[Advertisements⬇️]

Birnin gayu 6 - Bankinhausanovels
Tue. May 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

                 birnin gayu🏘️

                    chapter6

          ASHA KARATU LAFIYA

Deeda kuwa ita ya fara gani, duk da kuwa akwai wadanda suka rigata; sabo da ita ya fara cewa a kira masa.
. Tare suka shiga da Inna. Tayi sallama, ya dago kai yana murmushi ya amSa mata sallamar.
Ya kalli Inna yayi dariyar tsokana yace, “Su Kaka ‘yan mata, an iso?” .
Ta yi dariya tace “Ya ka ganni ras dani, duk Budurwar da muka jera sai an ‘daukeni an barta”. . Yace, “Kwarai kuwa..Ai Kaka-“kinyi
fice , ‘Deeda dai kallonsu take tana dariya Kwarai halayen Ibrahim yana burgeta, duk da‘ alamu sun nuna dan masu hali ne ga ilimi ga wayewa amma ba shi da girman kai sai saukin kai sannan, ‘ga dukkan alamu mutum ne mai halin kwarai. ‘ ‘ ‘ ‘ . Bayan ya gama barkwancinsa da Inna ya mai da hankalinsa kan Deeda yace, “Malama Deeda zan fara da miki tambayoyi kafin in kai ga ‘ maganar Ciwonki. ‘
Tambayoyin da zan miki kamar cikakken sunanki, shekarunki da sauran‘ su, sabo da ina son bude miki (File ) ne don rubuta komai game da ciwonki, nan gaba in kin zo sai a dauko koda
bani zan ganki ba wani Likitan ne in ya karanta zai san komai game da rashin lafiyarki. Ina fatan  kin fahimta?”
Ta girgiza masa kai.
“Na .fahimta”.
Cikin‘nutsuwa yake ma ta tambayar tana ba shi amsa har suka gama, ya dinga ma ta tambaya game da Tarihin ciwon na ta tana ba shi amsa, amma wani lokacin Inna ta kan tsoma Baki har suka gama suka je ya mata gwaje- gwajen da ya dace sannan ya ba ta magani ya kalleta ya ce, “Kar ki damu ba wani matsala ba ce na tashin hankali, kamar yadda ki ka gani yanzu Fatarki ta fara washewa in kin Sha maganin nan zai taimaka miki sauran duk ilahirin jikinki ya wartsake.
; Sannan’ irin ciwonki ba a cika samunsa ta nan ba, yana wuya a samu masu irin wannan
Ciwon, shi yasa ma ba za a fahimci mene ne ba sabo da ba kowa ya san ko ya taba jin irin ciwon ba sai Likitoci irin mu.
Jikinki da fatar jikinki baya son inda ki keda yanayin wurin da ki ke zaune, misali;
Ruwan Garinku, yanayin Abincin wurin da irin Iskar Garin da aka Haifeki ki ka girma, kina da (Allegy) da wannan garin yankin wurin gaba daya, don haka da ki ka bar garin ki ka shigo nan sai aka yi dace jikinki ya karBi yanayin inda ki ka dawo, don haka fatarki da jinin jikinki ya fara washewa ya mike da kansa daga yamutsewar da ya yi.
Ga mutum mai irin jikinki ba .kowanne irin Abinci da ruwa zai karbe ki ba.
Kai hatta kaya zuwa mayukan da zaki dinga amfani da .,shi ba kowanne Jikinki zai karBa ba, dan haka a duk lokacin da ki ka fara cin wani abu ki ka fahimci canji a jikinki ki yi saurin kiyayewa, haka kaya da sauran abin da ya Shafi‘ jikinki.
Daga.kin yi amfani da abu ki ka ga ya canji a jikinki to ki yi saurin barin abun, in kin kiyaye insha Allahu ba za a samu matsala ba.
Yanzu» ga Magani‘ nan da kuma sunayen irin Abincin da ’za ki kiyaye cin su da kuma irin abin da ya kamata ki dinga ci, duk ba wani abu mai ‘ wuya bane da zai gagaraba”. . Nan Deeda ta yi shiru tana jinsa tana kuma tunanin Ciwonta
Wane irin ciwo ne da ba ta taBa ji k0 ganin me; irinsa ba? Ikon Allah! Allah mai yarda ya so!!
“Allah Ya kare ya kuma ba ki lafiya Deeda”.
“Alhamdu lillah, Likita ina godiya, yau na samu haske akan abin da ya shige mini duhu.
Na gode, Allah Ya saka ma ka da alkhairinSa”. ‘ .
Deeda ta fada‘tana’ kallonsa. Ya mata murmushi yace,’ “Karki damu Allah Ya Yi
mana jagora ya bamu LAFIYA, sai ki kiyaye kuma ki dinga shan magani”.
“Zan kiyaye insha Allah. Na gode”.
Inna mai Fura tace, “’Likita Kudi fa? Kamar nawa za mu biya?”
Ya yi dan’daria ya ce, Kaka ‘yan Mata nan Asibitin ai, na kyauta ne, k0: farkon zuwanku ba a fadi muku ba
“An fada mana Likita, sai dai in magani ma kyauta ne da kudin Katin
Ya yi’ murmushi yace, “Duk kyauta ne sai dai in bamu da maganin mu rubuta a siya a waje”. ,
“Ikon Allah! To yanzu Likita da kudinka ka ke siyan maganin?
’ Inna ta fada, kuma ta sa masa ido alamar amsa ta ke jira.
Ya yi dariya sosai ya yin da Deeda duk kunya ta kamata saboda tambayar Inna.
Ibrahim ya ce, “Kaka ‘yan mata ai nima biyana ake, ina nake da kudin daukan nauyin Asibitin nan? . ‘
Ai Likitocin ‘muna da yawa, ‘kowa da fanninsa.
Ni dai ina fannin Fata ne, wato masu matsala irin na su Deeda da makamantansu.
Me Asibitin shi ke biyanmu da kuma sauran masu kudi masu neman Lada, sukan ba ‘da gudunmawar .Magunguna da sauran abin da :Asibiti ke bukata k0 kudaden biyan Ma’aikata da sauransu don neman Lada da taimakawa  Talakawa marasa hali.”
“Ikon Allah!” In ji Inna.
. “Irinimu ke nan? Kai! Allah Ya saka musu da alkhairi, Allah Ya yi musu albarka, Allah Ya sa sauran masu Kudinmu suyi koyi da hakan
‘Amin”. Ibrahim ya fada yana dariya. Suka mike, Inna ta ce, “Mun gode Likita, Allah Ya yi ma ka albarka”.
Ibrahim ya amsa da, “Amin’ Ya kara da cewa, “In dai akwai wani matsala ku dawo, in kuma babu sai bayan sati shida ku dawo”.
“To Likita zamu kiyaye, mun gode”.
Har bakin kofa Inna na masa godiya ta fita, ya yin da Deedan ta juyo ta yi masa murmushi ta ce, “Gaskiyar Inna kana da kirki.
duk da ban san sauran ba, na san dai kafi  kowanne Likita kirki a Asibitin nan”. ‘
“Thank you are, welcome”. Ya fada yana murmushi. Sannan ta fita. Yayi dariya hade da girgiza kai yana  dariyar Inna a ransa ya ce, “Tsohuwar nan akwai magana, ga shi har ta sa shi Surutu don harya
manta yaushe rabonsa da ya tsaya surutu haka k0 a Gida ko a Asibiti.
Lokaci guda kuma ya shiga tunanin ciwon Deeda.
“Allah Yasa iyakar wahalarta ke nan, don kuwa in hakan ya ci gaba to a gaba za a samu. matsala, baya fatan abin da ya ke gudu ya faru”.
Shigowar mara lafiyane ya katse mai tunani.
Nan ya ci gaba da aiki ya yin da ya ke tunanin yadda zai sa Deeda ta masa aikin da ya ke so duk da k0 ya san abu ne mai wuya.‘
              %%%%%%%%%%
deeda ta isa Gida cike DA farinciki
zuciyarta a sake ta tsinci kanta cikin
nishadi  haka kawai zuciyarta ta mata haske, sam ba ta jin bakinciki ko Bacin ran tafiya, sai ma tunanin sabuwar rayuwa da sababbin mutanen da za ta tarar take yi. ‘
Inna mai Fura ma zuciyarta ta yi ma ta dadi, ganin yau ta daina ganin kunci a fuskar Jikarta.
Haka kawai ta dinga jin duniyar ta ‘dawo musu sabuwa.
A kofar Gida Tabawa k0 suka tarar da Mota da direba har ya iso yana jiransu.
Tuni har Tabawa ta gama jibge kayan Deeda a Mota ita kawai suke jira.
Ko cikin Gida Tabawa bata bari sun shiga ba ta taresu da su tafi kawai don duk abin da zu su buqata ta ‘dauko.
Inna ta kalleta ta ce, “Tabawa saurin me kike haka, k0 ciki ba za ki bari mu shiga ba kamar wanda ake kora
‘ .”Ba‘ haka bane Inna, Hajiyar tun ” dazu tai Waya ta ke ta fada kinsan ita ba a mata wasa, komai na ta kan qa’ida ne.
Kin san fa kun dade a ASibitin nan har na yi dana sanin tafiyarku
Deeda na jinsu ba ta ce komai ba. Tabawa ta bude musu Motar suka shiga baya ya yin da ita ta zauna a Gidan Gaba suka tafi
Inna mai Fura an shiga Mota mai tsada sai. washe baki take tana zuba Kauyanci.
Ya yin da Deeda ta fada duniyar tunani da sake-sake. ‘-
Ta yi nisa cikin tunani ba ta ankara ba taji Motar da suke ciki ta tsaya da alamar sun iso.
Ta daga kai ta gansu a Kofar wani ‘- makeken Gida mai girma da tsayin gaske, da alama Gidan sama da qasa ne, kuma komai na Gidan fari ne tas! ba Surki. ‘
Tun daga kan gate din Gidan har kalar fentin Gidan da komai na ciki fari ne tas. Tana nan ta zurawa Gidan Ido ‘tana kallon irin kyansa da tsarinsa tana mamaki.
“Dama ashe za a iya samun Gida irin wannan?”
,’ Can ta hango saman Gidan an rubuta; ‘BIRN IN GAYU’. .
Tana cikin karantawa ta ga gate na bude da kansa, don ita dai ba ta ga wanda yazo ya bude ba, tana mamakin abin suka kutsa ciki, har yanzu ba ta ga wani kalar abu a Gidan in ba Fari ba, hatta Ma’aikatan Gidan da ta lura suna kaiwa da kawowa fararen Kaya ne a jikinsu.
Tabawa dai ko a jikinta, da alama ta saba zuwa Gidan, Inna da Deeda aka bari da kauyanci.
Tafiya su ke Deeda da Inna na bawa idonsu Abinci har suka kai’ Bangaren Hajiya wanda Gidan sama ne, don kuwa ta (Lifter) suka tafi, wato Rana ta farko da Deeda ta taBa ganin lifta kuma ta shiga.
Inna dai sai addu’a ta ke har suka fita suka fada falon Hajiya.
_ Nan kallo ya koma sabo, sun sameta ‘tana harde a kujera jama’a na kewaye. da ita ana gaisawa.
Nan ta mike ta ja su wani falon don ganinsu a can, da fara’arta ta karBesu. ‘ Tabawa ta yi mamaki kwarai don ta zaci Hajiyar za ta Bata rai sabo da jimawar da suka yi ba su iso ba.
Deeda ne ta soma gaisheta, ta amsa tana dariya sannan ta gaisa da su Inna.
Ta kalli Deeda ta ce, “Na san dai k0 ba a fada min ba‘ wannan ce ‘yar Gidan tawa k0?”
Tabawa ta amsa da, “Eh ita ce Sunanta Khadija, amma ana kiranta da Deeda, amma ke kuma kina iya kiranta da duk sunan da ya yi miki”. .,
Hajiya tace, “Zan kirata da duk sunan da kowa ya santa da shi. Ina fatan dai zamu samu fahimtar juna?”
“1n Allah Ya yarda Hajiya, jikata ba ta da matsala”.
Tabawa ma ta karBa, “Gaskiya ne Hajiya Deeda akwai gaskiya ‘da rikon amana yadda kikeso. haka Deeda take”.
Hajiya ta yi dariya ta ce,”Da kyau abinda nake son ji”.kenan ‘ Deeda ta yi shiru tana kallon yadda masu Aiki ke kaiwa da kawowa, motsi kadan Hajiya za ta dau waya (Intercom) ta kira mai Aiki tana ba da umarni. ‘ ‘ Kamar Hajiya ta san me ta ke. fadi  a, cikin  zuciyarta ta ce,”Deeda ba aikatau zatai ba”. Inna mai Fura ta ke yiwa bayani. ‘ ‘ ‘ “Kamar yadda na fadawa Tabawa- , ’yar daki na ke nema wacce zan yarda da ita, zan iya bata amanar dakina, za ta iya sanin sirrina ba, tare da ta cuceni ba. “ta Kula min da daki da kuma wasu sirrika na kasuwanci na wacce zan iya amince ma ta ‘da dukiyata da sauransu. Da fatan kun gamsu da bayanina”. ,. “Na gamsu, kuma ina tabbatar miki da Deeda ba za ta ci amanarki ba. Sai dai don Allah nima  jikata na damka miki, ita amana Deeda ita kadai ce dani
yanzu haka itama haka da fatan duk abin da zai shafi addininta da al’adarta ba”. – ‘ “Kar ki damu Inna,” na karbi amanar Deeda zan riketa amana muddin ta rikeni da amana da zuciya daya to zamu ji dadin zama
Sun jima suna tattaunawa wanda  Inna mai Fura .ta gamsu da maganganun Hajiya __,  ta kara yiwa Deeda jan kunne Sannan Hajiya da kanta ta kaisu inda Bangarenta yake  Inna kam ta kasa yarda wai Deedanta ne zata zauna  a“wannan dakin
Tun daga  nan hankalin Inna ya soma kwanciya: ganin yadda Hajiya ta dauki Deeda ta amsheta’ hannu bibbiyu ba kyama. .‘
Ba su jima ba suka yi sallama, lokacin ne ‘ idon Deeda ya ciko da hawaye, lokaci na farko ke nan a rayuwarta da za ta rabu da Inna tun tana karama har ta taso su yi fada su yi wasa su yi dariya. ‘
Fadawa jikin Inna ta yi tana kuka.
Inna ma .sai da ta yi kuka tana lallashi, ganin hakan ya sa Hajiya tace kar ta damu za
a dinga kaita ta ga Kakarta, kuma Innan ma za ta iya zuwa ta ganta a duk lokacin da ta ke so.
Haka dai suka yi ta kwantar ma ta da hankali har suka tafi sun yi akan za a dinga tarawa Deeda kudinta na aiki sabo da Inna tace sana’ar da ta keyi ya isheta na buka’tun yau da kullum ‘ita kuma kudinta sai a tara ayi aurenta dasu. idan ta samu manemi kuma idan har lokaci yayi

        ()()()()()()()()()

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

kwana-a-tashi, a hankali Deeda ta Asoma sabawa da rayuwar
BIRNIN GAYU, haka Hajiya ta dinga nuna mata komai da komai yadda ake aiki da shi. Deeda ta lura Momi mace ce mai fara’a da jan mutane a jiki ta hanyar Siyasa. a Haka nan ba ta da matsala da mutane ko sa ido da takura, kullum tana cikin fara’a. Sai dai abu guda Hajiyar muguwar ‘yar kasuwa ce me son kudin tsiya, duk da tana da kudin amma ba ta son ta ga ta yi asaran k0na Sisi, haka nan bata bari kudadenta su makale, duk rintsi sai ta san yadda za su fito. , Tun da ta fahimci Deeda yarince mai’wayo, dabara da saurin fahimta saita jata a jiki yadda Deeda ke hada mata ‘kudi na kayan da suka shiga suka fita bata’ kuskure shi yafi birgeta, yadda Deeda ke aiki da Computer lokaci guda tana ma ta Transfer na kudedenta da ke Bankunan qasashen waje zuwa na Gida naija yana burgeta, ta lura yarinyarrrrrrrrr
Bayan wannan Deeda ke gyara mata Dakinta don bata yarda wasu masu aiki suna mata gyaran daki sabo da tsoro da rashin yarda sai ‘- –
a yanxu, duk wani me harka da Hajiya ya san Deeda,‘ ta kan bata wasu: shawarwarin wani lokaci ta yarda
kasuwanci kala daban-daban; take Wani lokaci Deeda takanyi‘ tunani da mamakin yadda Gidan yake ‘ ba ruwan wani da wani, kowa harkar
sa yakeyi ba sabo ba shaquwa tsakaninsu wani lokaci sai ta yi kwana biyu .bataga wani mahaluki ba daga Hajiyar sai ‘yan Aiki,‘ _ duk zaman da ta yi a Gidan bata ga
‘yan Gidan ba, ta dai ga »
Hoton yayanta, Wanda aka ce ma ta sun yi aure amma bata taba ganin sun zo ba. ‘
Bayan maganar kasuwanci da wani aiki ko shawara ba abin da ke hadata da Momi, haka ma su aikin Gidan ba mai mata magana balle ta yi sabo da su, kowa harkar gabansa ya ke‘ Wannan ya sa Deeda ~ta tsinci kanta cikin kewa daga ita sai TV sai Camputer wanda sune Abokanta masu debe mata kewa an bata komai;
Ci da Sha da Sutura komai ta sameshi a wadace, zama cikin ni’ima da cima mai kyau yasa ta murje ta yi Haske ta yi Kyau, sai dai ba wani farinciki ko nishadi a tare da ita, jikinta da yanayin rayuwarta ya canja: sai dai cikin zucin ba wani canji, zuciyarta tana nan kamar~yadda ta ke da, Karatunta ya tsaya sai dai ta godewa Allah‘da ta samu wannan dama. ‘ ‘
‘ Abu . guda ke sa ta farinciki in tana gaban Computer ko in Hajiya ta ba ta wani aikin don da alama Deeda tana da sha’awar (Business) kasuwanci wanda a zahiri shi ne burinta ta karanci Business ta Zama babbar Yar kasuwa wata rana.
Lokacin da maganin Deeda ya kare ta cewa Momi za ta gai da Inna, ba ta musa ma ta ba kuwa ta bata Driver ya kaita akan da yamma zai dawo ya dauketa.
               ///////////////
Inna ta ji dadin ganin Deeds sosai, musamman yadda ta ga ta goge ta murje tayi kyau, ga Kaya kamar wata ‘yar Mai kudi ‘ ta fito fes! Fes!! da ita, Inna Baki  a washe. — Tare suka je Asibiti. Yadda Ibrahim ya ga Deeda tabbas akwai canji sosai a tare da ita, tun daga yanayin shigarta, yanayin maganarta da wayewarta ya bam-banta da yadda ya taBa ganinta. Anya zai iya ma ta wani magana game da “‘ Sabeer‘.’ . Ga Sabeer abin nasa sai gaba ya ke, ga Daddy ya kusa dawowa har yanzu ya kasa Control din  Sabeer. ‘ Deeda ta katse masa tunani. “Likita lafiya kuwe? K0 akwai matsala ne?” ” “Ba komai ina dan wani tunani ne amma ba a
game da keba
‘ A halin yanzu ke dai ba ki da matsala don haka ina ga ba sai kin Kara shan wani magani ba, da :alama inda ki ke zaune ya karbeki don, na lura ya taimaka gurin gyara fatar jikinki.
Yanzu za ki iya tafiya, sai dai in akwai wani matsala nan gaba ki dawo”. ;
“Na gode Likita, zan wuce
“To ki gaida inna”.
“Za ta ji, tare da ita ai muka zo tana waje
Ya mike yana murmushi ya ce, “Bari inzo in gaida ‘yan mata kar ta fasa auren
Dariya sukai duka suka fita a tare. Inna na ganinsu kuwa ta mike tana dariya, suka gaisa ya ce “Nazo gai da Kaka ‘yan mata kar wani ya min shigar sauri”.
“Oh to da ba ka zo ba sai in yi sabon saurayi don samari har sun min yawa”.
wayar da ta yi Kara ya ja hankalinsu.
Bayan daga wayar ta yi sallama ta dan ja
gefe sannan ta’dawo wajensu tana cewa Inna mu tafi
Nan suka yiwa Ibrahim sallama, har sun fara tafiya Ibrahim ya tsai da ita, ya iso garesu ya ce “Miss Deeda in ba za ki damu ba zan iya samun
lambar Wayarki in Saurayinki ba zai damu ba ya fada cikin zolaya. ‘ “ Ta yi dariya ta ce “Su Likita manya, Saurayina ba zai damu ba, ga lambata Ta rubuto masa, ya yi godiya gami da cewa zata lya Jin kiransa kowanne lokaci. Ta so tambayar’ nasa lambar sai . ta kasa  da ya koma ya zurawa Wayar tasa ido yana kallon lambar
Karfe biyar ta‘yi sallama’ ‘da. Inna da Tabawa don dama dazun Hajiya ne ta yi mata Waya ta tambayeta karfe nawa za azo daukarta.
                ””””””””””
Wani dare Deeda na zaune‘ gaban
Computer bayan idar da’ Sallar lsha’i ta‘
mai da hankalinta sosai kan Computer
din sabo da wani Bussiness School da, ta shiga
online(P. C Training and Business Collage) tana jin
dadin Karatun sosai da koyarwan, haka nan tana ganewa da yake tana son abin. ‘
Wayartane yayi kara, ta yi mamaki kwarai don kuwa da_ wuya Momi ta kirata a wanna lokaci.
Haka nan tsira‘run wanda takeda Lambarsu masu siyen Kaya yana wuya su ma ta Waya a irin wannan lokaci.
Ganin an matsa da kira yasa ta mike ta nufi inda Wayar ke Chaji ta dauka, ta ga sabuwar Lamba ce. ‘ .
Nan ta daure ta danna 0k. tare da yin Sallama.
Muryar Namiji ce.ta ji an amsa ma ta sallamar nata. __
Yayi dariya ya ce, “Na yi sa’a kenan da har inatunanin ba za a dauki Wayata ba
Da fatan dai ban matsawa ranki shi dade ba?”
” wace ni?” Ta amsa masa.
“”Na so in fahimci’ muryar”.
“Dr. Ibrahim ne. Ya ba ta amsa.
“Likita Bokan Turai, barka da dare”. Ta fada tana yin dariya, da alamar kuma ta ji dadin kiran nasa.
“Lafiya, Alhamdulillahi”.
“Dama bugowa na yi mu gaisa in ji ya jikin naki?;Da fatan dai ba wata matsala
“Ba komai, jiki da sauki na warware, ina godiya”,
Sun jima suna hira sannan suka yi sallama.
Tun daga wannan rana Ibrahim ya kan yi ma ta Waya a duk lokacin da ya samu saukin aikinsa.
Haka nan itama tana kiransa sabo da shakuwa ta shiga tsakaninsu., duk da ba ganin juna suke ba a , Waya ne’
Sau da dama Ibrahim ya kan nemi shawara wurinta, haka itama ta kan bude masa damuwarta da matsalolin da ta ke fuskanta na rayuwar yau da kullum, domin Deeda jin Ibrahim take ‘Kamar Aboki, Dan uwa,
Bayan Kakarta ba wanda ta taba kusanci da shakuwa da shi sai Ibrahim.
A hankali Ibrahim ya fahimci Deeda da ’yadda take, yanayin rayuwarta  tunaninta duk mai sauqi ne.
Haka idan ta samu dama za tai abu da yawa a duk lokacin da ya tsinci kansa cikin damuwa k0 wani Bacin  rai to Wayar Deeda da kalamanta ke kawo masa sauki, yana samun nutsuwa sosai ,da
: kullum sai ya tambayeta Inna mai Fura.
,Yawancin wayarsu yakan mata magana akan halayen Sabeer, don har yanzu ya kasa shawo kansa  kokarinsa Sabeer ya’fahimta.‘ ta kance ita laifinsu take gani DA tun farko suka kasa controll dinsa sai yanxu
‘ ‘ Ibrahim ya kan yi murmushi ya ce, “Deeda ba za’ki fuhimta ba a hankali,’wataran zan warware miki zan fahimtar da ke   dangantakar da ke tsakaninmu da Sabeer da Gidan su halin yanzu, mu barshi a yaddaki kace . Ta yi ajiyar . zuciya tace, To.shi ke nan ‘Ibrahim, ni dai ‘na san kai mutumin kirki ne (Very good human being) wanda wannan halin naka na daya daga cikin abin da yake hurgeni  ina ganin girmanka da dajarka, ya yin da Kaninka.,..” ‘ .~
“Ya isa Deeda, ba zan jure yabon dakike min da kushe Sabeer be, mu bar maganar”. Ajiye Wayar ta yi ba tare da Sunyi ‘sallama ba, saboda ta fahimci maganar da ke hadasu fada . ‘kenan  Ta kanyi mamakin irin yadda Ibrahim ke qaunar Sabeer baya Kaunar abin da zai taBashi, baya iya jure jin. laifin Sabeer daga bakin wani. A hankali Deeda ta fahimci cewa ta yi wani irin shakuwa da Ibrahim cikin kanqanin lokaci. ‘
             &&&&&&&&&&&
Karfe biyun dare amma Ibrahim ya ‘kasa ‘ . rintsawa yanata kaiwa da kamowa, komai ya masa Zafi.  Ya tuno yadda suka kwashe da ‘ Sabeer sannan  damuwarsa shi ne wasu sababbin ABokai da yaga Sabeer din ya sake, ba su da aiki sai kashe kudi yawan zuwa Party da neman; Matan tsiya Maimakon .Sabeer ya  gyaru sai kara dauko hanyar-lalacewa’ yake
Ya kasa rikon Sabeer, ya kasa kula da shi, ya kasa riqe amanar da aka bashi, ga aiki yayi masa yawa ga nauyin Asibiti a kansa ga na marasa lafiya ga kuma  Kamfanin Alhaji, Kudade da yawa sun bata wanda bincike ya nuna da Hannun Hajiya a ciki, komai ya masa zafi, yama rasa abin yi, ga nashi Personal Problem din.
Ya dauko Wayarsa ya kira Farida idonsa jawur
“Kanina”. Ta kirashi muryarta qasa qasa
Hakan ya fadar masa da gaba. ‘
“Yayata lafiya na ji muryarki haka?” “Kanina na yi aiki ne kawai na .gaji, kaina ke dan min Ciwo”.
“Yayata Please ki dinga hutawa kinsha Magani ko‘  inzo ne?
Nifa yadda na ji ki ya jefani cikin tashin hankali‘da damuwa”. .
“Kanina kar ka damu na fadi ma gajiyace kar ka damu zan kula da kaina”.
Sabeer da da Daddy suna bukatarka , ke ba kya bukatata Yayata”. ‘ “Ba haka bane Kanina”. “Haka ne Yayata?” .-
“To in ke ba kya buqatata ni ina buqatarki Yayata”
Ya fada cikin murya mai rauni.
“Kanina ka yi hakuri na san ban maka adalci ba. ka yafe min kanina, ka yi qokari ka fahimci matsalata”.
Tuni har hawaye ya wanke ma ta fuska Kanina akwai matsala k0? Me ke faruwa?
“Ba komai Yayata”. Ya yi dariyar dole don kwantar ma ta da hankali.
“Kar ki damu, kawai dai na tsinci kaina cikin kewarki ne ina missing dinki, kar ki damu, sha Magani ki kwanta”. .
“To .Kanina na gode. Ina nan zuwa very soon”. ‘
“‘Allah Ya kawoki lafiya . Na san in kin zo da yardar Allah komai zai dai-daita”.
‘Ka kula da kanka kanina da Sabeer da Daddy gaba gaba daya. Sai da safe”.
Ta yi saurin ajiye Wayar. Ya jima yana kallon‘ Wayar sannan ya soma danna lambar .Deeda sai kuma ya fasa, qarfe ukun dare me zan ce mata?”
Ya nufi dakin Sabeer don ganin me yake ya yi Bacci in bai yi ba zai masa magana da gargadi
ya qara tuna masa abin da Mahaifinsa ya ce, ya kuma sanar dashi Daddyn ya kusa dawowa.
Hango qofar dakin ya yi a bude Wuta a kunne abin ya ba shi mamaki sosai, ya isa dakin da sauri, gabansa ya yi mummunar faduwa, Sabeer ne ya gani kwance da Kwalaben Giya, kwance a gefensa baya cikin hankalinsa yana sake da kayansa da Takalmansa da wasu Kwayoyi a gefensa.
innalillahi wa inna ilaihirr’jiu ’un.’.’” Ibrahim ya fada cikin tashin hankali.
Wani irin baqinciki da tashin hankali ya bayyana a fuskarsa. ” ‘ ” ”
Ya isa‘ gareshi da wuri.
“Sabeér” Ya kira sunansa da karfi. ‘ *
“Wato abin na ka har ya kai haka?”
‘ ‘ ldanunsa suka kada suka yi jawur, kukan ma ya kasa, ya lura Sabeer din k0 hannunsa bai iya dagawa balle bude ido sai surutan banza
Cikin takaici da bakinciki ya cire, masa Takalma tare da gyara masa kwanciya, ya tattara kwalaben ya bude wani karamin Fridge da ke manne a bangon Dakinsa.‘ Kwalaben giya ne masu tsadar qaske a cike a ciki. ‘
Nan ya hau bincike k0 ta ina a dakin, haka ya dinga yin karo da kayan maye kala-kala. Bai taBa shiga tashin hankali da bakinciki irin na wannan Dare ba.
“Ya aka yi na yi sakaci haka. na ci amanar Maman Sabeer na ci amanar Farida ban rike Sabeer ba ban kula da shi ba”.
Nan yakama kai awurin yanakukan bakinciki da takaici tare da tausayawa rayuwar Sabeer in ya mutu a wannan hali ya yi asara babba ‘ .
– Sam‘ ba shi da nutsuwa _a duniya balle ya samu nutsuwar neman lahira. ‘ ~
A wannan dare Ibrahim bai rintsa ba ya kwana yana sallah yana kai kukansa gun Allah tare“ da Addu’o’i sosai.
Hakan ya dan ba Shi nutsuwa. Da Asuba ya kira Farida amma ba ta dauka ba, ya sake kira, wani Likita ya dauka ya masa bayanin tana Asibiti
gaskiya bata da lafiya, amma ta ce ba ta son ya sani, amma Likitan ya tabbatar masa da cewa jikin na ta da sauki.
Tashin hankalin da lbrahim ya tsinci kansa ya. munana. ‘
“Yayata ba lafiya ga halin da Sabeer ya shiga, ga Asibiti ga Kamfani, ga Daddy baya nan Duniyar tai masa zafi ya rasa abin yi. ,
“Shin da wanne zaiji? Ba zai’ yiwu ya tafi wurin Farida ya bar Sabeer, a wannan haliba , ga Asibiti da kamfani duk suna buqatarsa, yana kaucewa kadan komai zai tsaya.
Yana cikin wannan halin nan ya hango Sabeer ya tashi cikin fushi ya nufi inda yake ya hau fada ta inda ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba.
Nan Sabeer ya zuciya shima ya amsa masa cewa, “Uncle IB zan yi abin da na ga dama ba wanda ya isa ya takura min ko ya‘ hanani. To meye in na sha Giya? Me ye a ciki za ka zo kana min fada? – ‘
Ni fa ba zan Yi aiki irin ka ba kullum Asibiti kullum kamfani, zan rayu yadda na keso, Kudine Uwata da Ubana sun tara min domin jin dadin ‘rayuwa, to me ye damuwarka
, ba za ka
Ka matsa min ka sa min ido. Ina kyale ka ne albarkacin Sister.
Ka rabu da ni, zan yi rayuwata yadda na ke so, kuma Giya ba wanda zai hanani in sha. Mene ne in na sha Giya?”
“Tas” Ibrahim ya wankeshi da Mari.
“Meye in ka sha Giya? Ba ka san me ye ba in ka sha Giya kana dan Musulmi kana irin wannan maganar?
Kai da ka san illar shan Giya da muninta da ko’ sunanta aka ambata sai ka ji tsoro da kyamar kiran sunan nata. .
Duniya kawai ka _sa a gaba, ba ka san zaka mutu ba, k0 ba ka san akwai
RAYUWA BAYAN MUTUWA BANE? K0 ba ka san kwanciyar Kabari ba ne?
. Ji bi kanka, ba ka jin‘ kunyar zama cikin duhu ba’ka san addininka ba? ‘
Ada ina ganin abin na ka kamar yarinta amma yanzu na lura ya zama ganganci;
To bari ka ji, daga yau na rufe duk wani Account dinka na kudi, duk wani hanyar Kudi na toshe maka ita, Makullan Mota babu su, kuma tun da kace ba za ka yi aiki ba, to ba kai ba fita. kana nan
cikin Gidan nan, ba Waya ba Abokai duk na rabaka da komai sai ka zaBa k0 zaman Gida a kulle ko ka bini Office qafata-Kafarka duk inda na shiga, zabi ya rage na ka”.
Nan ya ja kofar dakin ya rufe ya tafi ya kyaleshi yana ihu yana kwalla masa kire.
“Uncle ib please ka budeni ba zan iya zama a nan ba.
Please Unclc IB ba zan kara ba, zan yi duk yadda ka ce‘
Wayyo Uncle iB to ka mai da ni wurin Sister”.
Haka ya yi ta ihu amma bai saurareshi ba ya wuce ya figi Mota.
A wannan lokacin mutum daya ya keson gani ita ce Deeda, sai dai ya yi rashin sa’a yana zuwa Gidan ya samu Inna ta ce masa ai Dccda ba ta nan, ba a nantake zama ba. . ‘
Bai Kara ce ma ta komai ba ya fita ya kira Wayarta. Sai da yaiyi qara’ sau‘ uku kafin ya kai ga ta dauka, kafin tace Wani  abu ya tambayeta. “Kina ina?”
“Lafiya?” Ta tambaya.
“Ina son ganinki ne yanzu-yanzu! inda hali ki fada min inda ki ke yanzu zanzo in sameki, kar ki min wata tambaya sai nazo”.
Ta lura yana cikin zafi da Bacin rai, don haka- ba ta sake masa wata tambaya ba.
Ya sake tambayarta, “A wacce unguwa ki
ke?”
“Ka san BIRNIN GAYU?” “Birnin Gayu‘?” Ya maimaita cikin mamaki. Ta ce “Eh inkazo Gidan ka yi min waya”. “Kina nufin a Unguwar ki ke?” Ta amsa da, “Eh”. “To shi ke nan gani nan zuwa”. Ya ‘ajiye Wayar ya tafi yana tunani. Shin wane Gida Deeda ta ke a unguwarsu? To koma ina ne dai yanzu burinsa ya ganta k0 za ta taimaka masa ya samu saukin matsalarsa. Haka Deeda ta dinga kaiwa da kawowa yanda taji tashin hankali a muryarsa yasa ta cikin damuwa, sai ta ji itama na ta hankalin ya tashi. Momi ta. fito ta ce “Ta kula da Gidan zata shiga wani miting a Office ana jiranta”. Nan ta mata sallama ta fita, ya yin da Deed: ta kasa zaune da tsaye,
Wayar‘ Ibrahim  ya shigo, ta yi saurin dauka yace mata, “Gani a
BIRNIN GAYU, ta ina ki ke da Gidan?”
“Jirani a wunrin gani nan fitowa“;
Nesa’ da Gate din kadan ya yi parking yana jiranta, ya yin da ya zurawa wurin ido yana jiran ya ga ta ina za ta bullo. ‘
Bude Baki ya yi mamaki ya bayyana  a fuskarsa lokacin da ya hangota tana fitowa -daga BIRNIN GAYU, wato cikin Gidansu. :
Tsaye take a qofar Gidan tana kalle kalle.
Ya lura da hakan hakan ya sa ya fito daga cikin Motar ya nufo gareta, itama ta ganshi ta isa. gareshi fuskarsa cike da damuwa ta kula ta ce
,”Laflya Likita, meya-faru haka .kake son ganina?” ”
Ya kalleta cike da mamaki yace, “Deeda dama a BIRNlN GAYU ki ke?”
“Eh, labarin mai tsayi ne a Gidan na.‘ ke amma fa ba Gidanmu bane, aiki nake a Gidan”.
‘ “Aiki? Wane irin Aiki?” ‘ ‘ Ta ja dogOn numfashi. ,Karka damu “Zan, fahimtar da kai a hankali. Yanzu dai ka fada min mene ne?”
Muje can mu Yi magana”.
Ya wuce, bata bishi ba sai dai kallon mamaki.
Nan ya dawo ya jawo hannunta har suka isa bakin wani karamin Garden yaja kujera yace, “Zaunai ‘ Ba ta musa ba ta zauna, ita dai ya zame mata- abin kallo da mamaki.
Ganin haka yasa ya kalleta ya ce, “Yanzu zan ba ki dukkan wani amsar tambayarki.
Deeda ina cikin damuwa da tashin hankali ‘  wanda na ji ina son ganinki don duk duniya a yanzu bani da wanda zan zauna in fada masa matsalata.
Deeda k0 ba ki min maganin matsalata ba zan samu saukin zuciyata tun da na bayyana miki damuwa—ta.
Deeda ki taimaka min koda kalaman karfafa guiwa ne da kwantar da hankali don ina bukatarsu”.
Hawaye ya gangaro masa wanda hakan ya daga hankalinta,
Ibrahim da kullum murmushi ke
shimfide a fuskarsa wanda murmushinsa ya isa ‘ya kwantarwada duk Wani mai damuwa hankali,‘ ta ji – kamar ta rungumeshi ta ba shi baki, sai dai ba halin hakan.
Ya lura da yanayin data shiga hakan yasa yayi na maza ya daure ya yi ma ta wannan murmushin nasa sannan Yace, “Kar ki damu Deeda (I’m okay),‘nasan kina mamakin shigowata Gidan “nan haka? To nan dai Gidan mune
“Gidanku?” Ta fada tare da mikewa tsaye tana dubansa cikin mamaki.
“Tabbas haka batun ya ke muna Gida daya amma bamu taba sani ba?
Sai dai ba abin mamaki bane in kinyi la’akari da girman Gidan nan da yanayin rayuwar Gidan nan ba ruwan wani da wani; musamman Momi da ba shiga bangaren mu take yi ba”.
Ta kalleshi ta ce, “Amma Ibrahim nayi mamakin kasancewarka dan Gidan nan, halinka ya bam-banta da na sauran jama’ar Gidan nan.
Ibrahim halayyanka da dabi’arka ta bambanta da tasu.”
“Deeda ke nan, kowa da yadda Allah Ya yi. shi, kowa da irin halinsa da tunaninsa.
Yau zan baki labarin-DANGANTAKATA da Gidan nan da matsalar da na ke ciki, ina buqatar taimakonki da tallafawarki
“Ina jinka Ibrahim. Ni kuma na yi alkawarin taimaka maka in dai baifi karfina ba”. »
Ya kalleta sosai, itama ta kalleshi a hankali. Ya labarta mata komai. ‘
Lokacin da ya gama ba ta labarin sai ta yi ajiyar zuciya ta ce “Lallai Ibrahim kana cikin tsaka mai wuyar fita.
To sai dai ba abin da yafi karfin Allah, mu yi Addu’ar Allah ya kawo mafita.
‘Sannan Ibrahim me zai hana Yaya Farida ta dawo Nigeria sai na ga kamar idan tananan komai zaizo da sauki tun da Sabeer ma yafi jin maganarta, haka nan za ku taru tare da Daddy‘ ku rike Kamfaninku da Asibiti a tare, amma barinka kai daya da wannan nauyin ba abu bane mai sauqi”. ”
‘Yayi murmushi ya ce, “Deeda ke nan, yadda ki ka dauki abin ba haka bane, akwai dalili mai Karfin da ya sa Yaya Farida ta nesanta kanta da mu, wanda ba ta so mu sani, “kuma ‘wani sirri nena daban tsakaninmu da ita.
Sannan Daddy shi ya Bata Sabeer tun farko,  wani ma yana hukuntashi wahala yake masa, ba zai jure ba balle shi da kansa. . ‘
‘ Deeda a yau in na samu Sabeer ya kimtsu ya san me ya ke to ina mai tabbatar miki da matsalata za ta zama kadan. Sabeer shi ne babban damuwarmu da matsalarmu a yanzu. Deeda ki taimaka min”.
Ta kalleshi tace “Da me Zan taimaka maka Ibrahim bayan kaima ya gagareka balle ni da jininmu bai hadu ‘ba, wanda kaima ka san hakan, “Deeda naga Hope akan Sabeer lokacin muduwarku ta farko, yadda ki ka yi (Handling) dinsa cikin kankanin lokaci ya burgeni, rana ta farko da naga Sabeer ya zama (Serious) ranar da ki ka fara ‘haduwa da shi, tun daga wannan ranar na ganki a wata aba ta hanyar taimaka min mu canja rayuwar Sabeer mu inganta rayuwarsa  . Deeda za ki taimaka min?”
! Ta kalleshi a karaye cikin sanyin murya da tausayawa tace, “‘Ibrahim zan so taimaka ma ka, zan iyA komai don in kawo kwanciyar hankali  a rayuwarka.
Kaine mutum na farko da ka kalleni da qima da daraja har ka ga wani abu na dabam a tare da ni.
Dukkan rayuwata na taso cikin tsana ne da tsangwama wanda Mahaifina ma daya haifeni sai da ya gujeni- ~,
Kaine namiji na farko daya fahimci ‘ni mutum ce har ina da wasu (Qualities) k0 dabi’u,‘ halayya masu kyau da har zan tallafi rayuwar wani, zan yiwa wasu amfani, nima mutum ce mai amfani.
Na gode da wannan karramawa taka da mutuntawa ta ka. .
Ka yi Abota da ni lokacin da bani da ,kowa, lokacin da nake cikin rayuwar kewa.
Ka tausaya min ka taimaka min lokacin da na ke cikin hali na rashin lafiya, ka mayar da ni mutum wacce ta isa ka nemi shawarata k0 share min hawaye.
Ni din nan da ba komai ba kowa ba har na isa ka nemi taimako a wurina. Tabbas Ibrahim dabi’unka, halayyarka abin so ne
Ni Khadija zan iya komai sabo da samun nutsuwarka muddin bai kaucewa Addini ba.
Sai dai Ibrahim bana jin akwai taimakon dazan maka, don kuwa Sabeer bai daukeni mutum bama balle ya bani damar kawo wani gyara a rayuwarsa
lrin su Sabeer Mace mai kyan gaske ‘yar masu kudi ma basu isa ba balle ni Deeda ‘yar Kauye wacce bata da komai a rayuwa daga ranta sai “lfy sai kuma godiyar Allah, wacce don in rufawa kaina Asiri da ‘yar Tsohuwata na baro Garinmu da Kauyenmu don rufin Asirinmu ni da ita duka.
Ina yiwa Momi aiki, haka. aikin da na kewa Momi mai kyau ne da tsabta, ta rikeni Amana,~  haka.
Kaga k0 bani da hanyar taimaka maka kuma bani da abin taimaka maka da shi”.
Ya‘ harde’hannuwansa a kirji tare da sakar ma ta murmushin da ta ji ya saka ma ta nutsuwa yace “Deeda kenan, ni na ga abin da ba ki sani ba a tare da ke ‘
Ke kanki kinsan Allah ne mai kyauta da bayarwa, Ya yi miki baiwa ta hanyoyi da dama wandaba kowa zai iya saurin ganinsu da fahimtarsu ba lokoci guda sai ‘wanda Allah Ya nufa. .
ldan Allah Ya bawa wasu baiwar  dukiya, to kema fa akwai wani sirri da baiwa da ya miki, wanda ke kanki ba ki sani ba.
“Ke kuma kin iya nunawa matum ba kya jin baushi da wuri  shi yasa ki ke iya zama da Momi”. . .
Ta yi dan’dariya, “Ai ko Momi ba ta da matsala”. ‘
“Hakane a wurinki, sabo da ba kya taBa mata Kudi, kuma ba ki sawa dukiyarta ido
Kin san yanzu ba ta da matsala da ni da Sabeer, in dai ba shiga harkar Kamfani zamu yi ba, ta barmu da Asibitin, ita ta rike Kamfani.
Kinji fa tun Daddy yana da Rai take son rabon Gado.’
Tana jin dadin yadda Sabeer baya zuwa Office sai kokarin turashi Asibiti ta ke don kar yazo ya Sa-mata Ido wanda shi duk ba su dameshi ba, da Asibitin da Factories din da Kamfanonin Alhaji duk basu gabansa”. ‘
Ya kalleta ya ce, “Bari dai in yi shiru don kar in ci gaba in bugo Gangar Kusa da Dirom.
MEYE DANGANTAKARKI da- Momi?”
Ta yi mutmushi ta ce, “Yanzu kaima za ka ji”.
Nan itama ta labarta masa. ‘
Ya ce, “Na lura Deeda za mu yi babbar Business Woman (You have passion in business)”.
Ta yi dariya ta ce, “Kwarai (Business is my Passion) ni da bani da k0 KWANDALA!”
Ya yi murmushi ya ce”Ni na gani a tare da
ke? Kuma in kin bincika tarihin manya-manyan ‘yan Kasuwa masu Kudin yanxu, to ba su dako  Kwandalar suka fara har suka samu suka zama manyanmu a yau”.
“Ibrahim ke nan, haka dai ka ce, amma ni dai bani da wannan bukatar”.
“To na ji, yanzu mu bar wannan maganar, zan wuce 0ffice ina da abin yi da yawa. Ina fatan za ki yi nazari akan maganata?”
” “Maganar Sabeer Ibrahim na fada maka ba abin da zan iya”.
“Za ki iya, ki bar komai a hannuna”.
“Na ji, zan tafi nima ina da abin yi
“Toshi kenan
Suka mike a tare. ‘ ‘
“‘Sai mun yi Waya k0 in ce sai haduwa ta gaba, zan zaga da keki san BIRNIN GAYU da kyau”. tayi murmushi gamida cewa Allah shi kaimu

to nima nace Allah shi kaimu gobe donjin ci gaban wannan qayataccen lbrn. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]