Yar tallah18

             *YAR.      TALLA*

              *CHAPTER18*

1page is missing
Gaban Ahmad yayi wani mummunar faduwa cikin sanyin jiki yace, “Lafiya kuwa meke damun kine? Tamkar ba zata tanka masa ba saboda yanda kukan yake. neman Kin tsayawa, sai daya sake‘ maimaita mata tambayar, sannan ta samu ta tsaida
, kukan cikin shakakkiyar muryar da ta gaji da kukan
Tace
“YallaBai me yasa rayuwa take zuwa da abubuwa marasa dadine irin haka? YallaBai me yasa rayuwata kullum bana ganin haske sai duhu a cikinta? Me yasa rayuwa ta kullum take neman rugujewa ne saboda wahala?” YallaBai shin ….. ”
Kuka yaci Karfinta ta kifa kanta a kan cinyarta taci gaba da raira abin ta. Wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar Dr. Ahmad, ya durqusa gabanta a hankali har tana jiyo kamshin turaren dake fatar shi.
Muryarsa a sanyaye ya kira sunanta ‘Saudat Wanda yasa ta dago kanta da sauri don bata taBa
zaton ya san sunan taba, kuma yau ne karo na farko daya taBa kiran sunan nata. Yaci gaba da magana, ‘Saudat k0me rayuwa ta
‘ bada hakuri aka a karba, ki karBa’ duk abin da rayuwa tazo miki da shi ki rungume shi, sai kiga Ubangiji ya taimake ki a duk inda kike, yawan kuka ba zai kare ki da komai ba sai ma ya haifar miki da . wani ciwon. Kalle ni Saudat.” Ya fada da siririyar » murya, ta dago da jajayen idanuwanta tana kallon ,
shi, ya mika lallausan hannun shi yana goge mata hawayen: “Ki daina zubar da hawayen ki irin haka, alhalin
baki tanadi mai share miki shi ba.”
Saude tayi saurin janye fuskarta cike da jin kunya da nauyi, ya dan razana tare da fadar “Oh am sorry Ya mike ya ciro hankicif daga cikin aljihunsa ya mika mata. Ta karba ta soma share hawayen ta gama ta miKa masa ya karBa ya mayar aljihu, sannan yace
“Tashi muje ciki, kin ci abinci kuwa?”
Shiru tayi don rabonta da abinci tun jiya don haka ba musu ta mike, suka nufi falon kai tsaye
Suna shiga ta nemi gefen kafet ta zauna bai tanka
‘ba Ya wuce kai tsaye wurin firij din da ake aje kayan gwan’gwani ya bude ya ciro wani qaton cake tare da
~ lemo guda da fresh milk ta kwali, sai chips a wani
Qaramin plate wanda yaji dafaffen kwai da madara
‘ ga shi ya dauki sanyi.
Ya nufo inda Saude take zaune ya ajiye mata a gabanta, sannan yaja gefe ya zauna saman kafet din yana’ fuskantarta, da hannu ya yi mata nuni da taci, ba musu tasa hannu ta dauki milk din ta fasa, ta bade cake din ta rinqa hadawa tana ci. Cake din yayi mata wani masifar dadi don sai tace tunda take “ bata taba cin abu mai dadinsa ba ita kanta tayi
mamakin wanda ta cinye, don chips din kasa cin shi tayi don bata saba cin irin shi ba.
Ta daga madarar ta shanye tas, don sai da taji babu wuri a cikinta, duk abin da take yana zaune yana kallonta tana gamawa ta mike da niyar tattara
kayan, ya daga mata hannu.
“Barshi kawai za a tattara.” Kallon shi kawai tayi sai dai ta gaza magana.
Don haka shi ya katse shirun ta hanyar fadar, “Kije kawai ki huta’, kin’ga kin sha kuka kada kan ki ya yi ciwo, kin ji?’ ‘
Saude ta amsa da to a hankali, sannan ta juya zata tafi hartakai bakinkofa tajiya kira sunanta ta’ waigo tana kallonsa. Tamkar wanda aka matse bakinsa aka ce dole sai ya fadi abin da yake son fada ~ ya ce, “Please kar ki sake yin kukan nan don Allah.”
Saude ta daga masa kai alamar to, yace, “Kin yi alkawari?’ Da kai kawai ta amsa masa, sannan ta . juya ta fice
A yanzu mamaki yake bata bata taba tunanin yana da tausayi da jin Kai irin haka ba, ashe dama yana da kyawawan halaye irin haka ya Boye su, Allah Sarki, ko da yake ai rayuwarta abin tausayi ce ga duk wani mutum mai imani. _ ‘ .
Ta zauna bakin gadonta ta janyo Wayarta miss ‘ call biyar ta gani, ta san kuma duk aikin Hamid ne, ‘ Allah Sarki soyayya. Ta ajiye wayar karkashin
Kanta ta kwanta. Hirarta da shi jiya cikin dare ta dawo mata tamkar yanzu ‘suke yinta, ta yi wani ”murmushi tare da yin wani juyi
. Da safe misalin Karfe takwas ta nufi Bangaren Dr Ahmad da mamakinta yau kwance ta same shi cikin falon Kasa, saman doguwar kujera da News paper a hannunsa yana dubawa, yana sanye da wando three quater wanda ya wuce gwiwarsa sai
bakar singileti a jikinsa. Saude ta durkusa tare da ‘ ”gaishe shi.’
Ba tare daya dago kansa daga karatun da yake ba ya amsa mata gaisuwar. Saude ta mike ta soma aikinta kamar yanda ta saba, sai da ta kammala tsaf sannan ta soma turare falon da turaren wuta, kamar wadda aka cewa dago kanki, karaf su kai ido hudu, ‘gaba daya idanuwansa da hankalinsa ya tattara su a ‘kanta.~
‘ ’Saude taji ta yi wata masifaffiyar tsarguwa, cikin  basarwa irin ta gogaggun maza yayi
mata alamar kira dakansa, jikin Saude ya Kara yin sanyi ita dai ta fara tsorata da irin kallon da yake mata, ba yanda ta iya haka ta ajiye bonar din ta nufl  inda yake ta dan durkusa kusa kadan tare da fadar, _
“Gani‘ Yalla Bai.”. Idonsa na’ kanta kamar mai san karantar wani abu cikin idanuwanta yace“Ya kamata a tsaya da aikin nan haka a kawo mana abun karyawa k0ke baki soma jin yunwa bane?” Yadda ya yi maganar cikin “salon nuna tausayinsa a kanta shi ya ba ta mamaki
Saudat ta sunkuyar da kanta qasa‘ tana kallon yatsun hannunta, sannan ta amsa, da to muryarta a sanyaye, bai tanka. mata ba har ta mike ta fice daga falon, ya koma ya kwanta ya dora hannun shi guda a kan shi ya lumshe idanuwansa komai yake tunani Oho.
Saude ta karBo break din ta kawo da sallamarta ta ajiye masa. tiren kayan abincin a gabansa tare da fadar, ‘Ga abincin. ”
Dr. Ahmad ya yunkura ya tashi zaune ya sauko daga kan kujerar ya zauna a gabanta tare da harde qafafuwa tamkar wani karamin yaro yace, “Zubo mana. ’ Saude tayi saurin kallonsa tana san tambayarsa shi dawa amma kwarjinsa ya hana,
don haka ta sunkuyar da kanta. Ta dauko ‘ plate biyu zata zuba Dr. yasa hannu ya janye dayan yana fadar, ‘Plate guda zaki zuba mana.” Ba ta musa ba ta dauki saving spoon ta , debo soyayyar agada (Plaintain) tare da alalar nama da kwai sai soyayyar nama cikin dankali ta zuba su kowane gefe da gefe a tsakiyar plate din sai ta zuba wata hadaddiyar miya kadan sannan ta tura plate din a gabansa ta rufe kulolin, sannan ta dauki
kofi guda biyu ta zuba kunun madara da gero tasa ‘cokula ta miqa masa.
Dr. Ahmad ya zuba mata manyan idanuWansa da dan murmushi a fuskarsa yace, “Sannu.’ Bata amsa ba saboda yanda ta ji nauyin yanda ya mata sannun,
kamar ba yallaBan data sani ba. . Da kan shi ya matso da plate din a gabanta shima ya matso tare da miqa mata kofi guda na kunun Gaban Saude yayi wata mummunar faduwa ta yi
saurin matsawa tana girgiza masa kai alamar a’a. Dr. ya hade fuska tare da fadar.
“Karbi mana meye haka?” Yanda yayi maganar cikin tsawa yasa ta saurin mika hannu ta karBa.
Ya ce “To sa hannu muci maza.’ Ta yi saurin kallonsa idonta ‘ya ciko da kwalla ta gaza yin magana, Dr.Ahmad ya girgiza kai cikin damuwa yace “Abincin ne ba zaki ci ba shine za kiyi kuka?”
Tayi saurin girgiza masa kai,alamar a’ a Ya kada kai cike da damuwa ya mike ya koma kan kujera ya kwanta ya lumshe idanuwansa ba tare daya yi magana ba. ~
Wani irin abu yayi wa Saude tSaye a zuciya, shin wai ita me ya maida ta ne? Yanzu abincin ma da zai ci sai ya wahalar da rayuwarta a kansa, abin da yake mata ya soma ba ta tsoro. Ji take tamkar ta mike ta
bar masa falon, in yaci ma k0 bai ci ba ruwansa. Bude idanuwansa da’ yayi shi ya katse mata tunanin da
take cikin sanyayyar muryarsa yace “Na takura ki k0? Ki yi hakuri kina iya tafiya kawai. ’ ‘ Gaban Saude ya yi wata irin masifar .faduwa cikin muryar kuka tace“Ka yi haquri dan Allah ’  Ya dauke kansa kafin yace “Aini banyi  fushi ba.” ‘ . . Damuwar data gani qarara a fuskarsa ne ta
Narkar da zuciyarta, ita kanta tana mamakin kanta -. yanda hankalinta ke tashi idan suna tare bata san lokacin da bakinta ya bude ba sai dai taji tana ‘ fadar
“Kayi hakuri yanzu ai zanci.”
A hankali ya dago yana kallonta, ta ta” sunkuyar da idanuwanta kasa, wani takaitaccen murmushi yayi tare da saukowa daga kan kujerar ya zauna gefenta. Da kan shi ya dauko kofin kunun ya mika mata, tasa hannu ta karBa cike da jin nauyi ta soma sha, dadin kunun ya ratsa mata kwanya ashe haka yake da dandano a baki, tun tanajin nauyi har ta dake taci sosai tana cire hannunta yana cire nasa.‘ a
Ta dan zuba masa idanuwanta, ya daga mata gira, alamar ya aka yi? Shiru tayi “ta kwashe kayan ta dawo ta gyara wurin da sukaci abincin sannan ta qarasa inda yake zaune yanacikin karanta
jaridarsa, ta dan durkusa. _ “Zan tafi Yallabai ko akwai wani abin da~ ka keso?” ‘
Dr. Ahmad ya dago da kansa ya kalle ta a nutse~ kafin yace, “Me yasa zaki tafi nan ba falo bane? Me yasa ki ka kasa sakin jiki?” Saude tayi shiru ba tare da ta iya cewa komai ba Dr. ya girgiza kai tare da fadar samu guri ki zauna ina san muyi magana.’ Ba musu ta samu gefen kujerar da yake zaune ta zauna a saman kafet. Dr. Ya wurgar da jaridar kan kujera tare da gyara zama ~sosai ya harde yatsun hannunsa guri guda sannan ya kira sunanta.
‘ “Saudat, kiyi hakuri da takura ki da nake ki daure ki bani labarin ki ina san inji labarin ki na damu da in san wace ce ke kuma meye dalilin kawo ki aikatau maimakon a inganta rayuwarki da ilimi k0 dan kema ki amfanar da wasu a gaba?”
Saude tayi shiru tana tunanin dan abin data sani a cikin rayuwarta, idonta ya ciko da kwalla-ta dago tana kallon shi da sarqaqkiyar muryarta tace
“YallaBai babu komai a cikin rayuwaba sai duhu, . babu abu guda na haske a cikinta, idan ma na samu
to ya suBuce mini. ban san komai a cikin rayuwata ba sai wahala da. Qaskanci,  haka rayuwar tawa ke  tafiya… ‘ Kukan da take riqewa ya soma kwace mata, tasa
hannu tana goge hawayen kafin taci gaba ‘ “Ni dai nasan ance an haifeni ne a garin Katsina, kuma na bude idona a cikinta, don haka na
ci gaba da rayuwa a yanda tazo mini a ciki, “tunda nayi wayo na ganni a: gaban Yayana Rabi’u sai mahaifina Malam Bala, sai kishiyar mahaifiyata Inna Laure da yarta iKilima wadda ake ce mata ‘Yar Baba.’ » A nan ta Iabarta masa gaba dayan labarin rayuwarta har ya zuwa yanzu. Tana gamawa ta kifa kanta a saman cinyarta tana kuka. Tausayinta ya qara kama Dr Ahmad wanda yake jin tamkar ya”. zubar mata da hawaye, ya tausayawa halin data ’ tsinci rayuwarta tun tana yar karamarta har girma ta mallaki hankalinta, amma Inna Laure ba zata bar ta haka ba wannan wace irin macece? ‘ ; Ya kira sunan ta cike da damuwa yace.“Kiyi hakuri Saudat insha Allahu sai kinyi,alfahari da rayuwarki ni zan maye miki gurbin Yaya Rabi’u da kuma Hamid in dai ina numfashi. Saudat sai kinyi ‘ dariya da farin ciki kamar kowace mace, ki kwantar”da hankalin ki ki daina kuka haka kinji?” ‘ _ Kai kawai ta daga masa alamar eh ya zaro ~ hankicif cikin aljihunsa ya mika mata ta karBa ta’ share hawayenta sannan ta mika masa ya karba kafin yace, “Yanzu ki tafi kije Ki kwanta  1page is missing Yace to shi kenan,‘kidan bani lokaci zan danyi tunani a kan matsalarki kafin. in “ samar miki mafita da fatan‘dai ba zaki yi fushi da;
Duk abinda rayuwa ta sake baki ba zaki karba da hannu biyu
Saude ta daga masa kai alamar eh yace to allah ya kaimu
Jin yayi shiru yasa ta miqe ta nufi hanyar fita har takai bakin korar taji ya kira sunanta ta waigo tana kallonsa yace ki kawomin coffe yau  da daddare kai kawai ta daga masa ta juya ta fice abinta koda ta koma bangarenta ruwa kawai ta watsa ta koma ta kwanta a binta wani barci ya dauketa ba ita ta farkaba saida wayarta ta dameta da qara tasa hannu ta dauka cikin magagin barci  jin muryar hamid yasata saurin watstsakewa daga baccin suka shiga hira sunfi awa biyu a haka sannan sukai sallama da niyyar zai qara kira zuwa anjima misalin qarfe goma daidai saude ta fito daga bangarenta ta fita kai tsaye kichin ta nufa ta dauko flasks din coffe da qananun kofinan da yakesha dasu ta nufi bangarensa dasu saidai tun kafin ta qarisa ta hango bangaren nasa dun dum babu alamar hasken wuta tsoro ya kamata gashi bata taho da wayartaba ballentana ta haska kuma babu damar ta koma
Wayyo allah taji tamkar ta fashe da kuka
Taja ta tsaya cak tana tunanin abinyi tun kafin ta
Qarasa nazarin taji wani haske mai Karfi ya taso da saukar ruwan sama mai Karfi  ai bata san lokacin data kwasa da gudu ba tayi Bangaren nasaba gashi duk ta jike Tamkar daga sama taji ta yi tuntuBe da wani abu  ta fasa wata uwar qara ta saki kayan ta kwasa a guje, karaf sukai kicibis  da mutum, ta sake kwala wani qara mai qarfi cikin dabara ya rungume ta sosai a jikinsa yasa  hannu ya kunna wutar falon. Amma har a lokacin ‘ ihu take tana, zullon kwacewa, hannu yasa ya
tallabo qeyarta ya juyo da fuskarta saitin tasa su kai
ido hudu. Sai Alokacin ta tsaya da ihun ta saki wata _
. ‘ nannauyar ajiyar zuciya cikin muryar kuka tace ‘Wallahi ka tsorata ni na zata, na zata… ’sai kuma tayi
Shiru Yanda take maganar a shagWaBe ya burge shi har bai san lakacin da ya saki wani murmushi ba yasa dan yatsunsa ya lakace mata hanci yana fadar, . “You are so beautiful Ya lumshe idanuwansa tare da mata wani murmushi,wadda ta tsaya iya makoshinsa kawai
‘ Sai a lokacin Saude ta lura da irin rikon da yayi mata tayi saurin zame jikinta da nashi a kunyace saboda yanda ruwan. ya jika kayanta duk suka mammanne a jikinta tamkar ba tasa komai ba ta juya da gudunta ta bar falon tana ji yana kiranta amma bata tsaya ba, haka ta koma sashin nata cikin ruwan. ‘
Tana shiga ta hada kanta da bangon falon tana jin tamkar qasa ta tsage ta shige ciki, saboda kunya da nauyi. Ai k0 ba za ta sake yarda su hadu ,ba duk rintsi kai dole ma in bar gidan. nan, wannan abun ” kunya har ina, musamman idan‘ matar gidan ta samu labari ai ita ta san ta kade har ganyen ta. Kunya ta isheta tarinqa jin tamkar tarusheda kuka.
Ta samu ta yi ta maza ta cire kayan ta dauko tsohon zaninta tayi daurin Kirji da shi ta haye kan ‘ gadonta ta ja bargo ta kwanta. Amma sai me? Data rufe ido sai taga tamkar ga Dr.Ahmad  zai rungume ta, ta zabura ta tashi zaune tana muzurai, ga qamshin turarensa daya mamaye ta, ta yi wani gajeran murmushi tare da komawa ta ‘kwanta: ta runtse idanuwanta a haka bacci mai nauyi ya dauke ta. Washe gari tunda ta farka take zaune tana san
zuwa wurin aikin nata, amma kunya ta hanata,ji ‘ take ba za ta iya sake hada ido da shi ba,
bata san tsawon  lokacin data dauka a zaunenba sai data soma jin cikinta na kukan yunwa, ta daga kanta ta kalli agogo. Sha daya da mintina, tana shirin tashi zaune taji an turo Kofa an shigo. Tayi saurin tashi tana fadar, “Sannu Aunty.”.
Ta amsa da “Yauwa Saudat lafiyadai ki kek0?” Saude tace “To da sauqi dai kaina neke dan ”ciwo.” ‘ .
Tace, ‘Ayya, Allah Sarki kije Hajiya na neman ki tana falo.”
Gaban Saude yayi wata mummunar faduwa, tace, ‘Lafiya dai k0 Aunty? Allah yasa ba wani laifl nayi ba.
‘ Aunty tace “To laflya, YallaBai ne ya aiko kiranki.’ _  Hankalin Saude ya Kara tashi alamun tsoro ya . bayyana karara a fuskarta, ta mike jiki amace tana fadar, “Gani nan zuwa.”
Cikin sanyin jiki ta canza kayan jikinta sannan ta fito zuciyarta na faman bugun dardar  harta qarasa .falon ta hango’Asma, tsaye riqe da Kugu, tana sanye da wasu riga‘da siket  sari tare da ‘mayafinsu tamkar wata .Ba’indiya, takalmin nan mai shegen tsini a qafarta.
TA danyi nesa da ita Saude ta tsaya ta durkusa tare ‘ da fadar, ‘Ina kwana Hajiya.” .
Asma ta watso mata wani razanannan kallo kafin tace ‘Shut up ke nan har marar kunyace wace ce ke? Uban waye uban ki a garin nan da har za kiqi zuwa aiki saboda jin dadi har Dr. ya aiko kiran ki, me kike ji da shi a cikin gidan nan? Me kika taka’?
, Banza sakarya jaka‘ yar qauye.
Yau k0 rashin lafiya kike dole zaki sanar inba daibakisan inda kankiyake ba, tunda an ajiye miki wayar tarho da zaki iya kira da ita ki sanar, amma ke isasshiya kin yi shiru abinki wato idan ana so a nemeki toki -sani wannan shi ne laifinki na biyu cikin manyan laifukan da ki ka aikata a gidan nan duk ran daki kikai na uku,kisani aranar”zakikarbi takardar sallamar ki kinji na fada miki” Tana gama fada ta juya ta haye sama a zafafe
Jikin Saude yayi sanyi matuqa, ta lallaba ta mike ta fice zuciyarta a cunkushe da baKin cikin yanda aka wulaqanta ta ba tare da an saurari uzurinta ba.
Rayuwa kenan ,
Haka ta sa kai ta shiga falon tare da sallamar’ta, tsaye yake tsakiyar falon ya goya hannayensa a baya yana jin sallamarta yayi saurin waigowa ya nufo ta da hanzarinsa
Lafiya Saudat meya same ki? Ba dai ruwan jiya  ne ya saki zazzaBi ba?”
Saude ta girgiza kai alamar a’ a, sannan ta durkusa tana gaishe shi, bai iya amsawa ba ‘ ya sake jefo mata wata tambayar
‘Ban yarda ba Saudat idan lafiyarki qalau me yasa yau baki zoba?”
Saudat ta Kara dukar da kanta qasa tare da fadar, ‘kaina ne yake ciwo kadan shi ya sanya.’
Dr. ya ce ni dai na sani, :nasan baki da da lfy Saudat bari in kira likita ya duba ki, kin ci abinci ‘ ‘ kuwa? .
Da sauri tace ai na warke.
Dr ya. girgiza mata kai a’a Saudat ban san wasa da lafiya, taso kici abincin kafin yaz0.
Ganin yana shirin riko hannunta yasa tayi saurin tashi da kanta tabi shi ya nuna mata tsakiyar kafet ta’ zauna sannan ya nufi dining ya dauko kayan abincin ya kawo mata, yau da kan shi ya zuzzuba mata ya tura mata a gabanta tare da fadar. ,
‘Don Allah ki daure kici.”
Kai kawai ta daga masa, sannan ya wuce ya dauki wayarsa ya kira likitansa. Yana cikin wayar ne Asma ta sawo kai falon tana wani taku sai kace wadda  take filin. gasar iya tafiya, Dr. ya zuba mata idanuwansa cike da tuhuma. ‘
Karaf idonta ya sauka kan Saude wadda tuni hanjin cikinta ya shiga juyawa saboda tsananin
firgita da tashin hankali, Asma taja ta tsaya tana ,fadar.
“Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce kecin abinci a food flask dinka, kam babban ……. ’

Wohoho jama,a akwai rikici fa mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin yaddah zataci gaba da kayawa
Naku har kullum
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKEN ZAZZAU*

About AIS

Check Also

Yar tallah32

           *YAR.    TALLAH*                *CHAPTER32* Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana tirje~tirje da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *