[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
*YAR TALLA*
*CHPTER15*
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]
gobe qarfe biyar na yamma, ina da taro a Hotel sai na dawo.” Ta juya ta fice abin ta babu maganar mayafi
Matar ta mikawa Saude wata leda tana fadar, “Wadannan su ne kayan da zaki saka.”
Saude tasa hannu ta karbi kayan jikinta a sanyaye.
Matar ta yi wani takaitaccen murmushi tana fadar, “Ya naga farawa da iyawa har kin yi la’asar, haba Saudat kar ki karaya mana ki batawa Hajiya rai ki dauke ni a matsayin Auntynki ki yarda da abin da zan fada miki, ki sawa zuciyar ki zaki iya abin da aka saki da kuruciyar ki ai babu abin da zai gagare ki-Maigidan ‘mutum ne mai saukin kai yanayin rayuwarsa irin ta Turawa ce idan dai ki ka nutsu komai zai zo miki da sauki, kinji?”
Saude ta daga mata kai alamar eh sannan ta karbi kayan ta koma Bangarenta ta fada kan gadonta da. kayan zuciyarta na barazanar
fashewa.
Tsawon Iokaci ta dauka tana saka da warwara, , sannan ta yunkura ta tashi zaune ta zazzage kayan daga ‘cikin ledar tana daddagawa. Suite ce baKaKe riga da siket sai ta cikin fara, ta tsaya tana kallon
kayan sun burge ta sosai, ta linke su ta maida a leda.
Ta yunkura ta sauka daga kan gadon ta janyo abincin da Aunty ta kawo mata ta bude
Tuwon shinkafa ne da miyar agushi, Saude ta zauna ta ci abincinta sosai ta gama ta mike tayo alwala ta dawo ta yi sallah sannan ta koma ta
kwanta.
Sai dai fargabar da ke zuciyarta babu abin da ya canza yinin yau haka ta yi shi, ba kuzari a jikinta tana tsoron abin da zai iya faruwa idan ta kasa yin abinda Asma ta sanya ta bata san irin hukuncin da zata yanke mata ba qila ma ta iya kashe ta kawai.
‘Zuciyarta ta kara tsinkewa wasu irin hawaye masu zafi suka taru a idanuwanta, watakila ajali ne ya kawo ta gidan, tasa hannu ta goge ‘yar kwallyar da ta tarar mata ta juya daga gefen da take ta lumshe idanuwanta, amma ba barci take ba.
Washe gari Saude na zaune a qasa gefen gadonta, tana tunanin da ya zame mata jiki, zuciyarta ta lula duniyar tunanin Hamid da irin kulawar daya bata a rayuwa. K0 a yanzu ba ta fidda rantaba tana ji a jikinta za ta koma gida ta same shi, tana ji a jikinta shi ne mijin da zai aureta suyi rayuwarsu cikin kulawa da Kauna.
Aunty ta turo kofa ta shigo tare da sallama, Saude ta bude idanuwanta tana amsawa. Aunty ta tsaya daga bakin kofa tana fadar, “Ya na gan ki anan zaune, k0 kin manta ne yau ne ranar da aikin ki zai soma?”
Saude ta kalleta tace Na sani Aunnty ba tace sai Karfe
biyar ba?”
Annty tayi wani takaitaccen murmushi kafin ta ce “YallaBai ya yi tafiya zuwa qasar China sati ukun da suka wuce, don haka yanzu zaki tashi ki fara gyara masa Bangaren shi ki zauna har ya iso.” Ta wurgowa Saude makullai tana fadar, “Ungo
wannan sune makullan bangaren sa.”
Saude ta cafe lokacin da bugun zuciyarta ya tsananta, Annnty ta juya tana fadar, “Ki tashi ki shirya ina falo ina jiran ki na raka ki Bangaren nasa.”
Saude ta taKarKare ta mike ta nufi bandaki ta dade a tsaye zuciyarta na faman kaiwada komowa, sannan ta daure ta watso ruwan ta fito, ta zauna bakin gadonta ta ciro kayan daga cikin ledarsu ta sanya kamar yanda Aunty ta nuna mata, ta mike tsaye siket din bai Karasa isowa kasa ba ya dai wuce gwiwoyinta, sannan ta janyo hijabinta ta sanya sannan ta kawo takalmin da ke cikin kayan ta saka wanda yake sawu-ciki, sannan ta fito ta samu Aunty zaune tana jiranta tana fitowa suka jera suka fita. ~ ‘
Gaba daya suka fita daga wannan shashin, suka . nufi daya Bangaren wanda ke hagu. Aunty ta karBi makullin ta bude sashin suka shiga, komai na sashin irin na wancan ne, babu abin da ya bambanta. Aunty ta mika mata makullin tana fadar.
“Ga shi ki goge komai ki gyara,idan kin gama. Ki zauna har ya iso, daya iso ki karbi jakarsa ki kawo masa abu mai sanyi kin ji?“ Saude ta daga mata kai ‘ alamar eh.
Sannan ta juya ta tafi ta bar ta tsaye tana faman bin katafaran falon da kallo. To ta ina ma za ta fara? Ita dai a iya ganinta ba taga abin da ya yi datti ba, ta taBe baki sannan ta fara takawa saman matattakalar ‘ ‘ benen ta shiga cikin falon, kai tsaye wani qaton falo ne ta fara shiga wanda, har yafi na farkon haduwa da tsaruwa.
Idanun Saude suka sauka saman wani makeken hoto wanda yake jingine a kasan gefen bango, ta danci gaba da bin hoton da kallo. Wani kyakkyawan namiji ne ajin qarshe wanda shekarunsa ba zasu‘ wuce talatin da biyar ba, kallo daya za kai masa ka tabbatar ya hadu tamkar wani Balarabe, yana rungume da Asma suna murmushi’su duka, sunyi masifar kyau, amma duk kyan Asma bata kai mutumin ba, duk da yana namiji, don shi kalar kyansa yafi kama dana Larabawa saika rantse Balaraben Saudiyya ne
Saude ta wuce a hankali ta shiga zagaye falukan sashin da bedroom din dake ciki, ita kanta tana ,tausayin kanta saboda sashi~sashin dake ciki sun kai
goma, haka ta dauko mofa da tsintsiya da tawul da .bokiti ta fito ta shiga gyaran sashin,‘
Sai da ta gyara ko’ina da ina ta goge tare da kunna bona bonar da ke falukan kowacce ta zuba turaren ‘wuta a ciki, sannan ta dauki room fresner ta dinga feffesawa a ko’ina da ina, ta Kara gudun A.C sannan ta rurrufe ko’ina kamar yanda Aunty ta fada mata, ta dawo falon qasa ta zauna gefen kujera tana faman zare na mujiya, sanyin A.C na ratsa ta. A take tamkar ta kwanta saboda tsabar gajiyar da tayi.
Misalin Karfe biyar da ‘yan mintina Saude ta ji an turo Kofar falon ta zabura ta tashi tsaye kirjinta na wani masifar bugawa da qarfi da qarfi. Shi daya ne ya shigo yana sanye cikin shigar Kananan kaya, sai wani yaro dake bayansa wanda ke sanye da suit, yana rataye da irin jakar ma’aikata.
Ahmad ya tsaya yana watsa mata wani irin kallo
wanda ya Kara hautsina mata‘ yan hanji, muryarta na rawa ta fara fadar, ‘Sannu da zuwa
‘ Shut up! You are very stupid, get the hell out of here
Jikin Saude ya hau Bari ko’ina na jikinta rawa yake ga shi dai ba ta san tsiyar da ya fada ba, amma yanda ya kwatsa mata tsawa, ya tabbatar mata da korarta yake don haka jiki na Bari ta gifta zata wuce, Ahmad ya kara daka mata tsawa.
“Wait, nace ki tsaya.”
Saude ta ja ta tsaya, sai faman kyarma, take, don yanda ta ga tsantsar Bacin ransa ta tabbatar zai iya
kai mata duka cikin bacin rai yace hope baki dai hau min sama ba?”
Saude ta yi shiru tana faman rawar murya, yaja wani dogon tsaki ya wuce ciki, jikin ta yana rawa ta wuce, sai faman harde qafafuwa take, har tabar falon.
A tsaye ta samu Asma sanye da wata doguwar riga milk colour, ta dora dan qaramin mayafi saman kanta wanda ya tsaya iya wuyanta, gilas dinta yau a hannu yake tare da makullin mota da alama fita za ta yi.
Saude na shigowa ta tsaya tana kallonta, cikin tsantsar takaici take kallonta, jikinta ya qara yin la’asar tana shirin dukawa ta gaishe ta taji saukar wani mahaukacin mari’ har sau biyu, dama da hagu,
wanda yasa sai da ta kifa cikin takaici Asma ke fadar.
“Ashe ke dakikiya ce ban sani ba sakarya, jaka Dube ki, dubi abinda ke jikin ki, yanzu da wannan bakin abun kika shigar masa ko? Oh! Kin gama dani, amma kin ci sa’arsa da ya kyale ki da kin gane baki da wayo, don na tabbatar yau k0
‘ ruwa ba zai iya hadiya ba.” Ta ja tsaki mts! Ta juya ta dubi Aunty wadda ke« tsaye tace, “Rabi maza ki debo mata kayan shafawa da turarurruka, ta cire wannan bakin abin ta shirya, ki tabbatar ta koma ta ba shi hakuri, kuma Wallahi
idan ki ka sake yaqi amincewa daki zama ‘yar aikinsa na rantse miki sai kin fuskanci fushina kinji na rantse.” Ta’Karasa maganar da karfi, sannan ta juya ta yi gaba abin ta.
Wasu irin hawaye masu zafi suka biyo kuncin Saude, wayyo Allah wannan wace irin rayuwa ce ta samu kanta a ciki? Anty ta dafa ta muryarta a . sanyaye. .
“tace kizo muje, kada dan wannan abun
ya razanar daké, na san za ki iya yin abin dama yafi wanda aka saka ki, idan dai har kin sawa ranki zakiyi, za kiyi Saudat, please zo muje.” Saude dai ba ta tanka mata ba ta juya ta bi ‘ bayanta suka nufi wani sashi daban, ta tura wata ‘» kofa sai ga su sun fada wani dan falo irin na ‘ Sauden. ‘ Aunty ta bude wata loka da ke jikin bango saiga kayan kwalliya kamar su ci kansu, ta dauko leda ta dibar mata masu yawa, tun daga man shafawa, sabulan wanka, kayan kwalliya har da turaruka, sannan ta bude wardrobe ta ciro dan qaramin hijabin nan mai tsayawa iya wuya wato himar kalar ja ta
mika mata tana fadar
“Ki yi sauri ki je ki gyara ki tafi, dan na san yanzu haka akwai abubuwa da dama da yake buqata.” Saude ta karBa ta fice jikinta amace.
Sai data sake wani wankan sannan ta fito ta shafa mai a jikinta ta kawo wata ‘yar qaramar powder fara ta shafawa fuskarta, tasa man lice a bakinta, sannan ta mike ta mayar da kayan jikinta, ta dauki qaramin hijabin ta rufe kanta. Wani irin abu ya cunkushe mata zuciya, tunda take a duniya bata taba irin wannan shigar ba ace kana dan Musulmi amma ka fita a haka, kai duniya! Takaicin kanta ya kamata, k0 tsayawa ta dubi kanta ba ta iya ba ta dauki turare ta fesa guri uku kawai sannan ta fice zuciyarta na faman kai kawo.
Tsoronta ya qara tsananta lokacin da ta iso bakin sashin nasa ta daure ta yi ta maza ta sa kai cikin falon cike da fargaba. Turus! Ta ja ta tsaya ‘yar sallamar da take shirin yi ta makale mata a makoshi,
wani irin tsoro da fargaba mai tsanani suka dirar
mata Kwance yake tsakiyar falon saman kafet ya yi
daidai. daga shi sai gajeran wando bak0 singlet jikinsa, yayi matashi da hannayensa fuskarshi na kallon sama, idanuwan shi a lumshe suke kamar mai barci.
Saude ta runtse: idanuwanta da ’tana shirin ta juya da sauri ta-«koma sai kuma ta tuna
Da
maganar Asma da take fadi“Wallahi idan kika sake
Yaqi amincewa dake a matsayin yar aikinsa sai kin fuskanci fushina. ”
Hmmm YA abin yakene Mu tara gobe daidai wannan lokacin DONJIN yaddah wannan taqaddamar zataci gaba da kayawa Naku har KULLUM
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
[Advertisements⬇️]
[Continue Reading⬇️]