[Advertisements⬇️]

Birnin gayu5 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

                birnin gayu🏘️

                   chapter5

jama‘ar wurin ‘da suka’ taru_ suna kallonsa. Ya dinga Zaginsu da Turanci.  ” ‘ Wasu ko a jikinsu,”don ba suma fahimci me yake fadi ba, Ibrahim ne ya jashi suka shiga Mota da idonsa jawur kamar zai zubda hawaye. Ibrahim ya kalleSa’ yace, “Sabeer a dinga haquri, ba ,kullum“ zaka ‘sami yadda’kake ‘soba, “ Dama tsautsayine  yasa Motarmu’ tsayaWa anan
ya kalli  Nura. “”‘tuqa mana  mu ‘lallaba mu koma Gida, fitar dai tayautafasu
Sabeer ya harari Ibrahim cikin fishi‘ ’yacé “Tunda. bayanta kake bi da alama kaji dadin abin da ya faru dani in kaje ka  hada party Yayi  wani’ murmushin yace “Sabeer kenan.
Tabbas ‘naji dadin abin ba don”. komai ba sabo da darasi ne na farko ga rayuwarka.
Sai dai ba zanyi Party ba sabo da ina da abin yi da yawa , kaine  keda lokacin Party ba niba”. ‘
Sabeer ya , qara qulewa yaji- tamkar ya kamashi ,da duka, sai dai ba ‘zai iya hakan .ba sabo da matsayinsa‘ da girmansa da’yake dashi
Bai sake furta: komai ba, sai dai kallo daya za kayi masa kasan yana cikin ,bacin rai da zafin zuciya.
Ganin haka yasa‘ “Ibrahim . ya soma lallashinsa amma bai kulashi ba.. ‘
” Haka su Nura k0 kallo basu ishe shi ba.
Haka .suka haqura suka Kyaleshi, har suka isa Gida, ‘ya fita ya nufi Dakinsa k0 Marfin Motar bairufe ba.
Ibrahim ya bi shi da. Ido yana tunanin ta ina zai shawo kansa.‘ Fatansa dai kar ya yiwa sister Waya ya daga mata hankali
                     *****
_ DEEDA TA ISA gida Itama rai bace Inna mai fura tace Deeda lafiya! Magana fa nake kinaji , meya faru na ganki haka, naga kwanon furan  a Bace?” ‘ “Inna don Allah niki kyaleni”. Tayi Tsaki. “
‘ “Daman haka ‘yan BIRNI suke wulakanta Talaka k0 mara karfi shi ne wayewa?”
‘  “Ke Deeda ba dai fada ki kayi. da ‘wadanda suka fi qarfinki ba k0? ‘ ,Kinga fa nan Birni ne ki rufa mana asiri karki musu halin da kike mana a Kauye muna lallaba rayuwarmu ki jawo man masifa. ‘ ‘ Ni kam ki fito ki kai min daya Furan…” , “Nifa Inna ki kyalemi, bazan.”Iya daukan wani furaba”
Garam!! “Ta. ,_,rufe ,Kofa- —ta bar Inna da budadden Baki tana mamakin al’amarin Deeda. :- ” “Tomeya faru kumahaka?” ‘ Ta sungumi Kwanon Furan ta fita. , ‘ A can ta ji ‘labarin abin da ya faru. Nan ta godewa Allah ,daba wanda’yanuna ‘Gidan da» Deeda take da sun shiga wani tashin hankalin.
“ KARFE SHA BIYUN DARE
amma Sabeer‘ya‘kasa nutsuwa, k0 Abinci baiciba a wannan yammacin har zuwa dare bai iya ciba, tsabar tafasar zuCiya, sai kace wanda akai masa wani mummunan illa. K0da yake abin da bai saba ba kuma baizataba. ” duk lokacin daya tuna fuskar deeda sai Ranshi ya Baci, yayi Tsaki
Banza»Mummuna Yar kauye Yar gidan matsiyata kawai
Abin da yake’fadi kenan a harshen Turanci.Abin da yafi kona masa‘zuciya shine, Mace ‘ce ta ma‘sa wannan wulaqancin, waccé ba koman-komai ba. ‘
“Shin Ina zai ganta ya rama wulaqancin datai masa?” : ‘ ’
“Shin inya gantama taya ya zai some rama wannan wulaqancin datai masa?”
Lokaci guda Sabeer yaji burinsa shi ne neman yarinyar nan da ‘kuma_ rama wulakancin da tai masa wanda ya kasa samun irin wulakancin da zai mata ya qona mata zuciya, Wanda ba zata taba mantawa da shi ba har  qarshen rayuwarta
Ibrahim yana hangosa ’yana ta. kaiwa da komowa da alama har yanzu bai huce ba, abin na damunsa. ‘
yayi qoqarin lallashinsa yaci abinci koda kadanne  amma ina wannan dare. Abincin
ma daci yake yiwa sabeer. Da kyar ya sha rabin
Kofin juice
‘ ” Ibrahim tare ya kwana da‘ shi, ‘kowanne
juyi yayi sai yaga Sabeer na zaune ido biyu. ‘
‘ Shi dai tun da .yake bai taBa ganin abin da ya hana Sabeer Barciba a rayuwarsa sai yau. K0 Jarabawa bai taBa hanasa bacci
‘ Haka baitaba ganin Sabeer yadauki wani abu da muhimmanci haka ba. A wannan dare ya kira Farida. ‘
Ta dauka a gigice. ‘
‘Lafiya‘ Kanina, Waya yanzun nan?”
yi haquri Yayata
“Kanina aini bani da, matsala a kowanne: lokaci zaka iya kirana damuwata. dai shi ne naga  dare. ne_,yanxu a Nigeria lokacin da kowa ke baCci, dole inji tsoron ,~ ganin Wayarka a wannan lokacin Haka ne Yayata, kasa haquri nayi gari ya waye, naga ,abin da ban taba ‘gani bane a tare da. ‘sabeer daga ni har ke har Daddy ‘abin ‘da muke so mu gani a tare da shi kenan.“ –
“Kanina fada min mene ne don Allah?” ”
Ta fada cikin zumudi da dokin sonjin mene ne
“Yayata‘ yau lokaci‘ na farko da naga Sabeer .ya zama (Serious) akan abu, ya dauki wani abu da muhimmanci da gaske harma ya kasa bacci‘ yana ta (Planing) ta‘ yadda zai bullowa’ al’amarin, ‘yana ta ‘ Kullawa da kwancewa. Kin tuna Yayata ko Jarrabawa‘ k0 Ciwo ba ya hana Sabeer Bacci?”
Haka ne Kanina. Amma naji dadi ba kaji wani farincikin ‘daya mamaye niba. Akan (Business) ne ko Asibiti?”
Ibrahim ya danyi shiru sannan yace “Karki damu zan fada miki in kin zo k0 ma akan mene ne dai shi ne yadda ya zama (Seriou)  ya bada muhimmanci akan abin
“Haka _ne qanina, ina mana addu’a‘ Allah Ya mana jagora, ya kawo sanadin kimtsuwar Sabeer”.
“Haka ne Yayata, da alama Allah Ya kawo sanadi. Ke dai kici gaba da addu’a da fatan samun nasara ga abin da nayi niyyah
“Zanci gaba da addu’a qanina, Allah Ya taimaka”. .
“Amin”. Ya amsa.
Bayan tambayarta lafiyarta ’ :da wasu al’amura sukayi sallama.
Ya dawo ya samu har yanzu Sabeer na kaiwa da kawowa. –
Ya isa gareshi ya jawo hannunsa yace “Sabeer zoka kwanta dare yayi”.
Ya Bata fuska. _ , ‘
“Uncle IB ya ,zanyi in iya bacci?” ‘ ‘
Idonsa ya kada.
“Kaga wulaqancin da yarinyar nan tamin.
Please’Uncle IB ka taimaka min in nemo ta, ka sanni yanZu k0 Unguwar ba zan iya sake ganewa ba”.
“Zan taimaka maka. Ina dai yarinyar ka keson sake gani?” ’
“Sosai don, ba zan iya kyaleta ba”, ‘
“To kar ka damu zata zohar inda kake ta sameka..amma dai yanzu ka kwanta gobe muna da fita Asibiti”. ’
Da kyar ya lallaBashi ya kwanta ya dinga juye-juye ya kasa baccin har sai dab da Asuba – Bacci ya sace shi.
Juyin duniya kuwa Ibrahim yayi Sabeer ya tashi suje Sallah amma yaqi, haka ya hakura dole ya barshi.
Bai tashi ba sai wurin sha biyun rana. Nanma sai da Ibrahim yaje Asibiti ya dawo ya tashesa suka fita tare.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

                       *****
tun qarfe shida na safe deeda da lnna mai Fura ke layin ganin Likita, duk kuwa sammakonsu bai sa sun ga Likita da, wuri ba Saboda wani Tiyata na gaggawa daya Shiga, sai daya fito sannan ya soma ganin marasa lafiya
Deeda ta bata fuska cikin Kosawa ta ce, “Dama ai duk abin da aka ce ma kyauta ne sai. kaga wulaqanci. . ,
Ni dama tunda naji Tabawa tace mu zo wannan Asibitin kyauta ake ganin marasa lafiya na san za a wahala.
Aik0 Asibitin gwamnati ana dai siyan Kati…”
“Wai me yasa kin fiye gajen hakurine?” Kakarta ta fada a hasale. .
‘ “Ke da kike neman lafiya k0 ma kwana za kiyi ai sai ki hakura ki jira su ba mutane bane? Haba kin fiye mitan tsiya.
Duba Asibitin nan da kyau kin san ya sha karfinmu ba don alfarma muka samu ba”
‘ ‘ Deeda tayi tsit! don bata son musu k0 wani sa’insa da Kakarta.
Nan ta canja maganar da cewa, “Inna duba hannuna fa ya wartsake, jikina ya mike ba kamar da ba, sai ina ganin kamar yanzu bani da bukatar ganin Likita”.
“Kina da buKata”. Kakar ta katseta.
“Kika san ko ya sake dawowa? Ai gara ki yiwa Likita bayani in da Magani a baki da zai hanashi dawowa.
Kuma ma ai ba duka jikinki ne ya wartsake ba, har yanzu ta ciki, ta wani wurin akwai inda yake yamutse”. . ‘ ‘
“Shima a hankali ai zan washe kamar sauran
“Ki min shiru tunda har munyi haqurin jira har wannan lokaci kuma munzo to ba’abin da zaisa mu koma…”
Kafin Inna ta rufe Baki wacce ta shiga din ta fito tace Deeda ta shiga. Bata Bata lokaci ba ta kutsa kai ya yin da Inna ke jiranta a waje.
Zaune yake akan (Table) Tebur din dake cikin OfIice din, da alama shi ne Table din Likita. SABEER NE! !!
Hannunsa riqe da Game yana ta bugawa, gefensa kuma Fruts ne da Juice yana ci yana Game hankalinsa kwance. Hakan ba karamin nishadi yake sa shi ba.
Deeda ta turo. Kofar ta shigo tare da
sallama. ‘
K0 daga kai baiyi  daga Game din da ya ke ba balle ya amsa mata sallamar
Nan ta je ta tSaya a gefe gami da cewa, “Ina wuni Likita?”
Har yanzu bai dago kai ba sai dai ya amsa mata da cewa, “Likita na (Washing room) Bayi, ki jira ya fito
Nan yaci gaba da game dinsa. Ita k0 _taja
kujera ta zauna tana kallon yadda’ ya bawa game”‘ din muhimmanci. ‘ ’ “Lallai wannan bai da matsala a rayuwa “ta fada a ranta. ‘ ‘ Sai ihu yake yana dariya shi daya yana  buga game yana morewa abinsa. ‘Mutum babba dashi qaton Saurayi kamar Wannan’ yana abin Yara Kai Allah Ya“ kyauta. – ‘ – Toma wai shi ba Likita bane me ya keyi a nan?
Wai a gabansa zan ga likitan?  KO shima Likitan yazo gani? Bari dai in tambayesa’
Ta mai da hankalinta gareshi tace, “Mallam kaima Likitan zaka gani ko in fita sai ka gansa in shigo?”
Har yanzun bai kulata ba. Haushinsa ya kamata.
Tace, “Wai kai ba kajin kunyane Kato da kai kana abin Yara?” ‘
Nan da nan ko Sabeer ya fusata, ya dago kai .gami da juyowa da sauri don ci. mata mutumci. ‘
Carab  k0 suka yi ido biyu da juna. Ya mike tsaye cikin mamaki kuma a fusace, itama ta mike, ta lura da haushinta da ya ji amma ita bata ‘ ma gane shi ba. .
“Na lura yarinyar. nan baki da kunya, ba ki da mutunci! Ubanwa ya kawo ki Asibitin nan?”
Ta kalleshi sama da kasa ta buga mai Tsaki tare da Harara tace, “Sa’a kayi ban iya
Zagi ba dana maka wadanda yafi naka ciwo. Kuma karka’yarda ka sake zagarmin Uba”.
Sai an Zaga me ki ka isa kiyi? Dama nemanki nake, yau sai na miki rashin mutuncin da baza ki manta da shi ba”.
“Banyi tsammani ba”.
‘ Ta ba shi amsa kai tsaye.
“’Me kike nufi?”
Ta kada mai Idanunta wanda sai da ya sa yaji gabansa ya fadi. ‘
Wannan ne lokaci na farko da bama Mace ba, lokaci na farko da aka taBa kallonsa ido cikin ido ba tare da shakka k0 tsoro ba.
nace, “Ban tsammanin zaka iya ba. Ina nufin yanayinka da alamunka bana zaton ka Iya rashin mutunci , sabo da a yadda naga alamarka  girman jiki ne kawai kayi, amma har yanzu tunaninka da ayyukanka har kwakwalwarka ta yara ce basu girma ba.
Yaro k0 ban tsammanin ya san meye rashin mutunci  balle ya iya, sunansa kawai ka sani, don haka ka bari in Kwakwalwarka da tunaninka
sun gama girma sai Kazo mu kara rashin mutunci, inka gwada min na ‘YAN BIRNI ni .kuma sai in gwada maka na ‘YAN KAUYE”:
Tuni Sabeer ya kara harzuka, idonsa ya kada yayi ja ya kasa furta mata komai, kuma ya kasa mata komai, sai azabar zuciya kamar zata kashe shi. .
Tun-tuni Ibrahim yaji hayaniyarsu ya fifo ya tsaya a kofar ya -harde hannu yana kallonsu yana murmushi. . -’
Cikin qunar zuciya Sabeer yaCe mata, “Fita Asibitin nan tun da bana Ubanki bane, ba zakiga Likitan ba, kuma yau sai na nuna miki halin yarinta
Ya- zaro- Belt dinsa da karfin tsiya ya kai mata duka, tayi saurin sa hannu kuwa ta tisge. Mamakinta ya‘sa shi bude Baki.
_ “Bi a hankali Yaro kar (Body bulding) din da kayi ya yaudareka; kar ka ganni Mace ka raina min Wayo daga Kauye nake, naci Tuwon Dusa naci na Dawa, karka nemi raina ni.
Kuma dana san Asibitin nan na Mahaifinka ne da ban soma takoshi ba.”
Ta ja mai dogon Tsaki ta juya zata fita, wani kololon Bakinciki ya. tokare masa zuciya, ya rasa me zai mata.
Bata ankara ba ko ta taka Sunul ta fadi qasa ta daku. . –
“Wash Allah”. Ta fada
“Wayyo! Bayana”.
Sabeer ya Kyalkyale da. dariyar mugunta yace,”Su Budurwar Kauye masu karfi an sha Kasa”.
Ya matsa dab da ita yasa kafa ya’ takéta .sai da tayi Kara yace”Duk karfin Budurwar Kauye bata isa ta kai Namiji ba, musamman na Birni, BIRNIN ma na GAYU  Ya Kara taketa da Karfinshi yace, “Dama neman‘ki nake tun rashin mutuncin da kika min ban manta ba, kin hanani sukuni kin hanani
Bacci’ kin hanani cin Abinci, kin sani yawan
tunanin wannan mummunar fuskar taki, har ta zauna a kwakwalwata.
Yau wannan hannun daya watsa min Nono sai na Balleshi”.
Nan ya kai daya Kafar ya danne Yatsun da qarfi” ‘
Ta sa ihun Azaba, sai da hannun yayi jini sabo da irin takalman da yasa bana wasa ba ne.
“Wayyo Inna zai kasheni
Ibrahim ne ya matso wurin da sauri ya janyesa.
“Kai- Sabeer baka da hankali za ka kashe- ‘yar mutane?”
“Kyaleni in mata illa, gobe idan ta. ganni za ta canja hanya. Kuma wannan kadan ma ta gani.” ‘
Ibrahim ne ya taimaka mata ta tashi gami da dressing din hannun cikin . gaggawa ya samu jinin ya tsaya, amma baiyi nasarar tsayar da jinin ba.
Hankalinsa ya tashi, gaba daya ya rude, bai taBa tsammanin abin nasu zai yi tsanani haka ba da bai bari hakan ya faru ba. ‘
Nan ya sa hannun cikin qankara yasa mata Magani sannan ya daure da Bandeji ya nufi ciki don dauko Allura ya mata.
Bayan fitarsa Sabeer ya harareta ya ce, “Kalli ‘yanda kika zama abin tausayi…azaba kadai ta canjaki.”
“Allah Ya isa Ta fada cikin zafin zuciya.
– “Kuma kai ne abin tausayi bani ba, don ni kam ban iya bin ‘yan fage in yiwa mutum illa ba sai ‘dai in fuskance “shi. Kaji kunya daka nuna qarfinka akan Mace”.
Taja Tsaki gami da matsawa dab da shi, bai ankara ba taja farar Rigarsa ta goge Jinin dake zuba a hannunta gaba daya ta bata masa Rigar. ‘ ‘
Ya daga hannu zai Mareta, tuni ‘ta manta ciwon dake hannunta ta cafke Hannun ta gantsara masa Cizo ta fita da gudu.
. Inna dai bata ankara ba sai ganin Deeda tayi  ta fito da gudu a rude ta bita. “Ke Deeda!!!”. ‘ Can kuma saiga Sabeer ya biyota da gudunsa. ‘ ‘ Inna fa hankalinta ya tashi, ta bisu tana,”Deeda! Deeda!! Deeda! ! !” Daga qarshe dai  ta gaji ta hakura don ba‘ za ta iya gudunsu ba. ‘ – Sai da suka yi nisa sosai har suka fita Asibitin sannan Sabeer ya yi nasarar kamata ‘ Bata saurara masa ba’ tayi na ‘maza ta turesa da qarfinta. ‘ Sai GA Sabir ya fada cikin wani ruwan dake  a bakin hanya. . Tana’ ganin ya’ kai qasa kuwa ta arta ana Kare, bata tsaya k0 ina’ba sai da ta kai Gida, ta nufi daki ta rufe tana haki gami da tuno abin da ya faru kamar a wani Mafarki k0 Almara. . lnna dai hankalinta a tashe ta nemi abin hawa ta kOma bayan ta gama neman Deeda bata
ganta ba, ta tafi tana addu’ar Allah Yasa  ta koma Gida.
Sabeer ya mike cikin takaici da bakin ciki da Bacin rai, duk’ Kunya ta kamashi da yaga Yara da wasu Mutane suna kallonsa.
Wasu ‘yan Mata kuwa har dariya suke suna mai da‘ yadda abin ya faru, da alama a idonsu aka yi.
Da kyar ya iya daga kafa ya miqe ya wuce kai sunkuye takaici da kunya sun lulluBesa, ya rasa ma ina za shi.
Shi ‘don bai gane hanyoyin, don haka dolensa ya koma cikin Asibitin, ga‘ shi ‘ba Waya a hannunsa, haka’ dolensa ya sunkuyar da kai yana Boye fuska ya koma cikin Asibitin yana kaucewa jama’a yana kulla tsiyar da zai mata  Ibrahim yana ganinsa ya fashe da dariya
yaja shi wani Office dinda ba kowa ya ce, “Sabeer kai ne haka k0 Ido na ne?”
Cikin zafin rai yace, “Wannan Aljanar Yarinyar inna kamata k0 sai na harbe yar banza! Ni zata yiwa haka?”
“Ya isa haka Sabeer. Yanzu dai abin da ya faru ya faru ba yadda ka iya, ka koma Gida ka canja Kaya ka barni inyi aiki Please tun da nasan yau ma kai kam ka tashi’ba za kuma kayi aikin ba”
Ya Bata fuska.
“Uncle IB ka san ni ban gama sanin hanyoyin garinnanba, Please kazo ka mai dani
Ibrahim ya cira kai ya kallesa yace, “‘Ka yi hakuri Sabeer ba zan iya barin aikina inyi naka ba, yanzu haka marasa lafiya na dakatar ina sauraronka.
Please har yaushe komai sai an maka kai ba Yaro karami bane, inba zaka iya komawa ba zan ma (Driver) din Office magana ya mayar da kai Gida, amma ni dai ba zan bar aikina ba”.
Sabeer yayi fishi ya fisge Key din Motar ya fita, Ibrahim ya bisa da kallo sannan yaci
gaba da Aikinsa da niyyar inya gama’zai je inda suka hadu da yarinyar nan ya nemi Gidan su.
             %%%%%%%%%%
Sabeer kuwa, sai daya gama zagaye_ kafin ya kaiga gane hanyar Gida, ga shi ba dama ya kira Abokansa zasu masa dariya.
Haka ya yi ta shan wahala kafin ya isa Gida ya koma ya samu Momi ta dawo, wato Hajiya Amina, sai dai bai bi ta inda ta keba ya wuce ya cire kaya ya shiga Wanka. .
Ya jima kwance cikin Ruwa a (Bat Tap) yana tunanin irin abin da zai ma yarinyar nan da inda zai sake ganinta, sai dai hakan ya gagara, tunaninsa bai samu maganin matsalarsa ba.
Nan tunani ya fado masa, kawai ya kira Abokansa don su tayashi nemanta da kuma ba shi shawarar irin rashin mutuncin da zasu mata.
Bayan ya fito yaji kiran (Door Bell) na Bangarensa, bai kula ba sai da ya sa Kaya ganin an matsa ya fita ya bude.
Momi ce tsaye tace, “Lafiya Saber tun dazu ina tsaye, ina ka shiga?” ’ ‘ Ya dan sunkuyar da kai yace, “Momi ina Wanka ne Shigo mana,’dama ina shirin inna fita zanje in gaishe ki. Kin dawo lafiya k0?” : “Lafiya kalau”. Ta amsa masa lokacin da take zama ta ce, “Yayunka duk suna gaisheka.‘ . – ‘ ‘ Daddynku ya fada min komai’ game da_ dawowarka, sai ka dage ka koyi ‘Aiki, in da hali ma harka Karo ilimi a fannin da kafiso, duk da Asibitin muna da Likitoci, amma akwai bukatar ka a Asibitin. _. Ina so ka daukeni kamar Mahaifiyarka, duk abin daya shige ma duhu kazo ka sameni Bangarena na Shawara k0 wani abu. _ Sannan ina fatan ba ka da matsala da Ma’aikata masu kula da Bangarenka da Abincinka suna gyara maka Side dinka yadda ya kamata, ko?, duk abincin’da kake bukata order kawai za kayi…”
“Na sani Momi ba sai kin bata bakinkiba Ya katseta.  “Nan Gidanmu ne Gidan Ubana ba sai an bani ko ance in tambaya ba. . Sannan Sister ita ce Mamata ita ce komai na, kar kiyi qokarin zama Mamata ki zauna a matsayin .Matar Babana inaga hakan zaifi mana ni dake Sannan Uncle IB yana tare da ni, duk – bukatata shi kadai ya isa ba sai kin sa Baki ba‘ In koyi aiki k0 kar in. koya, wannan ba matsalarki bane Batayi mamakin halinsa ba, tayi wani murmushi irin ta manyan Mata da idonsu ya bude tace  To shi ke nan tunda haka ka ke so, muje a haka-tun da kafi son in, rikeka a matsayin dan ‘Mijina‘ Fine, ni kam na kware wajen iya,rike ‘dangantaka tunda rikon dan kishiya kakeson nai maka  ina maraba’da hakan. inaso ka ,sani bani da matsala da kai, bazan cutar da kai,ba amma fa kar ka shiga gonata kayi kokarin tsayawa a matsayinka”.
“Kema ina son ki tsaya a iyakarki”.
“Da kyau”.
Ta fada tare da girgiza kai ta fita. Ya bita da wani matsiyacin kallo gami da rufe gofar Falon ya koma ciki. ,
Wani radadi yaji ya ziyarci” hannunsa, nan ya mai da kallonsa kan hannun, yayi jawur har ya soma kumbura. ‘
Yaja dogon Tsaki, haushin Deeda da tsanarta ya Kara shigarsa, don gurin data gantsara masa Cizo ne.
“Amma wannan akwai ‘yar rainin wayo…niza ta fadawa bafar magana? Me take nufi dana girma amma halayena basu girma ba?
Tana nufin ni yaro ne
Nan ya mike yana kallon kansa a Madubi tun daga sama har Kasa, duk ta yamutsashi
kwana biyu kawai.
banzar yarinya yar KAUYE mummunar yarinya zata sani a gaba… zan mata rashin mutunci  To amma me zan mata?”
Waya ya dauko ya bugawa Abokansa yana musu neman gaggawa.
Cikin minti talatin suka hallara.
“Lafiya Sabeer irin wannan neman gaggawa?”
“Ba lafiya ba
Ya fada a qule.
“Wata Aljanar Yarinya ce ta sani a gaba, ta daga min hankali”,
Salim ya kalli Nura sannan ya kalli Nura sannan ya kalli Sabeer din yace, “Ba dai mutuniyarka data watsa ma No… .”
Wani mugun kallo daya masa yasa shi gum da Bakinsa bai Karasa ba.
Yace, “Na ganota”.
Sabeer din yace,”Shawara nake so ku bani. wane rashin mutunci zan mata?”
Nura ya ce, “Me zai hana ka yiwa banza lahani, wato ka banke banza da Mata sai ‘ta Karye ta dawo me Kafa daya?” ,
Saber ya girgiza kai.
“Not Bad Kai kuma ,fa Salim, me ka ke gani?”
Salim yace, “Hakan da ya fada dai-dai “ne” k0 ka kadeta ko kayi hayan wasu su saceta ta, Bace Bat na kwana biyu a rufeta inda k0 Hannunta ba zata gani ba don Duhu, ta Yini ta kwana da Yunwa..” ‘ .
Sabeer yace, “i Hope shawaranku yayi aiki,
Nura yace, “In dai har muka yi yadda nace dole ya taBata. In ta zama Gurguwa aita .nakasa”.
Sabeer yace “Ba wannan ba, samun inda take ma bala’i ne”. “Zamu nemota a same arean da muka hadu  da ita
zamu nemota, zan mata ,abinda ba za,,,,’yan Samari”. Muryar Ibrahim ne
suka mai da hankalinsu gareshi.  ‘yana wannan murmushin nasa yace ‘-‘.da;abin da zaku yi a rayuwa kuke planing tsarawa da yafi muku”.
yayi dariya gami da fadawa jikin unle lb yace kaida Sister ’kune rayuwata (My whole world)  ya yi, murmushi yace kadai fadi, amma ba Uncle IB bane zai zauna ma. da Mata ‘yar KAUYE ba. Ka tuna
ya fada tare da murmushi ya Bata fuska.
Ya ce, “Uncle IB karka Bata min rai, kasan  na tsani ‘yar Kauyen nan da aure amma nafi tsanar yarinyar nan (I hate her the most)”. .
Ibrahim ya ce, “Ni zan fita dama na leko dubaka ne zan fita ni ina da abinyi bani ’da’ lokacin tsanar wasu k0 daukan fansa, in kuma baka bar maganar ba sai na fadawa Sister”. ‘
Ya langaBe kai. ”
’Yace Uncle IB kar ka min haka mana”.
“Na dai fada maka ka zaba daukar fansa
.ko Bacin ran Sisiter”.
Nan ya fice ya barshi. Ya maida kallonsa kanSu Salim ya ce,‘ “Guys this plan is cancel”
Nura yace, “Wai kana nufin kana tsoron Uncle IB da Yayarka?”
Sabeer yace, “Sabeer  bai tsoron kowa, ko shakkar kowa just that ina son Sister da Uncle IB (and 1′ respect them a lot) ban san Batawa Sister rai, kuma sabo da wannan Aljanar ba zan ‘Batawa Sister rai ba, sai dai duk randa na hadu da ita sai na mata illa fiye da wanda ta min”.
Yana magana yana kallon inda ta dankara masa Cizo.
            £££££££££££££
da tambaya da bincike a Unguwar, Ibrahim ya gano Gidan Tabawa inda‘
Deeda ke zaune. Tana daki  tana shirya kaya ranta a Bace
sabo da washe gari zata tafi Gidan Aikinta.
Yaro ya shigo. “Wai .ana sallama da budurwar dake
Gidan nan”.
‘ Inna mai Fura ta kalli Yaron.
“,Waye ne
“Wani me Mota ne”. Yaron ya bata amsa a takaice.
“Jirani”. ‘ ‘
Nan ta shiga ciki ta dauki Hijabi ‘tabi bayan Yaron.
“Muje
Yana zaune cikin Motarsa a Kofar Gidan ya hango Yaro da Inna. Mamaki ya kamashi. Yayi saurin fitowa daga Motar lokacin da suke isowa. Innan ta kalleshi kallon tambaya. Kallon da take masa ya sa ya sha jinin Jikinsa. Tabbas ko k0 ba a fada masa ba ya san ko Uwarta ko Kakarta ce. Ya kalli Inna da kyau, ya ga irin shigar: da tayi ‘ ’ A ransa ya ce “Lallai wannan yarinya ta san inda tayi gado…” . Inna ta katse mai tunani tace, “Gani; naji an ce kana sallama da Budurwar Gidan”. . Ibrahim ya kalleta da kyau ya rasa ma me zaice mata. ‘ Tsayuwar da tayi ta riqe kugunta yasa yaso tuntsurewa da dariya amma sai ya dake yace “Budurwa’ na’ce ba tsohuwa ba
Ta kallesa da kyau tace, “A Gidan nice budurwa k0 kana musu ne? Me ya kawoka, me kake nema?” ‘
ta tsareshi da ido. Gaba daya ma ya rude ya rasa me zai ce mata.
yanata.soshe-soshen qeya da kame-kame, can dai ta tausaya masa tace, “jikata kake nema me za kai mata ya sauke numfashi yace, “‘Dama taje Asibiti ganin Likita ne to sai suka samu saBani da kanina ta tafi bata ga Likitanba nazo in bata haKuri ne kuma inji meye matsalarta donni Likita ne”. ‘
ta zaro Ido ta washe Baki. “Aiban sani ba.
‘ wannan ciki zaka shigo. Dama haka Likitocin- suke na birni har Gida suke biyo marar lafiya? Ikon Allah, ai Deedan tana Ciki shigo
‘ har ciki. A tsakar gida ta shimfida masa Tabarma sannan ta shiga Ciki‘ ta kamo  hannun Deeda.
ke fito  ga Likita har Gida yazo duba ki”. ‘
Deeda ta kalleta cikin mamaki.
“Likita?”
“EH”. Ta amsa mata a takaice.
“Ashe da rabon zaki ga Likita kafin ki tafi Zo muje ‘ Ta jata har Tsakar Gida wurinsa.
“Likita ga Jikar tawa”.
Deeda ta kallesa cikin mamaki.
“Likita har Gida?”
Taja Kujeran- zama na tsakar Gida ta zauna, yayin da Innar ta zauna a gefensa.
Deeda ta gaisheshi Sannan ta tambaya.
“Anya ni kuwa kazo nema? K0 ka Bata ne?”
“A’a ke na zo nema. Sunana Dr. Ibrahim, nine Likitan da kika zo gani da safe kuka samu saBani da Kanina”.
‘ Ta girgiza kai.
“0h!” Gami da dan yamutsa fuska.
“Wannan qanin naka?”
Ya yi murmushi gami da cewa, “Ina ji dai kuna da (Allergy) da juna, duk lokacin da aka ambaceki sai launin fuskarsa ta canja, ‘kema haka tun randa kuka’ hadu jininku yaxo daya
Nazo inga hannunki ne in baki haquri sannan inji meye matsalarki
Kallonshi take tana murmushi. A ranta tace, “Akwai bambanci tsakaninsa da qaninsa.
Shi mutum .ne mai sanyin hali da kirki. Haduwar farko na gane hakan.
Shi ko wancan haduwar farko na gane halinsa ‘mara kyau.
‘Jin tayi shiru bata amsa ba Inna ta yi carab  Ta amsa.
“Likita hannunta dai da sauqi, mu Mutan Kauye ne muna da. dabara da namu Magun’gunan irin wannan CiWon. –
Zan daiyi maka bayanin babbar matsalar duk da yanzu taji sauki ciwon da kansa ya baje”.
Nan ta soma zayyana masa ciwon Deeda tun tana karama har zuwa girmanta da shigowar su Birni ya soma bajewa da kansa a hankali.
Ya danyi shiru na tsawon lokaci ‘yana kallon Hannayenta.
Yaso ya fuskanci matsalar sai dai duk da hakan sai yayi bincike.
Yace, “Na fahimta Kaka, sai dai duk da hakan tana buqatar zuwa Asibiti sabo da a can ne zamu yi duk wasu gwaje—gwaje don gano ainahin ciwon, duk da dai yanzu ya washe ba matsala, amma ‘gaba zai iya dawowa, duk da ban tabbatar da wane ciwo bane, amma dai ba abun damuwa bane, inma ta sha Magani to da yardar Allah zata rabu da shi.
Don haka gobe in Allah Ya kaimu ta sameni a Asibiti karfe goma.”
murna ta lulluBeta. ,
:Na gode Likita.”
Mun gode, duk da goben zata tafi amma” zata ganka. kafin ta tafi”.
Ya mike yana fadin Allah ya kaimu goben, Inna tana  ta godiya, Deeda kuws kallonSa take  tana mamakin’ kirki irin nasa
“ya mike ya kalleta yace, ‘miss Deeda inga hannun naki?” .ta-‘ sunkuyar dakai ta mika masa  hannun ya kalla ba tare da ya taBata ba yace, “Kina da jiki ‘mai kyau don bai kumbura ba, indai yana miki radadi ki sha (Pain Reliver) Paracetamol
,to”Na gode”
Nan yayi sallama da su ya wuce.
Deeda ta bishi da kallo yayin da Inna ta rakashi har kofa. Ta dawo ta samu Deeda zaune tayi- Tagumi. ‘
tace, “Deeda kina tunanin tafiya ne? Karki damu  Allah na tare dake ina tare da ke
idan kinga ana saki abinda ba dai- daiba ko ba kya so zan dauko ki mu dawo “. Ta“ danyi murmushi tace, “Inna haka ne, ina tunanin tafiya sai dai inna tafi tunanin barin karatuna duk dana koyi abu da yawa na iya abubuwa da yawa karatu da rubutu, turanci da ma abu da yawa.
Haka na samu ilimin Addini‘ sosai a Makarantar wanda da ban sansu ba..
– Alhamdu lillahi da zaman da nayi a Gidan Tabawa da gatan data min, sai dai ilimi ba ya qarewa, yanzu na soma dandanarshi zan so inci ~gaba’da samunsa.
Sai dai ilimi ana samunsa ta kowacce fuska, duniyar ~gaba dayanta Makaranta ce, kamar yadda na koyi wani abu yanzu na fahimta, akwai mutanen kirki akwai na tsiya.
Inna duba bambanci tsakanin wannan Likitan da qaninsa.
Mutum mai nutsuwa mai kirki mai mutunci. Kaninsa kuwa…” ‘
Taja dogon numfashi. “Bana son ma tunashi balle maganarsa.
Inna karki damu  ina maraba da sabuwar rayuwar da zan shiga, a wurina wani sabon Makaranta ne na koyon wani sabon ilimin
rayuwa.
Idan Allah Ya kaimu gobe zanje Asibitin zan roqi Tabawa mubiya tacan» saimu wuce. Insha Allahu akwai‘haske a tattare da tafiyar da zanyi”. ‘ .Inna tayi ‘murmushi. ‘ :”Naji dadi Deeda yadda kika kwantar da hankalinki baki daga hankalinki akan tafiyar ba. Allah Ya taimaka ya sa alheri. Muna gari daya, zan dinga zuwa dubaki, zaki dinga zuwa kema inkin samu dama”. Haka suka kusan kwana- suna hira gami da tsara yadda tafiyar zata kasance. . Innan taci gaba dayi mata nasiha da bata shawara akan zaman rayuwa da kuma sababbin
mutanen da za ta tarar tayi mu’amala da su.

ya kuke ganin zaman deeda DA saber zai kasance a birnin gayu anyama zasu hadu kuwa?
Hmm muje zuwa wai mahaukaci yahau kura

www.facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]