[Advertisements⬇️]

Yar tallah - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

*YAR. TALLAH SABON LITTAFI*
Littafin ya fara ne kamar haka
Tafe tAke tana rusa kuka wiwi,,,,,wiwi
Duk ta hada miyau  majina da hawaye ta dame fuska gaba daya
Rungume take da tiren tallan tata wanda ba komai a cikinsa, sai ihu take kwararawa tana kiran wayyo kudina wayyo ni kudina
Mutane sai kallonta sukeyi masu tausayi daga cikinsu su kirata suji abinda ya faru su lallasheta ta tafi
A haka taita saqawa ta lunguna harta iso layin gidansu
Tunda ta iso layin rabi,u wanda bai wuce dan kimanin shekara goma sha huduba kejiyo sautin kukanta yana duqe yana faman wanke wanke
Yai niyyar miqewa karaf sukai ido hudu da inna laure
Ta watsa masa wani irin kallo simi simi ya koma yaci gaba da wanke wanken
Tace munafuki dan iska wlh ka sake ka  tashi baka gama wanke wankennaN ba saina karya maka qafafu
Ta qara jan tsaki ta hankade labule ta shige Daki
Rabi,u yai saurin tsame hannunsa daga wanke wanken ya kwasa yai waje da gudu
A bakin kofar zauren sukai kicibus yace waya tabakine saude?
Ta qara fashewa da wani kukan wanda yafi nada sauti
Rabiu ya qara janta jikinsa kiyi haquri saude fadamin meke faruwa?
Tadan sassauta da kukan tace kudina yaya kudin tallah ne wani ya kwaceminsu
Rabiu ya dafe kirji ido waje yace garin yaya saude?
Kinsan halin inna laure kuma dukanki zatayi
Ta qara fashewa da kuka wayyo yaya dan allah ka roqeta karta dakeni
Ya danyi jimm kiyi haquri saude babu yaddah zan iya  kixo muje kawai ta dakekin
Ta qanqameshi wayyo yaya wlh yankani zatayi
Idanunsa suka kawo kwallah ya cije yace zo muje saude insha allahu bazata dokekiba kinji?
Kai kawai ta daga masa tana share hawaye yaja hannunta suka shiga ciki
Tsaye take a kofar daki da alamun ta cika ta tumbatsa jira kawai take a tabata ta fashe
Saude ta qara fashewa da kuka wayyo allah na wlh yaya dukana zatayi
Inna laure ta zaburo tayo kansu
In dokeki dan ubanki laifin me kikayi?
Hala kin dawomin da sauran raguwar alalen ne ko?ta fada lokacin data shaqo wuyanta
Ina kudun suke in gani?
Ta qara fashewa da kuka tace wanine ya kwace kutumar ubannan wani ya kwace? Aiko yarinya yau zaki daku a gidannan don wlh saina lahira ya fikijin dadi. Ta jata kiyyyyyyyy….. A qasa har zuwa bakin rijiya ta janyo igiyar guga zaki fadamin ina kudina suke ko saina miki dukan mutuwa da igiyar gugannan?
Cikin kuka tace wlh wani ne ya kwace ya ruga tace lallai yarinya aiko jikinki zai gaya miki ni zaki kawowa zancen banza zancen wofi
Tasa qafarta ta tureta ta fadi ta dinga lafta mata igiyar gugar kamar badan mutum take duka ba
Hankalin rabiu ya tashi yaddah yaga qanuwar tashi keyi gashi tasa qafa ta take mata ruwan ciki. Wani irin kuka ya kwace masa ya duqa a wurin yana bata haquri
Inna laure tace au har kanada bakin magana munafiki xonan daman ai jiranka nakeyi ta shaqoshi ta hadesu guri guda taci gaba da jibga tamkar zautacciya
Hankali tashe inna mai dan wake ta zagayo gidan ko lullubi babu a tare da ita
Kai jama,a lafiya maike faruwane a gidannan?
Inna laure ta tsaya da dukan tana huci. Barni da yan iskan yarannan mai danwake nema suke su samin hawan jini. Niqi niqi ina fama dasu inkai gwauro inkai mari wai dondai a samu a rufama kai asiri amman yan iskan yaran basu gani kawai an tafi an barni da jaraba yanxu ace kamar saude wai har tasan taje  tallah ta boye kudin wai tace wani ya kwace sbd mugun hali irinna wannan munafukin annamimin dake koya mata
Inna mai danwake tace eh kam gaskia baku kyautawa kankuba. Yanxu ku harkunfi son aita jibgarku irin haka idan kun boye kudin kuci me dasu fisabilillahi
Tadan numfasa tana kallonsu kafin ta qara zaro ido a,a laure yaya nake ganin yarcan kamar bata motsine””
Ta qara matsawa tana tattabata ta dago da sauri hankali tashe tace wlh laure bata motsi. Tace kai haba mai dan wake da gaske kike?
Inna mai danwake ta daga hannun nata ta saki taga ya tafi ragwaf alamar ba rai
Inna laure ta kwasa da gudu tana gyara  daurin zani fadi take iya karfinta  na shiga uku ni laure

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Hmmm yanxu aka fara me zakuce gameda da wannan sabon littafin

*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]