[Advertisements⬇️]

Yar tallah12 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

               *YAR   TALLA*

                *CHAPTER12*

       *ASHA KARATU LAFIYA*

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Tana kallonshi sai faman sosa gemu yake wanda ke _ faman yi masa kaikayi duk yayi wani quda~quda da alama ba za a rasa kwarkwata a cikin saba, saboda tsabar qazanta da kurar duniya daya sha. Saude ta dame zuciyarta ta amsa masa don k0 kadan ba tajin za ta iya yi masa wulaqanci saboda girman shekarunsa dan yayi jika da ita.
Garba ya Kara watso haqoran nan wadanda su kai kore fatau kamar gansa-kuka yana fadar, “Haba Saude na ga alamar kamar bakisan magana dani, kiyi hakuri ni masoyinki ne ba makiyinki ba kuma ni aurenki zanyi bawai wasa zaikawoni wurinkiba yanzu haka idankika amince min mahaifinki kawai zan nema a yi magana.”
Saude ta watsa masa wani irin  kallo mai kama da harara ta zumburo baki kafin tace, “Ni fa ba aure zan yi ba yanzu
Ya yaqe baki yana fadar, “Haba Saude ke yanzu idan bakiyi aureba saime zakiyi?idan ki ka amince: ki‘ka aure ni, killa ceki zan yi a‘gidana, kin gama zuwa talla idan ma kina tunanin matana hudu ne to a shirye nake dana saki daya daga cikinsu Ya kikacene Saude?” ’ Haushi ya kamata ta mike afusace tadauki bokitin tallarta tayi gaba tabar shi nan zaune
Garba Gurgu yayi dariya yana girgiza kai yana fadar‘ “Yaro yaro ne.” Ya mike yana cangala qafa shima yayi gaba abin sa.
Bayan Saude ta gama tallarta da yamma likis ta koma gida a gajiye ta samu taci abinci tayi sallar Magariba, sannan ta dauki tallar dare ta fita kofar gida ta zauna da ‘yar fitilar aci-balbal.
Kamar daga sama ta hango shi tsangal-tsangal haushi ya cunkusheta ta hade fuska a zuciyarta ta kudiri aniyar idan ya sake yazo inda take saita cire kunyarsa daga idanuwanta ta yi masa rashin kunya tunda ta lura bai san girmansa ta gani bata daga masa kafa ba
Da mamakinta sai taga ya yiwa kofar gidansu tsinke, ta saki baki da idanuwa tana kallon shi, taga ya kira wani yaro ya tura shi cikin gidansu. Yaron bai jima ba ya fito tana kallon su can sai taga mahaifinta ya fito sun tsaya suna gaisawa, gabanta ya yi ’mata mummunar faduwa hankalinta yayi masifar tashi ba dai Garba wurin mahaifinta ya zoba.
Wayyo Allah na shiga uku! Abin data iya fada kenan wasu zafafan hawaye suka shiga zarya a kuncinta tana kallon yanda mahaifinta keta faman
washe baki yasa hannu ya karBi kudin da Garba Gurgu ya bashi, sannan suka sake yin musabaha, sannan ya shiga gida shi kuma ya wuce abinsa ba
tare da ya kalli inda take ba. Saude  ta kwashi kayan tallarta ta nufi cikin gidan. A tsakar gida ta samu mahaifin nata na fadawa
“Laure kinga wani abun murna k0 wai mutumin nan Garba Gurgu ke son Saude
Laure ta rannngada kuda tace, “Kai amma abun yayi min dadi wallahi, kaga sai a hada su su duka da ‘Yar Baba. don ita ma tace yaron nan mai zuwa wurinta da jar motar nan yace zai turo ai maganar aure
Malam Bala yace, “Ai ko haka za ai dama nina amsa masa, yanzu haka yace jibi za a kawo kayan nagani-inaso yanzu haka har kudi ya bani kin gansu dubu biyu. Kai gaskiya mutumin nan yana da mutunci.”
Laure tace“To, ai sai ka tsakuro mini nawa tunda ba kai kadai keda diyar ba
Malam yace, “Kefa tsiyarki ke nan duk abin ki ai kya bari’ na mutu sannan kyai rufe ni ai k0?”
Yaja tsaki ya cimimiyo kwarar dubu guda ya cilla mata ya juya zai tafi ya ga Saude tsaye rungume da kayan tallarta hawaye sun gama bata mata fuska.
Malam yace, “Ke kuma fa lafiya?”
Cikin muryar kuka Saude tace “Ka yi haquri Baba don Allah wallahi bana sonshi ba zan iya aurensa ba,sabo…
Malam ya katse ta ta hanyar fadar, “Ke dalla Saurara mini kin jiki Ba kya son shi sai wa kike so?”
Saude tayi shiru tana faman shashshekar kuka Malam ya sake fadar “Nace idan ba kya son shi, sai ubanwa kike so?Munafukar Allah,nankikaso ki jibge mana kita zama kitsufa a tasha kina talla, tunda kebaki da tunani ko,
Allah yataimaka kemaya kawo miki dauki, tunda kika tashi akwai bakon takalmin daya taBa zuwa wurin ki da sunan so, iye?
Amma shine har kina da bakin magana. Shekarar ki nawa yanzu a duniya? Kin zauna kin jibge babu mai taya ki kek0 kishin kanki ba kya yi, kina kallon ‘yar uwarki kullum wannan ya shiga wannan ya fita, harda masu motoci, amma saboda rashin kishin kai baki taba damuwa ba.” mtwwws! Ya wuce yana fadar.
“Idankinada wanda kikeso to saikituro shi ai lokaci bai qure miki ba daga nan har ranar daurin aurenki
Wani irin kuka ya Kara kwacewa Saude, ta aje kayan tallar tayi dakinta da gudunta tana. wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Laure taja tsaki ta tattara kayanta tana fadar, “Ke
dai kya kai su idan kaya ne dan  bakin ciki  sai dai ya kashe ki don, na gaba ya riga ya yi gaba har abada ba zaki iya kamo taba.”
Saude ta sha kukanta har ta godewa Allah bata . da mai lallashinta haka ta kwanta har bacci barawo ya sure ta. Haka ta farka yau idanuwanta duk sun ‘ kumbura sun yi jawur saboda kukan da ta sha jiya. Haka ta je tallanta ta dawo jikinta ba kuzari kana ganinta ka san tana cikin matsananciyar damuwa. Tayi zaman daBaro kan sumuntin tsakar dakin, don
kuwa dakin bai da arzikin k0 qaramar tabarma
Saude ta jingina da bangon dakin ta rafka wani ; uban tagumi ko tunanin me take Oho ‘Yar Baba ta dago labulen tana mata wani shakakken kallo kafin
tace
“Idan kin gama tagumin sai ki fito ga kayana Na hada ki wanke mini. ‘
Saude ta dago da jajayen idanuwanta tana « kallonta, haushi da baKin ciki suka turnuqe mata zuciya, tuni dama batun yau take jin takaicin abinda ‘Yar Baba ke mata ba sai kace itace babbar, sannan ita kuma  karama.
‘Yar Baba tace, “Kika tsaya kina kallona da wasu kananan idanuwanki can masu kama dana kwarkwata kixo ki min wanki nace
Takaici ya kuma turnuke Saude cikin fusata tace, “Wai ‘Yar Baba me kika dauke nine jakar ki ko
kuma me? Karfa ki manta a girme na girme ki,amma ki rinka! yi min abu kamar wata yarda kika haifa. Ai ba ‘yar wanki ki ka aje ba, da kikaga
dama can ina miki Inna ce ke sani, amma ke baki isakisani inmiki wanki ba” “
‘Yar Baba tace ‘Eh, lallai wuyanki ya isa yanka, harni kike gayawa magana yau k0 Saude dan kin ga Laure bata nan lallai zaki san kin yi da diya ba shegiya ba, za ki gani.” Ta juya ta yi gaba.
Saude taja tsaki ta IaIIaBa ta kwanta taci gaba da nazarin abindaya dameta. Bata ankaraba saidai taji saukar kayan wanki a jikinta ta zabura ta mike tana kallon mai wannan aikin.
0000hooo
“Wato kenan har kinyi girman da ‘Yar Baba zata sanya ki kiyi mata abu ki zage ta kice ba zakiyi ba.
‘ To yau sai na ga uban daya ,tsaya miki ki daukesu maza kije ki wanke mata, ki shanya ki zauna su bushe ki linke ki kai mata daki, tantiriya marar kunya, ai na godewa Allah morewa ta dama naga rayuwarki ta wulakanta, kuma nayi nasara, in dai ina numfashi kin auri Garba Gurgu kin gama, bankadaddiya yanda na ga bayan uwarki da wannan
takadarin kema sai naga naki. ’
” Taja tsaki ta wuce tana fadar. “Munafukar banza!” .
Wasu irin hawaye masu dumi suka zubo daga idanuwan Saude tasa bayan hannunta ta goge sannan ta’ shiga tattara kayan wankin ta wuce tsakar gidan,
Ta. wanke su gaba daya abun bakin cikinta har da bireziya da dan pant, saboda kawai tsabar raini da wulakanci. Rayuwa kenan.
Kamar yanda mahaifinta yace za a. kawo kayan nagani-inaso, haka kuwa aka yi Garba Gurku ya aiko mata da kaya cikin Gari yayi zafi, dinkakkiyar atamfa ce ta roba riga da zani sai dakakkiyar abaya kwaya daya, sai takalmin roba shi ma guda daya da sinqin sabulu guda da Katuwar ’kwalbar mai da dangwali -yaBa, sai naira dubu a sama.
Laure ta dauki naira duban sannan. ta mikawa Saude kayan don ba abin da yayi mata a cikin kayan. Wasu irin hawaye masu zafi suka ziraro daga idanuwanta tasa hannu ta karBi kayan ta wuce daki ‘ dasu.
Tana shiga ta wurgar dasu tsakar dakin ta durkushe tana raira wani sabon kukan mai cin zuciya. Tabbas tana cikin halin daya kamata a tausaya mata,Yayanta ya ringa yi mata gizo cikin idanuwanta ko wane hali yake yanzu oho? Saude ta sha kukanta ta gaji ta lallashi kanta ta yi shiru
Abu wasa-wasa lokaci yaci gaba da tafiya, Garba Gurgu ya ci gaba dayi wa Saude hidima, idan abun kirki ne sai Laure ta rike, idan kuma ta gajam tagajan ne  saita bata, ita k0 bata taba kallon kayan ba don yanda ta tsani mai kayan haka suma kayan ta tsane su.
‘ Ranar: wata Laraba Saude ta dawo daga tallar safe, misalin qarfe daya na rana, Laure tace yau ba tallar rana taje ta shirya za taje ta dubo ‘yar Garba Gurgu data haihu ta dawo gida wanka jiya yazo ya gayawa Malam.
Wani bakin ciki ya tokarewa Saude wuya, ta rasa ma abin da za tace saboda takaici, ta wuce dakinta ta yi kwanciyarta, har aka soma kiran sallar La’asar, Laure taji shiru ta leko dakin nata ta ganta a kwance idonta biyu k0 motsin kirki ba tayi.
Laure ta dauki sallallami tana fadar, “Yanzu zuwa ki kai kika kwanta dan kin raina mutane,? yayi miki dadi sosai wallahi. To sai ki fito ki shirya in ga ubandaya isa ya hanaki kije dubiyannan ki ciro cikin kayan da yake kawo miki ki sanya kinji na gaya miki”inba hakaba yanxu jikinki zai gaya ‘miki wallahi Tana gama fada ta juya ta wuce abinta.
Wasu irin hawayen bakin ciki suka zirarowa Saude ta yunkura ta mike jikinta ba kwari, ta fito ta janyo ruwa cikin rijiya ta dauko sabulu guda cikin kayan nasa daya kawo mata ta nufi bandaki tayo wankanta wanda rabon da tayi irinsa ba zata iya tuna shekarar ba.
Tana gamawa ta fito ta nufi dakinta ta janyo mai ta shafawa fatar jikinta, ta zazzaga farar hoda a hannunta tamurzawa fuskarta, ta bude ledar da kayan ke ciki kala uku .ne daga wata atamfa ‘yar
roba sai wani yadi mai santsi anyi masa dinkin riga da wanda, sai wani leshi marun an masa dinkin jaka tsaye.
Saude ta dauko shi ta saka ta Ciro takalmin robar
ta sanya ta kawo milk din hijabin da ke cikin kayan
ta sanya, sannan ta fltO zuciyarta na faman suya. A lokacin Laure da ‘Yar Baba na zaune gaban murhu
ana ta faman soyen kajin da saurayin ta ya kawo
Saude ta dubi Laure da idanuwanta wadanda suke san zubar da hawaye tace, ‘Na fito.”
Laure ta dago tana kallonta, alamun mamaki bayyane a fuskarta qarara, wanda har ta gaza danne shi a zuciyarta sai data furta. Tace
“Saude kece haka? Dube ta ‘Yar Baba kiga abun mamaki.”
‘ Kallo daya ‘Yar Baba ta yi mata ta dauke kanta tare da jan tsaki, Laure ta kada kai kafin ta ce, “To sai ki tafi k0wa kike jira?”
Haka Saude ta kama hanya jikinta a sanyaye ta yi. gaba. ‘
‘ Gidan Garba Gnrgu yana can qasan unguwarsu ne ta baya, haka Saude ta taka~ da qafa. Gidan qaton gida ne ginin qasa,~rabin katangar duk ta zube a Kasa
wanda aka sa buhu aka zagaye. Saude tasa qafarta cikin dogon zauren wanda aka fito da Katuwar kwata ta tsakiyarsa har tsakar gidan,
gaban tane ya shiga faduwa lokacin data sa qafa cikin soron gidan, bata san irin tarbar da za a yi mata ba, ta san mugunta ce kawai tasa Laure ta ce tazo gidan ba wani abu ba. Saude ta yi sallama a tsakar gidan wanda yake a hargitse sai ka rantse da Allah bai’taBa ganin Shara
ba ga wasu manyan tukwane da murahu a tsakiyar tsakar gidan ko’ina komatsai ne a tsakar gidan ba masaka tsinke, ga yara nan suna ta faman tsalletsallensu a tsakargidan sai kace basu taba ganin ruwa ba a rayuwarsu saboda tsabar Kazanta.
Saude ta Kara daga murya tana sallama sannan matan dake ta faman zirga-zirga suka ankara da ita aka amsa mata tare da . yi mata maraba, jikinta a sanyaye ta qarasa cikin, gidan tana danne fargabar zuciyarta.
Daya daga cikin matan ta janyo kujera ‘yar tsugunne ta miqa mata ta zauna suka shiga gaisawa, wasu su biyu babu riga a jikinsu sun saki nonuwa a waje sai kace silifas suna ta harkokin su babu abin daya dame su, sai Karamar suce keda daurin qirji. Kai da gani ka san anyi masu kisan Kuli, an kashesu ko kadan baza akirasu da mata ba.
Saude ta kakaro wani murmushi wanda iyakarsa saman laBBanta kafin tace, “Nazo ganin jariri ne.’
Babbar cikin su tace, “Au! Ni dai nace bamu. ,
waye kiba, suna daka ki shiga ki gansu.”
muyi kishi da jikannu wallahi, bata yiwuwa da sake an bawa mai kaza qafa”
A daidai nan Saude ta fito tana qokarin sa takalmanta taji matar na fadar, “Munafuka ashe Ieken asiri kika zo in dai gidan Malam ne ki shigo kema ki zauna, sannu a hankali zaki koma yanda muke ”
Sauran matan dai babu wadda ta tanka, harkar gabansu kawai suke. Saude tasa takalminta dai tayi waje, tana jin Garba ya biyo ta yana fadar.
“Tsaya Saudatu kiga dakin ki.”
Bata tsaya kulashiba tayi gaba da hanzarinta sai sauri take danko kadan batason ta hada ido dashi, munin shi da qazantar shi kadai ta isa tasa ta tsane shi, to balle ga shi tsohon najadu ga nakasa kaiii shi dai abun ya yi masa yawa.
Bata ankaraba tanata tafiya cikin sauri tana zancen zuci, bataji horn din da ake faman kwarara mata ba, saidai taji an hankadata gefe hankalin Hamid yayi masifar tashi, yayi saurin yin fakin din motarsa ya fito a guje: ya nufo inda take yana kokarin daga ta, Saude tayi saurin mikewa dan gudun karya tabata shima ya dago da niyar yabata hakuri, su kai four eyes, ido hudu, wanda ya
haifarwa Hamid da bugun zuciya mai tsanani.
Cikin tsoro da rudewa Saude ta soma bashi hakuri, kallonta yake ido cikin ido wani abu na faman zarya a cikin kirjin sa muryarsa a sanyaye yace.‘
Ai nine zanbaki hakuri nidana kadeki kiyi haquri wallahi ban lura da keba ne.”
Saude ta kada masa kai sannan ta wuce shi abin
ta.
Hamid ya yi saurin bin ta yana fadar, ‘Don Allah dan tsaya mana ‘yanmata.”
Saude ta waigo tana ’ kallonsa, ya dan gyara tsayuwarsa kafin ya ce ‘Don Allah idan ba za ki damu ba ki fada mini sunan ki.” .
“Saudee” Ta bashi amsa a taqaice.
Ya girgiza kai yana fadar, “Na’am Saudat, don Allah idan ba zaki damu ba kimin kwatancen gidanku
Saude ta waro ido tana kallon shi, alamun mamaki bayyane a fuskarta ta kasa ma magana, ya danyi murmusa kafin yace, “Kiyi hakuri kar kice na fiye shishshigi da yawa;”
‘ Saude ta dauke kanta kafin tace, “Lafiya dai ko?
‘ “Lafiya kawai dai ina so inxo in qara duba kine don ban sani ba ko wani abu ya same ki.”
Saude ta wuce shi tana fadar, “Ni babu abin daya same ni.” Hamid yayi tsaye yana kallon tafiyarta hatta kusa Bacewa ganinsa, yaja wani taqaitaccen murmushi mai sauti tabbas yau zuciyarsa ta samu abinda takeso,zaicigabada binta harya samu ya samo kanta. Ya juya ya shiga motarsa ya bita a baya harkofar gidansu ya rakota batasani ba, sannan ya koma abin sa.
Saude nashiga gida, Laure ta bitada kallo kafin tace, ‘Wai kin je gidan nasu kuwa?”
Saude ta daga mata kai alamar eh laure ta yatsina fuska kafin tace “Amma abinda mamakine da akace min amaryarsa mugun kishine da ita aina dauka sai sun karya miki qafar baya.” Taja tsaki mtws!
“Saiki wuce kafin tallar yamma ta qarisa
Saude ta wuce dakinta simi-simi ba tare da ta sake tankawa ba. Tana shiga daki ta kwanta, wani irin abu ya tokare mata zuciya, ta lumshe idanuwanta fuskar mutumin nan ce ke mata gizo, har yanzu hancinta baidaina shakar kamshin turarensa ba mai sanyin kamshi.
Dama yace yanasonta tabbas da saitayi kukan dadi. Makaskanciya irin ta ace irin wannan namijin yasota aidakamar wuya wai gurguwa da auren nesa. K0 ‘Yar Baba data fita komai bata samu kamarsa ba, ballantana ita mafi kaskanciya mai tsananin rauni Taja wani gwauron numfashi tare da
saurin kawar da abin dake zuciyarta, don ta san k0 a mafarkinta hakan ba zai taba samuwa ba.
Washe gari Saude ta dawo daga tallar safen ta, sannan ta dauro alwala tayi sallah; sannan ta fita’ tsakar gida ta zauna, Laure ta sauke alalar aka zazzage mata a bokiti ta dauka ta fice abin ta.
Hanyarta ta kullum yau ma ita tabi idonta na saman hanya ta wuce ta qofar gidan Alhaji Bashir, Hamid da ke zaune saman teburin maigadi yaga tahowartaya zabura ya mike, ya dubi Malam maigadi yana fadar.
“Ina zuwa Baba bari in dawo.” Bai jira abinda zai ceba ya yi saurin bin ta dan kar ta Bace masa.
Saude ta tsinci muryarshi na fadar. “Assalamu Alaikum. ” Ta waigo tana kallon shi da mamaki a fuskarta ta
kasa bude baki balle ta iya furta wani abu, Hamid yayi murmushi kafin yace, “Ruwan zuma neni ba madaci ba na kasance mai began ki tun a lokacin da na soma ganin ki ba wai sha katafi ba, mene na tunani a kan hakan?”
Saude ta fara nutsuwa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, wadda ta qawatu da dogon hanci da yalwatattun idanuwa wata nutsuwa ‘ta dirar .mata muryarta a sanyaye ta ce, “ZaBina ba tsakanin zuma k0 madaci bane, kyakkyawan zabina shine yawaita ayyuka, masu kyau da gujewa munanan dabi’u, na kasance mai zurfin tunani da Kwakwalwa ba da zuciya‘ ba, meye tunanin ka a kan hakan?”
Hamid ya dan saurara kafin yace, “Ikon Allah ga .shi nima yanzu haka Dady jirana yake, amma ba damuwa, ki fada masa zuwana gobe insha Allahu
zan dawo.”
Saude ta amsa da to, sannan ya juya ya tafi ta raka shi da idanuwanta.
Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya. Mamaki da al‘ajabi su suka dabaibaye zuciyar Saude, har yanzu bata fidda ranta da cewa mafarki take, zata iya farkawa a kowane irin lokaci. Ba
Washe gari Saude ta dauki tallar wainar .ta. Bayan ta siyar karfe sha daya da ‘yan mintuna ta dawo, Laure ta hada’ ta da sanwar alala duk da matsananciyar ranar da ake kwalawa haka ta zauna a tsakar gidan gaban murhun sai gumi ke tsiyaya a jikinta.
Tamkar daga sama yaro ya shigo ya yi sallama, Saude ta amsa tana kallon shi, yace, “Wai’ ana sallama da Malam inji wani mutum a waje.” Saude ta nuna masa dakin Laure da hannu tana fadar.
‘ “Shiga can ka fada masu.”
Yaron ya wuce ita kuma taci gaba da abin da take, yaron bai yi minti biyar da fita ba Malam Bala ya fito cikin shirin tafiya masallaci kasancewar yau
Juma‘ a bai fita kasuwa da wuri yasa kai ya fice Tsawon wasu mintina da suka haura goma zuwasha
biyu sannan‘ ya dawo gida yana faman Kwalawa
Laure kira‘ . “Laure Laure! Laure!!! Wai kina ina ne nake ta
faman kira kin yi shiru
Ta hankado labule ta fito tana fadar, “Wai ya akai ne, ka keta faman kwala min kira sai kace yaki?”
Malam Bala yayi kwafa, “Amma dai ai kin san ruwa baya tsami banza, kin san dai daga jin kiran‘ nan kin san da walaki.” Laure tace ‘To mu gani a qasa
Ya ce, ‘Tabarma zaki bani dan gidan Alhaji’ Bashir ne yazo wai wurin ‘yata yana son a bashi izinin turo iyayensa maganar aurenta.”
Inna Laure ta zaro qananan idanuwanta haqoran nan suka yo gaba sai kace kamfanin cokula tace “Kai don Allah yana ina? ’
Malam yace, “Yana waje
“A’a bari a kai masa tabarmar.” Ta juya da ‘hanzarinta ta nufi daki ta janyo masa tabarma  bayan kyaure ta fito fana fadar.
“Ga shi Malam ka shimfida masa a soro gatanan zuwa.” Ya amsa ya juya da hanzarinsa har yana tuntube
Inna Laure ta nufi dakinta can kurya kan gadonta mai suna bonanza ta shiga inda ‘yar Baba ke kwance tana faman sheka baccinta Inna Laure ta shiga tashinta.’ ‘Yar Baba ta bude ido da kyar cikin magagin barci. ‘ ‘
Ki tashi da Alla kinji aikhairi yazo mana har ‘ cikin gida, da rana tsaka.”
IKilima taja wani’ tsaki ta juya daya barin taci gaba da baccinta, Inna Laure ta Kara bubbuga ta Ta zabura a fusace.
“Wai mene ne don Allah zaki dame ni kawai ina baccina
Inna Laure tace, “Ki tashi banza arziki ne yazo mana da qafafuwansa dan gidan Alhaji Bashir yaron nan yaz0 wai neman auren ki tashi banza, ki shirya.”
‘Yar, Baba ta zabaura ta tashi zaune idanuwanta a warwaje tana fadar, “Kai Laure don Allah da gaske ki ke?”
Laure tace, ‘A’a ai sai ki tashi ki gani da idon ki yana soro shi da Babanki.”
IKilima ta buga wani uban tsalle ta dire daga kan gadon, saboda doki, ta kwasa da gudu zata fita Laure ta yi saurin riqo ta.
“Ke dalla tsaya haka za kije sai kace wadda ta tabu, ai sai kija yace ya fasa, maza ki shirya da Allah karya gaji da jira. ’
‘Yar Baba ta dan nutsu kafin ta ce, “Ba zaki gane bane Laure yaron ya hadu yanda baki tsammani kyakkyawa ne, kuma dan gayu, daga qasar waje fa ya dawo ya kammala digiri dinsa. Laure idan na aure shi wallahi na gama more miji, ai duk samarina
korarsu zanyi “Ta dan yi shiru kadan kafin ta ce
“To wai ma me zan sanya?” Laure ta ce, “Ki sa wannan shaddar taki sabuwa
Ginznar nan tana yi miki kyau sosai.”
‘Yar Baba ta kada kai alamar ta game, sannan ta juya ta bude akwatinta ta Ciro shaddar dinkin riga da siket ne ya sha aiki matuka, ta saka kayan wadanda suka dame ta matuka komai na jikinta ya flto. ‘
Ta zauna ta yi kwalliyarta sosai ta kawo dankwalinta ta ‘kafa daurin‘nan mai suna ture-kaga tsiya, sannan ta saka dan kunne da sarka, ta mike ta janyo wani dan ficicin gyalenta mai kama da matacin koko saboda shara sharansa ta yafa, ta saka takalminta mai tudun dunduniya ta saka, ta dauko wata gingimemiyar jaka saikace waddazata biki ta rataya a kafadarta, ta juyo tana kallon Laure tana wani murza idanuwa.
“Toya kika ganni?”‘
Laure tace, “Kin hadu ‘yata ai shi yasa nake qara son ki, dan kuwa   kyan ki daban yake dana sauran mata shi yasa kullum sai an mana sallama.”
IKilima ta sheke da dariyar jin dadi na kwarzantawar da Lauren tayi mata ‘ Malam ya hankado labule “Wai me take Jira ne har
yanzun kunsam jirafa bashi da dadi
Inna Laure tace, “Ai ga ta nan fitowa Malam, yayi hakuri. ” Malam Bala ya saki labulen ya juya
‘Yar Baba ta dubi Laure ni“Na tafi Laure.”
“A’a mu je in taka miki.” Laure ta fada tana yake hakora.
A tare suka fito, Saude na durkushe a gaban murhu sai faman hawaye take saboda hayakin daya turnuke ta, har ba ta iya ganin gabanta sai sharbar’ mijina take.
Suna isowa inda take Laure ta dube ta, ‘To ‘yar iska munafuka wutar ce ba zaki hura ba k0? so ki ke alalan ta jike a cikin ruwa, annamimiya munafuka.’ Ta duma mata wani uban kulli wanda ya sata yunkurin amai ta zabura ta mike tana faman sosa inda ta ‘maka mata dundun. .
Tace ‘Wallahi Inna itatuwan ne danyu sun ki su kama.”
Inna Laure ta haure ta da kafa, ‘Kan ubanki keda danyun yanzu dan kina munafuka wadannan itacen’ sune danyu,to idan ma kinbarta tayi danya dan kanki,danni yaddah kika fita da ita haka zaki saida ta ko ta kwabo bance ki dawo da ita gidan nan ba, wuta kuma kar ki hura ki yi shekaru dubu anan
Saude ta surce majina tare da goge ruwan hawayen dake zuba daga idanuwanta, ta duqa. taci gaba da hura wutar da baki, amma illahirin zuciyarta naaaaaaaa

Hmmm YA abin yake NE GURINWA HAMID YAZO IKILIMA KO SAUDE
MU tara GOBE DONJIN yadda WANNAN TAQADDAMA ZATACI gaba DA KASANCEWA TAREDA Niiii
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
KE CEWA GOBEMAA DA  LABARIII

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]