abin da yace masu ba ta yi cikin gidan da sallamarta, mutane neke ta kujibakujibarsu an cika tsakar gidan nasu‘makil da mata, an girke manyan tukwane da murahu Sai faman tuKin ‘ tuwo da sanwar miyé ake, kana gani k0 ba a fada maka ba ka san hidima ake.
Saude ta gaishe su sannan ta wuce dakin Inna Laure wanda shima yake ciké da jama’a, duk gungun matan  da Saude ta gani kafin ta gaishe su su sun gaishe ta, ana fadar sannu da zuwa Hajiya, bata damu ba don a‘ lokacin burinta kawai taji hidimar me ake a gidan nasu. ‘ ‘
Ta “samu ta kutsa dakin Laure ta gaishe da jama’ar sannah ta wuce har bakin’ gadonta inda take zaune ita ~ da ‘Yar Baba an ‘sha ankon shadda an kashe dauri sai faman zufa ake. ‘
Saude “ta~ qaraso har bakin gadon inda Inna Laure take inna laure ce ta fara  fadar ‘Sannu da zuwa Hajiya kar dai ince. harda ke aka taho kunji Saqon bazata haka, sai aka ce muku an daurawa yarinya aure yau din nan.’ ko
,Saude ta . durkushe a bakin gadon muryarta a sanyaye ta soma fadar, ‘Bikin wa ake Inna Laure?” ‘ . Gaban Laure yayi wata masifaffiyar faduwa ’wanda yaja mata wata muguwar zabura daga ita har ‘ ‘Yar Baban. Inna Laure ta mike tsaye tana gyara daurin zani tana fadar.
“Me nake gani haka me zan gani Saude kece ki ka koma tsohuwar karuwa haka? Innalillahi wa’inna ‘ ilaihir raji’nn! Jama’a ku taya ni figa kishiya ta zama zakara. Saude mu zaki zubarwa da mutunci a gari mu zaki jawa abun kunya abun fada, wayyo ni  Allah naga ta kaina ‘ .Sai ta fashe da kuka ta fadi qasa. Sumammiya jama,a sukayo kanta suna fadin a taimko da ruwa laure tayi dogon suma
‘Yar Baba ta kalli Saude sama da qasa ta
watsar taja wani uban tsaki tana fadar, ‘Aikin banza ai
. dai dadin abun da ba a san. asalin balbela ba da sai
tace daga Masar take, kuma duk riqar qadangare bai
isa ya zama kada ba a Kadangaren nan dai na shi zai
zauna. .
Idan kina jin dadi ne kin tafi birni kin goge to babu
, abin da gogewar taki zata kareki dashi domin yau dinnan
za a wuce gidan Garba Gurgu don tuni an daura auren, ‘
ki dashi a safiyar yau kuma wallahi tallahi wani abu
‘ idan ya samu mahaifiyata sai na dauki fansa a kanki
munafuka kawai.’ . ‘ Tunda ‘Yar Baba ta furta daurin auren nata Saude
ta sulale qasa tana wani gunji mai kama da gurnan,ji
take numfashinta na wani sam -samA kamar zai dauke.
Ta rushe’ da wani irin kuka mai daga hakali, ta zabura tayo waje a guje tamkar marar hankli ta tsallake mutanen dake waje da gudunta tana jin mahaifinta na kwala mata kira, amma bata tsaya ba
Dr Ahmad wanda ya gaji da zaman motar ya fito ya jiggina da motar yana latselatsen wayarsa ya ganta
Ta fallo a; guje hankalinsa yayi masifar tashi ya nufe ta yana qokarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani irin gunji kuka
ya rikice cikin tsananin rudani’ ya riko ta yana fadar, “Meya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne, ki fada min?’
Sande ta. Qara rushewa da wani kukan ba tare da ta saurara ba‘ ta shiga qakarin fadar, ‘Na mutu.. na mutu… na lalace… YallaBai.., an daura min aure yau..’
‘innalillahi wa ’inna ilaihirrajiun
Abin da
Dr. Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa kansa saman motar.
« ALHAMDULILLAHI
Wohoho jama nasan da yawanku kunyi missing din laure to mun dawo qauye ya abin zai kasancene da
DR AHMAD wai INA YAYAN SAUDE SHIN MASOYIN SAUDE HAMID FUSHI YAYI YA HAQURA DA ITA KO YAYA SHIN WAi ME ZAI FARUNE IDAN SU DILLALIYA DA ASMA AKA HADU Hmm YA AUREN SAUDE DA GARBA GURGU ZAI KASANCE wadannan amsoshin tambayoyin naku na cikin YAR TALLA BOOK3 WANDA ZAMU FARA GOBE daidai wannan lokacin idan mai sama ya nufemu da gani  Naku har KULLUM
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKEN ZAZZAU*

About AIS

Check Also

Yar tallah32

           *YAR.    TALLAH*                *CHAPTER32* Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana tirje~tirje da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *